Burinmu Shi Ne Mu Samar Da Zaman Lafiya A Cikin Al’umma —Farfesa M.B Shitu

Farfesa Muhammad Bello shitu na jami’ar Bayero ya bayyana cewa burin kungiyar” cigaban ilimi bai daya da raya al’umma” wadda akafi sani da  ”ICEADA” shine wanzar da zaman lafiya acikin al’umma ta hanyar koyawa matasa sana’o’I domin dogaro dakai.

Farfesan wanda shine shugaban kungiyar, yayi wannan jawabi ne a wajen rufe koya sana’o’I ina kwana biyu da gidauniyar ICEADA din ta shirya a unguwar Zawaciki dake karamar hukumar Ungogo dake jihar kano.

‘Burin mu shine tallafawa matasa maza da mata domin dogaro da kai kuma hakan zai kawo cigaba acikin al’umma tare da zaman lafiya mai dorewa” in ji Farfesan

Ya kara da cewa ”babu wata al’umma da zata cigaba batare da zaman lafiya ba kuma zaman lafiya yana samuwa ne lokacin da matasa suk dukufa wajen neman nakansu batare da suna zaman banza ba”

Yace sun shirya wannan koyar da sana’o’I ne ga unguwanni  16 cikin kananan hukumomi 11 acikin jihar kano inda yace ko a kwanakin baya sun shirya wani wasan kwallon kafa domin hada kan matasa da kuma nuna musu cewa zaman lafiya yafi komai.

A karshe farfesan yayi kira ga gwamnati data dage wajen samarwa da matasa abubuwan yi domin samun dawwamammen zaman lafiya a tsakanin al’umma sannan kuma da hakane za’a samu al’umma tagari mai son cigaba.

Shi ma a nasa bangaren Malam Aminu Muhammad Yahaya, wanda shi ne yake koyawa wadannan samari sana’o’in, ya bayyana cewa babu wata hanya da za’a kawo zaman lafiya indai matasa zasu zauna babu abinyi inda kuma a karshe yayi kira ga wadanda sukaci gajiyar shirin dasu dage wajen bunkasa abinda suka koya ta hanyar komawa inda suka fito domin koyawa yan uwansu.

Shamsuddeen Jafar Sani,  wanda yana daya daga cikin wadanda sukaci gajiyar wannan koyan sana’o’I yace yanada burin cigaba da abinda yakoya inda yace ya koyi yadda ake hada jakar mata da kuma yadda ake hada kayan mata da suka hada da Sarka da abin kunne da sauransu.

Asma’u Garba Ibrahim, wadda tafito daga bangaren mata a wadanda sukaci gajiyar wannan shiri Tace tayi farin ciki da samun wannan dama kuma ta bayyana cewa ta koyi abubuwa da dama da suka hada da hada jaka da yadda ake kwalliyar mata musamman a lokutan bukukuwa.

A karshe Dakta Auwal Halilu, malami a sashin kula da ilimin manya na jami’ar Bayero wanda kuma shine babban mai bada shawara kan ilimi a gidauniyar ICEADA, yaja hankalin matasan dasuyi kokarin ganin sunyi amfani da abinda suka koya domin dogaro da kai da kuma kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Shirin koyar da sana’o’I dai na ICEADA zai dauki kusan makonni uku anayi inda aka tsara za’a dinga yin kwanaki biyu a duk unguwar da aka tsara zataci gajiyar wannan shiri.

 

Exit mobile version