Connect with us

WASANNI

Cahill Ya Amince Da Komawa Galatasaray

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Garry Cahill ya amince da komawa kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray dake kasar Turkiyya bayan da tuni ya amince da albashin da kungiyar zata dinga biyansa.

Tun bayan da kungiyar Chelsea ta canja sabon mai koyarwa Mauricio Sarri dai Cahill baya samun buga wasa inda har yanzu bai buga wasa ko daya ba cikin wasanni uku da kungiyar ta buga na gasar firimiya ta bana.

Da farko dai dan wan ya bayyana cewa yanason cigaba da zama a kungiyar ta Chelsea domin yayi kokarin gamsar da kociyan kungiyar domin yaci gaba da yin amfani dashi sai dai yanzu labari ya canja inda ya amince da tafiya kasar Turkiyya.

Cahill, mai shekara 32 a duniya zai bar Chelsea ne bayan yayi shekaru 6 yana bugawa kungiyar wasa tun lokacin da yabar kungiyar Bolton Wanderers a shekara ta 2012 akan kudi fam miliyan 25 kuma ya lashe kofin firimiya da Chelsea a lokacin Mourinho.

Saura dai kwantaragin shekara daya yarjejeniyar dan wasan ta kare da Chelsea kuma tuni Galatasaray ta shirye kashe kudi domin kara karfi bayan tasamu tikitin buga gasar zakarun turai a wannan kakar.
Advertisement

labarai