Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTON MUSAMMAN

Cacar Wasanni A Nijeriya: Ba Doka Ta Hana Ba?

by Tayo Adelaja
October 30, 2017
in RAHOTON MUSAMMAN
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sabo Ahmad

Bincike: Duk da cewa, akwai dokar da ta haramta yin cacar wasanni a Nijeriya, amma kullum sai ƙaru wa take yi, ta hanyar salo iri daba-daban. Binciken da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya yi, ya nuna cewa,‘ya Nijeriya na kashe zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 1.8 a kan cacar wasannin a kowace rana. Haka kuma binciken ya tabbatar da cewa, taulauci da matsin tattalin arziƙin da aka shiga a Nijeriya, wanda ya haifar da rashin aiki yi, na daga cikin abubuwan da suka kawo wannan caca wadda take ƙaru wa kamar wutar daji a faɗin Nijeriya. Wani yaro Abiodun Kalejaiye ɗan kimanin shekara 16, ya ce, ya fara cacar wasan ne a cikin watan Janairu na shekara ta 2017, lokacin da ya haɗu da wasu abokai da ke zaune a unguwar Agege cikin garin Legas, waɗanda ba su da wani aiki ban da wannan cacar, saboda suna makwabtaka da inda ake yinta.

samndaads

“kodayake da farko na ɗauka cewa wasa ne kawai, wanda za a yi shi domin nishaɗi, amma sai daga baya na gano cewa, ashe caca ce” wanda ya gaya wa majiyarmu daga gidan da ake wannan caca.  Sannan kuma ya ci gaba da cewa,“Idan ka saka Naira150, a wasan kana iya cin Naira dubu 5, zuwa Naira dubu 8, koma fiye da haka, ya danganta da yadda wasan ya fito” wanda ya bayar da cikakkaen bayani cikin harshen Yarabanci.

Faɗa wa cacar da Abiodun ya yi, a matsayinsa na ɗan shekara 18, ya saɓa wa dokar ƙasa kamar yadda majiyarmu ta binciko.

“Duk shagon da ya ba yaro wanda bai kai shekara 18 ba,  takardar shiga gasar cacar,  ya aikata laifi, wanda za a iya cinsa tarar Naira dubu 20 ko ɗauri na ƙasa da shekara ɗaya, ko kuma a haɗa duka,” kamar yadda dokar ta ce.

Amma saboda rashin kiyaye doka a ƙasa ya sa dubban yara irin su Abiodun, suka faɗa cikin irin wannan caca har ma ɗaliban da ke makarantun sakandire, su ma da ya wa daga cikinsu sun jefa kansu a cikin wannan caca bisa dalilai daba-daban, musamman a unguwar Agege, da ke cikin garin Legas.

 

Cacar Wasan Na kawo Kuɗi Masu yawa.

Cacar wasa Kasuwanci ne da ake samun kuɗi da shi saboda haka, Abiodun ya ɗanɗana wannan samu tun yana ƙarami, don haka ya zama ɗaya daga cikin ƙaramin yaron da ya yi suna a dukkan inda ake buga wannan caca a unguwar Agege da ma su sassa na ƙasar nan. Cacar wasan ta taƙunshi sukuwar dawaki da tsren kare da tseren keke, da makamantansu.

“lokacin da nake buga ‘Aja-n-sare’ nakan ci kuɗi ba kamar sauran abokaina ba, wannan wasa yana da samu” in ji Lukumon Sha’ibu da ke irin wannan cacar a wata cibiyar cacar a garin Ijoko cikin jihar Ogun wanda ya faɗa wa majiyarmu da ke gudanar wannan bincike, sannan ya nuna wa majiyar ta mu abubuwa dabn-daban da ya ci a wajen cacar, irin su radiyo da waya.

Shi ma wani yaro ɗan shekara 17 da ke gyaran radiyo ya bayyana cewa, ta hanyar wannan cacar ne ya samu kayan aikin da yake gudanar da sana’arsa ta gyaran rediyo, wadda kuma da ita yake cin abinci da ita a halin yanzu. A shekara ta 2016, John Chukwudi, da ke Oddo Street, unguwar Obalende Legas ya ce, da kuɗin cacar ya sayi fom ɗin, JAMB, kuma ya ja abokansa zuwa wannan kasuwanci, wanda ya bayyana a matsayin kasuwancin da ake samun riba a cikinsa. Mutane na iya cewa, komai dangane da wannan cacar wasan , amma ni dai kam ta biyani domin kuɗin da na samu ta wannan hanyar ne na sayi fom ɗin JAMB, sai ya kasance sakamakona bai yi kyau ba, amma bana zan sake saye kuma ta wannan hanyar zan samu kuɗin in ji wani ɗalibi.

Ma fi yawan yaran da suke wannan cacar sun bayyana cewa ba ta shafar karatunsu, sai dai binciken da muka yi ya tabbar mana da cewa, wannan labarin ƙanzon kurege ne, domin sukan je wajen cacar har lokacin karatu.

 

Yawan Ƙananan Yara Masu Cacar Na Ƙaru wa.

Kamar yadda Hukumar kula da wasanni ta jihar Legas, ke cewa doka ta hana duk wani yaro da ke ƙasa da shekara 18 a ba shi damar yin cacar wasan a kowace cibiya da ake gudanar da irin wannan caca. Wakilinmu da ya ziyarci wasu cibiyoyin wannan caca da ke Legas da Ogun ya ga an rubuta a ƙofar shiga cewa, ba a yarda yaro ya zo gurin ya yi cacar ba, musamman ma mata.

“Wata yarinya ‘yar shekara 15 ta bayyana cewa, su wannan dokar ba za ta yi aiki a kan su ba, saboda sun saba suna zuwa suna yi, saboda haka babu wanda ya isa ya hana su, ita ma wata Osita  Oregun, da ke  Ikeja, a garin Legas mai kimanin shekara 14, ta ce, ma fi yawan gurare ana ƙyale su su yi cacar sbods masu gurin na neman kuɗin da za su biya ma’aikatansu.

A wani shago da ke Agege kan hanyar zuwa sitadiyan, wani ɗan makaranta John Kingsley, ya bayyana wa wakilinmu cewa, duk da cewar yana kula da shago,yakan samu lokaci ya je ya buga cacar. Akwai shagunan da muke zuwa muna yin wannan caca kamar sahago mai lamba IMG_20170929_da 105132  a unguwar Betnaija a Legas

Igwe Charles, ɗan kimanin shekara 15 da ke  Broad street, Legas Island, ya ce, sukan shiga kowane shago a garin aLegas su yi cacarsu ba tare da takura ba.

Haka ma wani ɗan makaranta ‘Show-boy’ ya ce, a wasu guraren za ka ga jami’an tsaro na zuwa su ma suna yin cacar don kada garaɓasar samun da ake ta wuce su

 

Mun San Yin Cacar Ya Saɓa Wa Doka

Amos, ɗan shekara 16 wanda ke zsaune a  Oshin Street, kusa da Kudirat Abiola way, Legas, ya ce  duk da cewar ya san caca babu kyau, amma yake yi saboda ya samu kuɗin da zai biya buƙatun rayuwarsa. Saboda duk abin da yake son saya zai iya saya da kuɗin cacar, sannan kuma zai iya yi wa kansa hidimar makaranta ta wannan hanya, ya ce ba ya sa kuɗi masu yawa a cacar, saboda kuɗin da ya taɓa ci ma fi yawa su ne, Naira10,000.

Shi ma wani yaro ɗan shekara 16 Uche Michael, wanda ke riƙe da tikitin wasan, ya ce ya san cewa, ba kyau ƙaramin yaro ya yi caca.

“Ina yi ne domin in samu kuɗin makaranta, kuma in biya wasu buƙatuna,” in ji shi.

Suleiman Anisere, wanda ke da shago a Amode close, Olusosun, Kudirat Abiola way, Legas, cewa ya yi, “muna hana yara yin caca a nan, sai dai ba zai yiwu kuma mu hana su a wani wurin da ba namu ba”.

Mai shagon Winners Golden Bet a Oregun, Adeyemi Adewale, ya tabbatar da cewa, cacar da ‘yan makaranta ke yi na tauye su wajen karatu, sannan kuma yana kawo koma baya wajen ci gaban ƙasa. Zai sa kuma yaran shi ga miyagun ɗabi’u. Saboda haka ina shawartar yara su guji yin wannan cacar, domin za ta tauye musu rayuwa”.

Kodayake wani jami’in Hukumar daga Legas ya mayar da matarni bisa wannan zargin da ake yi wa hukumar.

Gbemisola Ajibose, shi ne sakataren Hukumar kuma mai ba ta shawara a kan harkokin shari’a, ya ce, Hukumar na ɗaukar matakin hana ƙananan yara yin cacar wasan.

Lokacin da wakilinmu ya tuntuɓi Hukumar kan batun wannan ƙalubale, ta ce tana iya ƙoƙarinta wajen ganin dokar hana yara cacar na aiki sosai da sosai.

“Ita ma Hukumar kula da cacar wasan ta jihar Legas ta ce ba ta yin ƙasa a gwiwa wajen ganin an bi dokar sau da ƙafa.

“Yana daga cikin abin da kullum  muke sa ido a kansa na ganin cewa dokar hana ƙananan yara cacar wasa na aiki kamar yadda ya kamata a jihar Legas”, in ji Hukumar

Saboda haka, sai Hukumar ta buƙaci goyon bayan jama’a da su sanar da ita a duk inda suka ka ga ana yi wa dokar hana yaran cacar wasan karan-tsaye, domin ɗaukar matakin da ya dace.

SendShareTweetShare
Previous Post

Addini Da Siyasa: Rikici Tsakanin Ƙabilun Nijeriya

Next Post

Watsi Da Mata Da Matasa Suka Sa Na Fito Takarar Gwamnan Bauchi –Bahijja

RelatedPosts

Gwamna Masari

Satar Mutane Ta Zama Harkar Kasuwanci – Gwamna Masari

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Satar mutane, musamman ta bangaren yin garkuwa da mutane, ta...

Ba Mu Taba Samun Kowane Irin Tallafi A Kebbi Ba – Manoman Kankana

Ba Mu Taba Samun Kowane Irin Tallafi A Kebbi Ba – Manoman Kankana

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Duk da irin gagarumar rawar da manoman kankana ke takawa...

JIBWIS-FCT

Kwamitin Tallafa Wa Marayu Na JIBWIS-FCT Ya Gudanar Da Taron Karshen Shekara

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Kwamitin tallafawa marayu na Jama’atu Izalatul Bid’a Wa’ikamatis Sunnah dake...

Next Post

Watsi Da Mata Da Matasa Suka Sa Na Fito Takarar Gwamnan Bauchi –Bahijja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version