Daga Na’ima Abubakar Kano
Kalmar Yaudara kusan kalma ce da ahalin yanzu ta zama ruwan dare, duk da kasancewarta abar kyama da kuma bukatar kauce mata. A lokuta da dama wasu jinsi na al’umma sun dauke kamar wasa ko ace hanyar jiga abokan mu’amillar yau da kullum. Abinda kullum mafi yawan jama’a ke tambay ashi ne tsakanin mata da maza wa yafi yaudarar dan uwansa. A iya fahimtata A a gaskiya mace tafi namiji yaudara, abin da yasa nace haka shi ne mace ko maza sun kai goma tasan yadda zata bi da kowane a cikinsu, kuma har cikin zuciyarta duk cikinsu wata kila ba wanda ta ke yiwa so ko na minti daya wanda take so yana can waje daya su dai wadancan kawai yaudara ce irin ta mace.
Suma mazan suna nasu salon yaudarar matan amman ba kaamr matan ba, wannan kuma kila baya rasa nasaba da alakar da kan jawo samun damar shigar da yaudar a tsakaninsu. Alokuta da dama karya na taka muhimmiyar rawa dake haifar da yaudara, musamman idan batun soyayya ko akasin haka ya faru. Ita mace kullum a iya fahimtarta ‘ya ce a ruwa ta mai rabo saboda haka kila hakan kan sa tayi amfani da wani salo na yaudara don hada wasu bukatunta da take fatan cimma. Haka kuma abangaran maza yawan ci kan so a san ko su suwaye ke haifar da yaudara sanadin karya, shi yasa zaka tarar da wasu samarin na yaudarar yan’mata ta hanyar su ‘ya’yan wane ne ko sun Mallaki kaza da kaza.
A wasu lokutan har hana cikinsu komai suke yi domin mallakar abin da zai iya daukan hankalin ‘yan matan wajen yarda da abin da za’a fada masu. A wannan zamanin domin daurewa karya gindi da yiwa yaudara kwalliya samari har hayar mota suke karba da tufafi, kai har turare suke karba wanda da yazo zata ce ga wane yazo donin tashin kamshin turaransa , sakamakaon imanin mace da kuma imanin da tasaka a ranta sai kaga cikin kankanin lokaci an daureta da igiyar zato.
- Za a iya tuntubar Na’ima a wannan lambar – 08039701321