Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Burina NURTW Ta Dogara Da Kanta A Kaduna – Aliyu Tanimu Zariya

by
2 years ago
in TATTAUNAWA
4 min read
Burina NURTW Ta Dogara Da Kanta A Kaduna – Aliyu Tanimu Zariya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A kwanakin baya, sabon shugaban kungiyar direbobin haya ta kasa, wato NURTW reshen jihar Kaduna, ALHAJI ALIYU TANIMU ZARIYA, ya jagoranci Dora harsashin ginin kamfanin da zai rika yin ruwan roba da kuma na le da tare da kaddamar da wasu motocin haya uku kirar Sharon a cibiyar kungiyar da ke garin Kaduna. Bayan kammala wannan taron ne wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABDULLAHI GIDAN bAKKO, ya sami damar tattaunawa da shi kan wadannan ayyuka da ya kaddamar da kuma karin haske kan wasu abubuwa da kungiyar bisa jagorancinsa ta sa a gaba. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:

Wane karin haske za ka yi ma na kan abubuwan da ka kaddamar a yau?

Lallai shugabancin wannan kungiya ta NURTW reshen jihar Kaduna ta kaddamar da wasu ayyuka guda biyu a nan ofishinmu da ken an garin Kaduna. Abubuwan da mu ka kaddamar su ne, fara gina kamfani a cikin harabar ofishinmu da za mu rika yin rowan roba da kuma na leda sai kuma wasu motoci kirar Sharon guda uku da mu ka kaddamar, duk dai a wannan rana.

Labarai Masu Nasaba

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

To shugaba, mene ne dalilin kaddamar da wadannan abubuwa biyu da ka ambata?

Babban dalilin shi ne, mu ganinmu a matsayinmu da Allah ya ba mu jagorancin wannan kungiya a yau, mun zauna mu shugabanni a matakin jiha, mu ka fara tunanin wasu hanyoyi za mu fito da su domin kungiya ta yi amannar tan a da na ta hanyoyin da kudade za su rika shigo ma ta?

Wannnan ne ya sa mu ka yanke shawarar fara aiwatar da abubuwa biyun da na bayyana ma ku, wato wannan kamfani da kuma motoci guda uku. Kuma abin da na ke son in bayyana ma ka shi ne shugabannin da suka shugabanci wannan kungiyar a jihar Kaduna, kowa ya yi abin da zai iya, domin ci gaban kungiyar, kuma sun bar tarihin da har abada, in har a na numfashi, ba za a manta kyakkyawar shugabancin da suka yi ba, tun mu ma Allah ya ba mu shugabancin, shi ya sa mu ma mu ka fara aiwatar da abubuwa biyun domin mu ma mu fara tunanin barin tarihi tun yanzu.

Kuma mu a halin yanzu ba maganar ofisoshi ne mu ke bukata ba, domin shugabannin da su ka gabata, kamar yadda na bayyana a baya, sun samar ma na yalwatattun ofisoshi na ko wane mukami a jiha, kuma ofishinmu ba haya mu ke yi ba, na mu ne na kanmu,shi ya sa mu ka fara tunanin aiwatar da waDannan abubuwa biyun. Ka ga in wannan kamfani ya fara aiki, to ba mu da matsalar kuDin shiga da za mu yi wasu ayyukan da su ka shafi ci gaban kungiyar da kuma ’ya’yan kungiyar baki daya, domin kudin shigar wannan kungiya ta mu guda daya ne kawai, wato tasoshin mota.

Wadannan motoci uku da ka kaddamar, za su karaDe jihar Kaduna daga nan cibiyar ofishin a nan garin Kaduna?

A ‘a, babu mota daya a cikin motocin da za ta kasance a a ofishinmu, domin mu shugabannin jiha, mun yanke shawarar inda motocin za su yi aiki, Daya mun bayar a tashar Kawo  sai Daya a Abuja Junction Daya kuma mu ka bayar da ita a babbar tashar mota ta dayar a fly-over da ke Kwangila ta karamar hukumar Sabon gari, kuma shugabannin kungiyar da mu ka danka ma su motocin ne za su yanke shawarar  wuraren da za su rika bi a sassan Nijeriya, ba jihar Kaduna kawai ba.

Yanzu ga wadannan ayyuka biyu manya kun saw a gaba, wani sako ka ke da shi ga shugabannin kungiyar na kananan hukumomi da sauran shugabanni baki Daya?

Babban kiran da zan yi ga shugabannin ako wane mataki, su zama ma su amana da taimakon mambobi da kuma duk wani fasinja da ya shiga tashar mota domin shiga mota zuwa inda za shi, duk wanda ya yi waDannan abubuwa da aka ambata, ya sauke nauyin da aka dora ma sa. kuma yadda shugaba zai kare hakkin direba, wajibi ne ya kare hakkin fasinjoji da ya shafi rayuwarsu da kuma dukiyarsu. Ga mambobi, duk abin day a same shin a dadi ko na kasin haka, lallai a kasance tare da shi, musamman in hadari ya same shi, ka da a juya ma sa baya, a ba shi duk tallafi da duk abin da dokar kungiya ta ta ce, haka shi ma fasinja.

A karshe, akwai kira da za ka yi ga wadanda ke shiga motocin haya a bakin titi, wato waDanda ba sa shiga tasoshin mota a duk lokacin da za su yi tafiya mai nisa, ba ma su tafiya a cikin gari ba?

Babu ko shakka Ina da kira gare su kuwa, domin kiran da zan yi shi ne, lokaci ya yi da al’umma za su fahimci muhimmanci shiga tasha a duk lokacin da za a yi tafiye-tafiye, domin a duk lokacin da mutum ya shiga moyar haya a bakin titi, in ya manta kayansa, a ina zai koma ya kai cigiya? Idan matsala ta same shi, a ta ina za a gane inda ya fito da kuma inda za shi?

To, wadannan matsaloli ya dace mai shiga mota bakin hanya ya lura das u, domin in an tuna, mutane nawa aka saan zarge wuyarsu, wasu an hallaka su, wasu sun shiga halin wahala a dalilin shiga mota a bikin titi. Ina son al’umma su lura da cewar, a cikin tasha, akwai inda a ke rubuta sunan fasinja da lambar wayarsa da lambar wani dan uwansa da ko da ya sami hadari, za a iya kirar dan uwansa a yi ma sa bayani. Kuma idan ma mutum ba shi da yalwataccen kudin mota ne, in har fasinja ya shiga tasha ya sami shugabannin kungiyar za su ba shi duk tallafin da ya ke bukata.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda A Ke Koma Wa Marhalar Farko

Next Post

Edward Kallon: Tasiri Da Mahimmancin Kafafen Yada Labarai A Duniya

Labarai Masu Nasaba

APC Da PDP

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

by Yusuf Shuaibu
4 weeks ago
0

...

Buba Marwa

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

by
1 month ago
0

...

Dakta Yusuf Sani

Ba Na Jin Dadin Yadda Ake Yi Wa Malaman Jami’a Kudin Goro — Dakta Yusuf Sani

by Yusuf Sani
2 months ago
0

...

Hodar

Rikita-rikitar Badakalar Hodar Ibilis Ta Su Abba Kyari

by
3 months ago
0

...

Next Post
Sai Mun Hada Hannu Za Mu Ci Moriyar Ma’adinai Da Kananan Sana’o’i –Edward Kallon

Edward Kallon: Tasiri Da Mahimmancin Kafafen Yada Labarai A Duniya

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: