Umar A Hunkuyi" />

Burina Na Ga Na Raba Nakasassu Da Yin Bara –Yahaya Makaho

A ranar Alhamis 19 ga wannan watan na Yuli ne, aka yi wani gagarumin buki na raba gudummawa da tallafi ga masu nakasa. Gidauniyar nan ta Malam Yahaya Makaho ce ta bayar da wannan tallafin wanda ya gudana a harabar ofishin gidauniyar ta Yahaya Makaho da ke kan titin ‘Independence Way,’ cikin garin Kaduna. Gidauniyar ta baiwa wasu yara makafi ‘yan makaranta mazada mata, Musulmi da Kirista tallafin abubuwan karatun na su ne har na kusan Naira miliyan guda. Hakanan wasu guragu masu sana’o’i, su ma sun sami tallafin, da kuma wasu makafi masu gyaran ababen hawa da makamantansu duk sun sami tallafi daga gidauniyar ta Yahaya Makaho. Ga abin da Yahaya Makaho ke cewa kan manufa da kuma dalilinsa na kafa wannan gidauniyar a wajen taron;
“Kamar yadda na sha fada ne, ba ni da wani tunani da ya wuce kullum na ga cewar ba mutane masu lafiya ne kadai suke da damar jin dadi ba, ko kuma yin abin da ransu yake so, ina son na ga cewa mu ma, masu nakasa muna da daman yin abin da ranmu yake so, muddin dai abin nan bai sabawa doka ba, ta kasa ko ta Addini. Amma sai na ga cewa mutananmu an bar su a baya, kamar yadda ku ka ji bayanai a ]azun, a cikinmu akwai Lauyoyi, amma da wuya ka ji an ce an tura wani Lauya waje ka za domin ya kare wani shugaba ba, duk wani mahimmin abu ko babban al’amari na siyasa, kasuwanci ko mukamai da makamantansu, ba zaka gani ko ka ji an tura wani mai nakasa a kan shi ba, sam ba mu a bakin komai a cikin kasarnan. Duk kuwa da irin hazaka da basirar da Allah Ya yi wa da yawa daga cikinmu kamar yadda ya yi wa kowa.
Duk da cewa, za ka samu gwamnatocinmu sukan gina wuraren da za a koya wa masu nakasa sana’o’i, amma iyakar ta kenan, in an koya maka sai kuma a sake ka, ba jari ba kuma wani taimako. Muna da kungiyoyi da a kullum za ka ji suna ta babatun suna taimako, amma sam abin bai kaiwa kanmu mu nakasassu. Hakan ya sanya na fara tunanin ko dai mutananmu, ba su san irin taimakon da nakasassun suke da bukata ne ba. Da wannan ya sanya ni na yi tunanin na kirkiri gidauniya domin na taimaka wa ‘yan’uwana masu nakasa. Wadanda suka iya wata sana’a na tallafe su, na taimaka masu, sannan kuma wannan gidauniyar in ta sami dama, sai ta rika sayan kayayyakinsu tana kaiwa kasuwanni na ciki da wajen kasarnan tana sayarwa mutane, wannan shi ne tunani na, shi ne kuma babban dalili da hadafin kafa wannan gidauniya.
A taron namu na yau, mun fara ne da bayar da tallafi na musamman ga nakassasu musamman yara maza da mata makafi ‘yan makaranta, inda muka tallafa masu da takardun karatu da na rubutu, alkalumman rubutu, tufafin makaranta, na’urorin keken rubutu irin na makafi har ma da biyan masu kudaden makaranta da makamantan hakan. Sannan kamar yadda kuke gani, kayan karatu irin na makafi tsada gare su, misali daya kawai, alkalamin rubutu, in na mai gani ne zai iya sayansa a Naira goma ko ashirin, amma alkalamin rubutu irin na makaho, kwara guda ya harari Naira dubu guda. Abin da zaka kashe wajen koya wa makaho guda karatu, zai ishi yara masu gani sama da guda goma. Wannan ne ya sanya iyaye da yawaba sa iya kai masu nakasan makaranta, domin ba za su iya daukan nauyin karatun na su ba.
