Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

CAN Ta Jinjina Wa Gwamna Inuwa Bisa Kyautata Zaman Lafiya A Gombe

by Muhammad
January 11, 2021
in LABARAI
4 min read
Jinjina
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa zai ci gaba da samar da shugabanci na gari ga al’ummar jihar baki daya ba tare da la’akari da banbancin Kabila, addini ko ta siyasa ba; a bisa hakan ne ma, kungiyar Kiristoci ta CAN ta nuna gwamnan a matsayin jagoran tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.

samndaads

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakwancin kungiyar kiristoci ta kasa CAN reshen Jihar Gombe, yayin da ta kai masa gaisuwar Kirsimeti dana sabuwar shekara shekaran jiya a gidan gwamnati.

Gwamnan ya bayyana ziyarar da cewa tana da muhimmanci kuma nau’i ce ta godiya da al’ummar Kiristan jihar ke yi tare da nuna goyon bayan su ga gwamnati a kokarin da take yi na kyautata rayuwar al’ummar jihar.

Ya ce ‘‘Da muka hau kan karaga a shekara ta 2019, na sha rantsuwa da Alkur’ani mai girma a matsayina na musulmi cewa zan jagoranci jama’a da gaskiya da adalci da kuma daidaito, kuma na tabbatar ina yin iya kokari na wajen tabbatar da haka. Hakan ya sa muke aiwatar da ayyukan raya kasa a lungu da sako na fadin Jihar Gombe. Idan aka yi zancen hanya, mun kuduri aniyar samar da hanyoyi masu tsawon kilo mita dari-dari a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 11 da muke da su, a karkashin shirin mu na samar da hanyoyi, kuma muna kan aniyar mu ta cimma hakan.”

Gwamnan ya kafa hujja da hanyar da ake gudanarwa yanzu haka a karamar hukumar Balanga, dake zama daya daga cikin wurare masu munin yanayi da wuyan sha’anin yin aiki irin na hanya, lamarin da ya sa gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da yin hanya a yankin, ya na mai cewa da yardar Allah, gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa hanya ta hade yankin kudanci da arewacin karamar hukumar Balanga, wanda hakan zai baiwa al’ummomin kudancin karamar hukumar damar zuwa helkwatar karamar hukumar ba tare da sai sun ratsa ta Kaltungo, Billiri, Akko, Gombe da Yamaltu Deba ba.

Ya ce haka kuma lamarin yake a Malala da Dukkuyel na karamar hukumar Dukku dama wasu wuraren a fadin jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da ayyukan hanyoyi da makaranti da asibitoci da ababen more rayuwa masu nagarta don cin moriyar al’ummar jihar.

Sai ya bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa duk da cewa ana fama da matsin tattalin arziki sakamakon matsalolin da annobar korona ta haifar, gwamnatin sa za ta ci gaba da maida hankali kan ayyukan da suka wajaba a kanta don sauke nauyin da talakawa suka daura mata.

Gwamna Inuwan sai ya bukaci karin goyon baya ga duk sassan gwamnatinsa don ta cimma nasarar ayyukanta na alkhairi ga al’ummar jihar, yana mai cewa talauci da cututtuka da yunwa ba su da idon banbance kabila ko addinin mutum in sun tashi kama shi.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmanicin zaman lafiya, yana mai cewa matukar ba zaman lafiya, babu wani abun ci gaba da za a iya cimmawa, inda ya yaba da kokarin jama’ar jihar na rungumar zaman lafiya da ririta ta.

Game da wasu bukatu kuwa da kungiyar ta CAN ta mika wa gwamnan, gwamna Inuwa Yahaya, ya ce gwamnatinsa ba za ta kau da kai ba ga wadanda suka sha mata wahala, har ma wadanda ba cikakkun ‘yan siyasa ba, wadanda ke da gudunmowar da za su iya bayarwa a fagen shugabanci na gari.

Gwamnan ya kuma baiwa kiristocin tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kafa shugabannin gudanawar hukumar kula da ziyarar Ibada ta kiristoci ta jihar, yana mai cewa gwamnatinsa ta amince da kujeru 70 ga masu ziyarar Ibada zuwa kasar Isra’ila.

Game da shirin kwaskwarimar cibiyar kungiyar ta CAN kuwa, Gwamna Inuwa ya amince da bada Naira miliyan 25 ga kungiyar don yin muhimman gyare-gyare a cibiyar, baya ga Naira miliyan 10 da ya bai wa kungiyar a matsayin goron sabuwar shekara.

Shugaban riko na kungiyar Kiristocin ta Nijeriya CAN reshen Jihar Gombe Rabaran Sunday Congo wanda ya samu wakilcin sakataren rikon kwarya na kungiyar Apostle John Adetiba, ya ce sun ziyarci gwamnan ne don kai masa gaisuwar kirsemeti dana sabuwar shekara.

Sai ya yaba wa gwamnan bisa kawo sauye-sauye kan matsalolin kudin da suka dabaibaye hukumar kula da ziyarar Ibada ta kiristoci, lamarin da ya janyo kiristocin jihar suka rasa zuwa ziyarar Ibada Urshelima a bara.

Malamin addinin ya bayyana daya daga cikin shirye-shiryen gwamnan na alkinta muhalli da ake kira Gombe Goes Green 3G a takaici da cewa muhimmin shiri ne da zai taimaka wajen magance matsalolin sauyi da dumamar yanayi da duniya ke fuskanta.

Tun farko a jawabinsa, shugaban kungiyar ta CAN shiyyar arewa maso gabas Rabaran Abare Kallah, ya ce kiristoci na goyon bayan ayyuka da shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ke aiwatarwa a jihar ta hanyar tafiya da kowa, yana mai kira a gare shi da ya ci gaba da wannan kyakkyawan salon shugabanci.

Sai ya gode wa gwamnan bisa nada kiristoci da dama a muhimman mukaman gwamnatinsa.

A jawabinsa na fatan alkhairi Rabaran J. R. Mangai, ya bayyana gwamnan da cewa jigo ne na zaman lafiya, yana mai addu’ar Allah ya ci gaba da yi masa jagoranci a harkokin tafiyar da mulkin jihar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yaya Za A Iya Maganin Mantuwa?

Next Post

FRSC Ta Gurfanar Da Masu Laifuka 157 Gaban Kuliya A Bauchi

RelatedPosts

NIS Da NAPTIP Sun Sake Shan Damarar Yaki Da Safarar Dan Adam

NIS Da NAPTIP Sun Sake Shan Damarar Yaki Da Safarar Dan Adam

by Yahuzajere
8 hours ago
0

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da...

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

by Sulaiman Ibrahim
14 hours ago
0

Gwamna jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Ya sanar da Mutuwar...

Sakatariyar

Sakatariyar Karamar Hukumar Da Ake Wata Guda Ba A Shige Ta Ba A Kano

by Muhammad
22 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kananan Hukumomi ne ke zaman gimshikai...

Next Post
Hukumar FRSC

FRSC Ta Gurfanar Da Masu Laifuka 157 Gaban Kuliya A Bauchi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version