Burundi Ta Ce Ba Za Ta Ba ICC Haɗin Kai Ba

Gwamnatin Burundi ta ce ba za ta ba da haɗin kai ga kotun manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ta ICC haɗin kai a kan aniyarta na gudanar da bincike kan zargin take haƙƙin bil Adama a kasar ba.

Ƙasar da ke Afrika ta Gabas ta fice daga yarjejeniyar kotun duniyar ta ICC, amma kuma kotun ta ce fice war ba zai hanata aiwatar da aikinta a cikin ƙasar  kan ƙarar laifukan da aka gabatar mata a baya ba.

Da take jawabi ga manema labarai a babban birnin Burundi Bujumbura, Ministan shari’a Aimee Laurentine ta ce kotun ICC ba ta da hurumin gudanar da bincike a cikin ƙasarta.

Ta ce Burundi babu ruwanta da batun wata shawara da kotun za ta ɗauka. Gwamnatin Burundi ba za ta yi aiki da wata shawarar kotun ba, kuma tana ƙara jaddada matsayinta cewar ba za ta ba kotun ICC haɗin kai ba, sannan ba za ta lamunta da aniyar Kotun na neman shiga ƙasar Burundi ta gudanar da aikinta bisa zalunci ba.

Martanin gwamnati Burundin na zuwa ne kwana guda bayan da alƙalai uku na Kotun ICC suka ba da umarni ga mai shigar da ƙara da ya buɗe bincike a kan zargin take haƙƙin bil Adama da aka yi a ciki da wajen ƙasar Burundi tsakanin Afrilun shekarar 2015 da kuma Oktoban shekarar 2017.

Burundi ta zama mamban yarjejeniyar Rome Statute wacce ta kafa kotun manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ta ICC a shekarar 2004. Ƙasar ta ba da sanarwar ficewarta daga wannan yarjejeniya a cikin watan Oktoban bara kuma sanarwar ta fara aiki a watan da ya gabata. Burundi tana zargin kotun da auna ƙasashen Afrika.

Exit mobile version