Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home ADON GARI

Burinmu Tallafawa Mata Da Kananan Yara —Hajiya Murjanatu

by Tayo Adelaja
September 11, 2017
in ADON GARI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hajiya Murjanatu Sulaiman Shika itace shugabar cibiyar ‘Women Connect Initiative’, ta kasance malama a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda take karantar da harshen turanci. A wannan tattaunawar da ta yi da Jaridar Leadership A Yau, ta bayyana irin ayyukan da cibiyarta ke gudanarwa.

Zamu So Mu Ji Sunanki Da Takaitaccen Tarihinki

Sunana Murjanatu Sulaiman Shika, ni ‘yar Shika ce, kuma na yi makaranta a Zangon Shanu, dake Samaru. A can na yi firamare da sakandare a makarantar ‘Unity School’, bayan na gama ne kuma na tafi jami’ar Ahmadu Bello inda na karanci harshen turanci a digirin farko, a fannin kuma nayi digiri na biyu. Bayan na kammala ne aka bani aikin koyarwa anan sashen koyar da harshen turanci na jami’ar ta Ahmadu Bello, Zariya. Na yi aure, ina da ‘ya ‘ya uku. Haka kuma ni ‘yar rajin kare hakkin bil’adama ce, musamman fannin da suka shafi yara da mata.

 

Masu karatu zasu so su ji suna da ayyukan cibiyarki

Sunan cibiyarmu ‘Women Connect Intiatibe’, kuma ayyukanmu duka akan mata ne, da kuma ‘ya ‘ya mata. Mun fi mayar da hankali akan lamurran da suka shafi matan, ta yadda za a taimakawa juna, da cigabanmu gabadaya. Duk inda muka samu labarin mace da ke da kokari amma ta gaza samun wanda zai tallafa mata, mukan je mu kai tallafi. Mukan shiga sako-sako mu kai tallafi. Irin wannan ba wai yana nufin ka je kauyuka ka fito da mace ba, a’a a wurin da take za ka tallafa mata da abin da zai yiwu ta yi sana’a, don ta samu ta cigaba. Wasu za ka ga suyan kosai ne sana’arsu, wasu dinki ne, da sauransu.Saboda haka mu kan yi la’akari ne da abubuwan da mace tafi iyawa, sai mu tallafa mata a kai, wasu ma basai sun fita daga gidajensu ba, a cikin gida suke gabatar da sana’o’insu, suna taimakawa ‘ya‘ya da mazajensu. Su kuma ‘ya‘ya mata muna tallafa musu ne akan karatu, don kuwa duk macen da ka bata ilimi ka gama mata komi. Saboda komi kankantarsa da shi zata yi amfani ta koya ma ‘ya‘yanta, dan abin nan da ta koya da shi za ta yi amfani ta tallafawa ‘ya’yan nata.

 

Wadanne abubuwa ne suka baki sha’awan assasa wannan cibiya?

Gaskiya zance iyayena; Babana da Mamana.Babana yana da makaranta, tunda na taso na ganshi, makarantarshi kamar ta sadakace zance ma, sai ka ga mutum yana da ‘ya‘ya biyar, amma biyu yake biyawa, ukun kumasuna karatu kyauta, tamkar dai abin da ake yi yanzu na bayar da tallafin karatu ‘Scholarship’. A kullum mun taso mun ga mahaifinmu yana tallafawa mutane, haka ma babata, aikin kenan taimako. Shi yasa ma ba zan iya cewa ga takamaimen lokacin da na soma wannan tafiya ba saboda kawai na taso ne na ga na fara.

 

Wadanne wurare cibiyarku take gudanar da ayyukanta?

Muna da sassa a wurare daban – daban, ba kawai a Kaduna muke gudanarwa ba. Muna dashi a Zamfara, muna dashi a Kano, muna dashi a Sokoto, a Katsina da Abuja da Kaduna. A hankali muke kara fadadawa. Amma asalin hedikwatarmu tana Kaduna. A hankali muke kara samun mutanen da suma suna son su cigaba da wannan aikin tallafi, da haka muke fadadawa a wasu wuraren.

Mu kan fuskanci matsalolin rashin tallafi daga jama’a. Saboda duk wanda zaka tallafawa, dole sai da kudi zaka yi amfani dashi. Mu yawancinmu muna aiki, da kudadenmu muke amfani, sai kuma akwai wani shiri da muka gabatar na‘Skill Ackuisition’ wanda dashi za a ba mata horon sana’o’i, akwai wani mutum da ya bamu tallafi da kekunan dinki, shi ne wanda ya taba fitowa ya bamu tallafi. Amma duk yawancin abubuwanmu da kanmu muke yi. Idan sauran basu da shi, ni nake bayarwa, musamman bias la’akarin yanayin da aka tsinci kai yanzu, na babu. Sai ya zama dan kankanin abin da muke dashi, dashi muke tallafawa don ganin mun canza ma marasa karfi rayuwa. Kuma muna kokarin fita mu nunawa mutane irin ayyukanmu don su taimaka, saboda wannan aikin sadaka ne.