Sannan ni duk da yake ba gwamnati ne ba, duk da ma cewa, gwamnatin zai yi wuya ta iya daukan nauyin raba nakasassun da bara, amma dai abin da na yunkuro a kansa shi ne, zan bayar da gagarumar gudummawa ta gani ta fada, wajen na ga na hana barace-baracen. Ina wannan tunani ne domin ina da zuciya ta kyamatar bara, don haka ina son na cusa wa ‘yan’uwana irin ra’ayin da nake da shi. In har na samu ire-ire na, muka kai misali bakwai takwas, tabbas za mu yi duk abin da muke iya yi na matsawa gwamnati da ta sauke nauyin nakasassun da ke kanta ta kyautata masu domin ta raba su da wannan baran.”
Shi ma Kwamared Muntari Saleh, sakataren ya]a labarai na kungiyar ta Makafin Arewacin Nijeriya, wanda kuma har ila yau, shi ne babban bako a wajen raba wa Makafi da guragu tallafin, ya yi tsokaci ne a kan, mahimmancin kafa wannan gidauniyar wacce ya kira ta da abu mai mahimmanci. Daga nan kuma ya yi kira ga duk wani da yake da nufin taimaka wa nakasassun da cewa, yanzun fa daman hakan ta samu, domin kuwa ga wannan gidauniya da Yahaya Makaho ya kafa, wacce ya ce ta sha bamban nesa ba kusa ba da ire-irenta da aka sha kafawa a baya, domin kuwa yanzun mu dinne zaka zo ka taimaka wa kai tsaye, ga mu gaka. “Wannan fa dan’uwanmu ne Makaho, wanda ya yi wake-wake har ya sami kudinsa, sannan kuma sai ya ga bari ya zo ya taimaka wa ‘yan’uwansa da wadannan kudaden da ya samu,” in ji Muntari Saleh.
A karshe yake yin kira ga gwamnatoci da masu kudi da cewa, in har da gaske ne suna son a daina bara, to ga fa hanya ta samu. “Yahaya Makaho fa bai kai ga wannan matsayi ba, face da taimakon wani bawan Allah guda daya rakkin, wanda shi yaba shi dukkanin gudummawan da har Allah Ya kai shi wannan matsayin, shi ne kuwa wani dan kasuwa mai suna, Alhaji Nasiru Dano, wanda a yanzun haka mun kammala shirin nemansa da ya zo mu nada shi a matsayin, ‘Garkuwan Nakasassun Nijeriya” in ji Muntari Saleh.
Sulaiman Yahaya, (Aronsi 10-10), wanda babban na hannun daman Yahaya Makahon ne, kasantuwan shi ma matashi ne dan boko, dan siyasa kuma makaho, ya bayyana irin gwagwarmayar da suka yi ta sha tare da Yahaya Makahon har kafin Allah Ya kawo su a matsayin da suke a halin yanzun, “Duk don fito da mutuncin nakasassu ‘yan’uwanmu, mun yi abubuwa da daman gaske, a baya can tare muke yin waka da Malam Yahaya Makaho, daga bayane ni na zo na shiga siyasa, wanda har takara na yi a cikinta, ina kuma cikin nata a halin yanzun. To alhamdu lillahi, kamar yadda duk duniya suke gani a yau, Malam Yahaya ga shi ya tara ‘yan’uwansa masu na}asa yana raba masu ababen bukatar bunkasa rayuwarsu, duk da shi ma fa ba fa ya koshi ne da ku]in ba, amma dai zimmar aniyar da muka dauko na ganin dawo da martaban nakasassaun ne ya sanya shi yin hakan,” in ji Makaho Sulaiman Yahaya, wanda aka fi kira da Aronsi 10-10.

Exit mobile version