CAN A Bauchi Na Neman A Rushe Kotunan Shari’ar Musulunci Cikin Gaggawa

 CAN

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

 

Reshen kungiyar Kiristoci ta kasa a Jihar Bauchi (CAN) ta bukaci a gaggauta rushewa da daina amfani da tsarin kotunan shari’ar Musulunci a fadin kasar nan, ko kuma su ma a kirkira musu kotunansu na (Kotunan gargajiya na addinin Yesu) sannan kuma a samar da wata hukuma daga cikin kundin tsarin mulkin kasa da za ta lura da zallar hakkin Kiristoci.

Kungiyar ta ce, sashi na 10 da ke kundin tsarin mulkin Nijeriya ya haramta ma wata addini ko wani bangare ko jinsi samar da wata hukuma ta addini da za ta kula da zallar muradin addini guda a kasar nan.

Kan haka ne, suka ce kafa hukumar shari’ar musulunci da kotunan shari’ar musulunci ya saba wa dokar kasa kuma haram ne a kundin tsarin mulkin kasa, don haka ne suka ce ko a rushe hukumar shari’ar musulunci da kotunan shari’ar Musulunci ko kuma su ma a kafa musu nasu sabuwar hukuma da kotunan da za su tafiyar da tsallar harkokin Kirisoci a wannan kasar.

A bukatar da CAN ta gabatar a gaban kwamitin majalisar wakilai kan jin ba’asi dangane da waiwaye kan kundin tsarin mulkin Nijeriya a Bauchi, CAN ta ce an nuna mata wariya da rashin adalci na samar da hukumar shari’ar musulunci zalla.

Don haka ne CAN ta kara da cewa, “Samar da kotunan shari’ar Kiristoci tare da hukumar da zai ke kula da harkokin kiristoci ne zai nuna cewa ana tafiya da kowa da kowa ba tare da nuna wariya ga wani sashi ba a cikin kundin tsarin mulkin kasa.”

Sannan kuma kungiyar ta ce idan aka kafa kotunan shari’ar Kiristoci zai taimaka musu wajen kula da zamantakewar aure, harkokin rayuwa, sasanta tsakani, kyautatuwar rayuwa da kuma kara bin tafiyarsu dari bisa dari.

CAN ta lura da cewa cigaba da amfani da tafiyar da hukumar shari’ar Musulunci da gwamnatin tarayya da jihohi ke yi ba tare da samar da wata hukumar kiristoci da za ta yi daidai da na musulmai ba, to tabbas rashin adalci ne tsagwaranta kuma hakan ya saba wa dokar kasa, don haka ne suka nemi masu ruwa da tsaki a fannin tsara kundin tsarin kasa da su yi nazarin wannan batun dari bisa dari.

Wakazalika, CAN ta kuma ce a kotunan shari’ar musulunci da hukumar shari’ar Musulumci babu wani kirista ko da guda daya wanda ke aiki a wajen, “Hakan na kara nuna irin wariya da ke akwai. Don haka muna neman namu hukumar da za ta yi daidai da na musulmai.”

Exit mobile version