Abba Ibrahim Wada" />

Burina Shi Ne Mu Sake Lashe Gasar Siriya A – Ronaldo

Shahararren dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa babban burinsa a wannan kakar bai wuce yaga kungiyar tasa ta sake lashe gasar firimiyar bana ba saboda yadda gasar take basu wahala a bana.

Jubentus ta doke Inter Milan kuma ta haye teburin gasar Siriya A a wani wasa da aka buga ba tare da ‘yan kallo ba bayan da hukumar kula da gasar tace za’a dinga buga wasannin Siriya A ba tare da ‘yan kallo ba saboda cutar Coronabirus data addabi kasar.

Wannan na daya daga cikin manyan wasannin kwallon kafa a kakar wasa ta bana a Italiya, kuma za a ci gaba da buga wasannin babu ‘yan kallo a filayen wasanni daban-daban na kasar  har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Aaron Ramsey da kuma dan Argentina, Paulo Dybala ne suka zira kwallon da da ta baiwa Jubentus damar darewa kan teburin da maki daya a saman SS Lazio.

Da alamun kalubalen gogayyar da Inter Milan ke fama da shi ya zo karshe tun da abokiyar hamayyarta Jubentus ta ba ta maki 9 tsakanin kungiyoyin biyu wanda hakan yake nufin Jubentus tayi mata nisa.

Cristiano Ronaldo bai ci kwallo ba a wasan, wanda karon farko ke nan hakan ta faru a gasar Siriya A tun 10 ga watan Nuwamban bara sai dai dan wasan ya bayyana cewa babban burin nasa dai bai wuce su lashe gasar ba.

Kawo yanzu mutum 366 ne suka mutu a Italiya dalilin cutar Coronabirus, kuma akwai mutum 7,375 da suka kamu da ita sannan kuma ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana cewa an killace sama da mutum miliyan 16 saboda cutar.

 

Exit mobile version