 

Wadanne fannoni kike ganin kun fi bukatar tallafin al’umma?

Eh to, gaskiya akwai fannoni da yawa. Na daya akwai shiri da muka yi na ‘No hunger feeding campaign’, shi wannan na abinci ne, saboda mun yarda da cewa bai kamata wani ya kwana da yunwa ba, kowa ya kamata ya samu abin da zai ci ya kuma ciyar da ‘ya‘yansa. Wannan shirin muna zuwa ne gari – garin da basu ma sanmu ba, bamu ma sansu ba, da kuma kauyukan da bamu taba tunanin zamu shiga ba. Idan ka ba mutum abinci ya ci ka gama mishi komi. Da haka ne muke iya samun daman shawo kan iyaye har mu sanya ‘ya’yansu a makaranta. Idan ka basu abinci, zasu aminta da kai.Idan muka ga ‘ya ‘yansu muka tambayesu me yasa basu zuwa makaranta, sai su ce ai basu da yadda zasu yi, sai mu ce musu toh mu su bamu dammar sanya su a makarantar. Sukan kuma amince mana.Kenan mu kan samu nasarar yin abubuwa guda biyu a lokaci daya.Wasu matsalolin sai mun shiga kauyuka muke ganewa, wasu lokutan da hawaye muke fitowa daga wuraren da muke zuwa.Akwai ranar da muka raba shinkafa a Kudancin Kaduna, watanni uku kafin bukin Ista ‘Easter’. Sai wata yarinya ta ke cewa mahaifiyarta, yau zasu ci shinkafa, yau zasu ci shinkafa.Sai mahaifiyar ta ce mata, ai shinkafan nan daureshi za a yi sai bukin Ista za a dafa a ci. Sai Ista fa aka ce, ka ga kenan mutane na cikin wani irin hali. Har yau ana kirana ana godiya akan wannan tallafi. Toh irin wadannan abubuwan muna rokon mutane da su rika tallafawa, a rika taimakawa mutane. Akwai kuma maganan makarantar yara mata, muna bi muna janyosu da Magana mai dadi, muna kuma koya musu sana’o’in hannu; irinsu saka, dinkin tabarma, dinki, yanzu ma mun samu wacce tace zata koyawa matan kimiyyar kwamfuta.

Mu abin da muke so, ba kawai ka zo ka bamu kudi ba, mutum na iya zuwa ya bamu kayan aiki, wanda zamu koya musu sana’o’i. Wanda kaitsaye zaka ga amfanin tallafin da ka bayar saboda kaitsa ye mutanen ne zasu amfana.

 

Daga karshe wanne sako kike da shi ga wadanda suke cin moriyar tallafinku?

A kodayaushe ina cewa don yau ba ka san da mutum ba ya zo ya tallafa maka, ya kamata ne kai ma kayi kokarin ka samu ka taimakawa wani. Ba ki sanni ba, amma nazo na baki, ke ma ki nuna min wannan abin ya shige ki, ki tallafawa na kasa da ke. Akwai matar da ta yi wannan a Zariya, an bata kayan yin sana’ar kosai. An gayyace niamma ban samu zuwa ba, sai dai aka dauko mana hotuna. Yadda lamarin ya afku kuwa, shi ne; bayan ta dan yi karfi sai ta siyo buhun wake da kayan yin kosai ta tallafawa wata ita ma da ke da matsala, wannan ya matukar burgeni. Akwai wadanda muka basu dubu 1,000 kowanne, suma suna yin sana’o’i kanana a gida, suma sun yi matukar jin dadi, saboda dashi suke taimakawa kawunansu. Kodayaushe muna ce musu a ci gaba da tallafawa juna, don a rage samun matsaloli a tsakankanin mata.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

An Kusa Kawo Karshen Barace-barace A kasar Nan —Goni Sheikh Musa

Next Post

Bankin Bunkasa Noma Zai Kashe Dala Biliyan 400 A Kasar Nan

RelatedPosts

Aikin

A Rayuwata Ban Taba Sha’awar Aikin Gwamnati Ba – Rukayya Abubakar

by Muhammad
1 day ago
0

Da yawa masu karatun boko idan ka tambaye su shin...

Mata Mu Farka: Jan Hankali Ga ‘Yan’uwa Mata Da Kuma Tsarabar Girki

Mata Mu Farka: Jan Hankali Ga ‘Yan’uwa Mata Da Kuma Tsarabar Girki

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Daga Sister Iyami Jalo Turaki Iyaye mata mu farka daga...

Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna – Inji Aisha Galadima

Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna – Inji Aisha Galadima

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Daga Amina Bello Hamza Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa...

Next Post

Bankin Bunkasa Noma Zai Kashe Dala Biliyan 400 A Kasar Nan

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version