Cafke Nnamdi Kanu Kanu: Malami Ya Yi Wa Lauya Madu Wankin Babban Bargo   

Lauya

Daga Abubakar Abba,

A jiya Laraba, Atoni Janar na Tarayya kuma Minitan Shari’a Abubakar Malami ya yi kakkausar suka kan furucin Kelechi Madu bayan cafke jagoran ‘yan a ware na yankin Biyafara Nnamdi Kanu.

A wasu daga cikin furucin na Madu ya danganta Malami a matsayin marar alfanu ga fannin shari’ar kasar nan kuma bai da ce da kujerrar da yake a kai ba.

A martanin na Malami, ya yi kira ga mahukuntan kasar Kanada da su yi watsi da furucin na Madu domin furucin nasa, ya saba wa dokar kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, abin kunya ne furuncin na Madu, musamman ganin cewa, Nnamdi Kanu arcewa ya yi bayan an bayar da belinsa, inda kuma aka sake samun nasarar cafke shi don ci gaba da fuskantar shari’a.

Ya ce, abin a bayyane yake, an bi ka’idojin shari’a, Nnamdi Kanu ya taka hurumin beli, inda ya kara da cewa, babu wata doka da aka taka wajen cafko Kanu.

Malami ya ce Kanu  ya more waklicin lauyan da yake kare shi, sannan ba a taba hana masa ‘yancinsa ba duk da cewa, tuni Gwamnatin Tarayya ta haramta kungiyar IPOB.

Malami ya kara da bayyana cewa, shin Madu ma kana ne a lokacin da Nnamdi Kanu ke yin amfani da kalaman tunzura, da janyo tashin hankali a kasar nan? Kuma shin, Madu, a matsayinka na lauya kake goyon bayan wanda ya tsallake beli kuma ake zargi da aikata ta’adanci tare da cin amanar kasa? Sannan me ya dakatar da kai Madu bayyana irin laifukan da Kanu ya tafka wa kasa tare da magoya bayansa?”.

A cewar Malami, yana  kyau a ilimantar da  Keleche Madu kan jahilcin da yake da shi na cewa, kasarsa ta haihuwa Nijeriya da kuma kasar Kanada, inda yake yin ikirarin yana gudanar da aikin lauya, dukkan su sun rattaba hannun yarjejeniya kan cafko duk wani dan kasashen biyu da ya tsallake beli ko kuma ya aikata laifin cin amanar kasa da a dawo da shi kasarsa don a yi masa hukunci kamar yadda doka ta tanadar.

Ministan ya yi nuni da cewa, babban abin kunya ne a matsayin Madu na babba a fannin shari’a na lardi, ya gaza sanin ilimin dokokin kasar da kuma sanin ka’idojin dokokin kasa da kasa na kasar da yake da zama.

“Ina son in ja hankalin Madu kan karkashin dokar kasar Kanada ta R.S., C 1985, c. C-46:1-sakin layi na biyu kan wanda ya aikata mugun laifi da kuma cin amanar kasa da kuma sauran hukuncin ta.”

Ya kara da cewa, sashe na 46 daya a cikin baka ya bayyana cewa ga duk wanda aka samu ya ci amanar kasa a Kanada na daya ko ya  kashe ko kuma ya yi yunkurin hallaka Sarauniyar kasar ko kuma wani sashe na jikin mutum ya samu rauni ta sanadiyyarsa, tabbasa ya yi yunkurin kisa ne ko lalatawa kuma hukuncn wanda ya aikata hakan zaman gidan kaso  ne.

Ya ce,  na biyu kuma an tanadi hukunci kan wanda ya hari kasar Kanada da yaki,  inda na uku kuma duk wanda ya taimaka wa wani makiyi kan a far ma kasar Kanada da yaki  ko a kan duk wani jami’in tsaronta, nan ma kasar ta tanadi hukunci.

Ya bayyana cewa, sashe na 46, na biyu a cikin baka ya fayyace cewa, duk dan kasar Kanada da aka samu da cin amanar kasa ko yin amfani da karfi don kifar da gwamnatin kasar ko tayar da tarzoma,  akwai hukuncin da kasar ta tanadar.

A cewar Malami, haka idan ba tare da yarjewar mahukuntan kasar ba, in har wani dan kasar ya fitar da wasu bayanai ko kuma ya yi kuskuren samar da wasu bayanai ga wani wanda ba dan kasar ba, a game da Rundunar Sojin kasar   ko wani shiri, mahukuntan kasar za su iya danganta hakan  a matsayin yin kutse ga fannin sha’anin tsaron kasa.

Malami ya yi kira ga Madu da ya kawar da jahilcinsa da ke a zuciyarsa domin ya koyi ilimin doka kafin ya bude baki ya yi wani furucin batanci, domin in ba haka ba, zai ci gaba da zubar da mutuncinsa ne a idon duniya kan aikin na lauya da yake ikirarin yana da ilimi a kai.

Exit mobile version