Connect with us

LABARAI

CAN Da JNI Sun Yi Shelar Mafita Ga Rikicin Benuwai

Published

on

Duk wani kokari da za a yi domin warware rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi a Jihar Binuwai, matukar ba a yi aiki da dokar samar da wuraren kiwo na musamman ba yanda ya dace, tabbas ba wata nasarar da za a samu, kamar yanda gamayyar kungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da kuma kungiyar Kiristoci ta CAN rassan Jihar suka ambata.

Wannan ita ce matsayar da kungiyoyin biyu suka cimma wa bayan kare wani taron da suka yi wanda kungiyar samar da fahimtar juna a tsakanin Addinai ta, Interfaith Dialogue Forum for Peace (IDFP), ta shirya tare da hadin kan cibiyar nan ta Bienna mai suna, KAICIID Dialogue Centre.

Taron wanda aka yi shi a garuruwan, Gboko, Oturkpo da Makurdi, ya sami halartan jami’an na kungiyoyin Jama’atu da ta CAN da ke Jihar. Da yake magana a wajen taron a garin Makurdi, Sakataren kungiyar Musulmin ta Jama’atu, Alhaji Baba Ahmed, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da an yi aiki da dokar ta samar da wuwaren kiwon na musamman ta hanyar samar da wuraren a cikin gaggawa.

Shi ma shugaban kungiyar ta CAN, Rabaran Akpen Leba, wanda Bishop Mike Angou, ya wakilce shi, ya yi kira ne ga al’umma da su girmama doka, ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.

“Musulmi da Kiristoci ba su da wata matsala a Jihar Binuwai. Damuwar dai tana kan rikici ne na manoma da makiyaya wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa.

Ya kamata gwamnati ta yi kokarin kawo karshen wannan kashe-kashen a cikin Jihar.

A taron na Uturkpo, wani jagoran na Fulani makiyaya, Alhaji Garba, cewa ya yi, mugunta da son rai ne suke haifar da rikicin, sai ya kirayi al’umma da su zama masu kamewa da kuma yafiya. Kasantuwar ni a nan Oturkpo ne aka haife ni, ba ni da wani wajen da zan koma da zai iya zama gida a gare ni. Alhaji Garba ya ce, in har mutane za su dauki tausayi na ‘yan adamtaka da kome ya warware.

Mutane da yawa da suka yi magana a wajen tarukan duk sun yi kira ne ga gwamnati da ta dakile hanyoyin da matasa kan bi suna shan muggan kwayoyi, suka ce kuma ya kamata a magance matsalar rashin aikin yi ga matasan.

Shugaban kungiyar ta IDFP a Jihar, Alhaji Ibrahim Yahaya, ya gode wa duk mutanan da suka gabatar da jawaban a wuraren tarukan, ya kuma ce shawarwarin da masu jawaban suka bayar a wurin taron za su taimaka wajen hada cikakken rahoton na su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: