Kwamared Sunusi Mailafiya" />

Cancanta Al’ummar Jihar Edo Su Ke Bukata, Ba Jam’iyya Ba

alimailafiyasunusi@gmail.com – 08036064695

Yanzu haka tuni zaɓen Jihar Edo ya ɗauki ɗumi, yadda al’umma Kasa kowa ya sanya idanu don ganin wanda zai kai bantensa tsakanin jam’iyyar APC ko PDP. Zaɓe ne wanda yake cike da kalubale tare kuma da bada wani haske ko hasashe akan abinda zai iya faruwa a babban zaɓen kasa na 2023, musamman saboda yanayin mulkin jam’iyyar APC da kowa yake kuka da irin salon mulkin ta, da kuma yadda wasu ke zargin tana amfani da ƙarfin mulki wajen bawa kanta nasara.

Yanzu dai awanni kaɗan ne suka rage a san wanda ya lashe wannan zaɓe, wanda yan takarkarun Gwamna 14 sukai takara, amma kuma hankali ya fi karkata tsakanin jam’iyyar PDP da APC.

Gwamnan jihar Obaseki mai ci na karkashin jam’iyyar PDP yana neman zango na biyu ne, wanda gabanin zaɓen ya fice daga jam’iyyar ta APC sakamakon kiran hakan a matsayin rashin adalci da aka yi masa na hanashi takara, wanda hakan na da nasaba da rikicin sa da Shugaban jam’iyyar ta kasa, kuma tsohon Gwamnan jihar Adams Oshiomole. Rikicin siyasar ya dabaibaye kafafen yaɗa labarai wanda har sai da yayi awon gaba da kujerar Oshiomole ɗin, hakan ta sanya Obaseki tsallakewa zuwa jam’iyyar PDP, kuma suka bashi takara. Yayin da shi kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu ya runtumo jam’iyyar APC daga PDP ya samu takarar Gwamnan daya daɗe yana nema.

Jihar Edo dai na da ƙananun hukumomi har guda 18. Sannan hukumar zaɓe ta INEC tace mutanen da suka yi rijistar zaɓe sun kai miliyan biyu, da dubu ɗari biyu da goma, da ɗari biyar da talatin da hudu (2,210,534), amma kuma mutanen da suka karɓi rijistar su miliyan ɗaya ne da dubu ɗari bakwai da ɗoriya (1.72), sannan kuma akwai guraren kada zaɓe har guda dubu biyu da ɗari shida da ashirin da bakwai (2,627).

A bisa tsari irin na wannan zabe, jam’iyyar APC ta tura wakilan ta ne Karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ita kuma jam’iyyar PDP ta tura Gwamnan jihar Ribers Nyesom Wike.

Duk da cewa hasashe yana nuna cewar jam’iyyar APC itace ke da nasara duba da irin sakamakon zaɓen da yake fitowa, amma kuma hakan ba shine yake nuna lalle itace da nasara ba, har sai an kammala haɗa jimillar ƙuri’u, sannan ne za’a san wanda ya cinye wannan zaɓe me cike da rikici.

Al’ummar jihar Edo dai Adalci da nagarta suke bukata domin bunƙasa jihar, musamman ta ɓangaren ilimi, samar da ayyukan yi, tare kuma da farfaɗo da ɓangaren noman jihar wanda Gwamna Obaseki ya fara. Duk wani yunƙurin waɗannan jam’iyyun na ganin ko ta halin ƙaƙa sai sun ci zaɓe, ya kamata su ajje makaman su a gefe. Ni inada ra’ayin tun wuri ma ya kamata a soke tsarin tura jami’an jam’iyya don ganin ta kowane hali se jam’iyyar su taci nasara, hakan shine kusan ummul-aba’isin janyo tashin-tashina da murɗiya, yayin da kowa yake son nuna ikon sa, Kamata yayi kawai a bar al’ummar jiha su zaɓawa kansu abinda suke ganin yadace. Musamman jam’iyyar APC da ta kowane hali Adams Oshiomole yake son sai ya nunawa duniya cewar shine yake naɗawa, kuma yake cirewa, wato shine yake nuna alkiblar siyasar jihar sa, wanda ko da ace Fasto Osagie bai cancanta ba, to amma shi a gurin Oshiomole ta kowane hali sai ya kayar da Obaseki don ganin ya kawar dashi daga wannan kujera, wannan tsarin siyasar tuni kasashen da suka ci gaba sun dena yinta, wannan tsari ne na siyasar jahiliyya.

Al’umma cancanta suke bukata, ko daga wace jam’iyya ɗan takara ya fito. Wanda zai kasance musu agogo sarkin aiki, tun daga kan ayyukan raya jihar su wacce take da tarihi mai yawa tun tsohuwar Bendel kafin a rusheta a shekarar 1991 inda aka samar da jihar Delta, kuma garin Benin ya taɓa zama shedikwata ta yankin Midwest tun kafin samun ƴancin kai. Jiha ce wacce ta tara manyan ƴan siyasa irinsu Anthony Enahoro, wanda shine mutum na farko daya fara shigar da ƙudurin bawa Nijeriya yanci a shekarar 1953.

Noma yana ɗaya daga cikin fitilar wannan jiha, manyan asibitocin jihar na bukatar ɗaukin gaggawa, haka matasan jihar na bukatar ayyukan yi, akwai babban kuskure idan har son rai, rashin adalci da kuma tasirin Ubangidan siyasa yayi amfani a wannan zaɓen, wannan ba shine lokacin daya kamata wata jam’iyya ta dage dole se ta samu kujerar Gwamna ba. A koda yaushe nafi kallon wanda al’umma zasu amfana daga irin tsarukan sa, da kuma zuciyar son hidimtawa al’umma da yake dashi. Ko da ace Fasto na jam’iyyar APC ne ya cinye zaɓe, hakan zai fi tasiri idan akace al’ummar jihar ne suka zaɓeshi babu wani maguɗin zaɓe, ko kuma kaka-gida da jam’iyyar su tayi. Haka kuma idan Obaseki shine ya koma kan mulki, shima zaifi tasirantuwa idan akace al’ummar jihar ne suka ga cancantar ya koma don cigaba daga inda ya fara, hakan zai kuma nuna mana tasirin tunanin al’ummar jihar, idan kuma saɓanin haka ya faru, to zai zama babban kuskure ace kullum a siyasar Nijeriya, wasu ne daga katanga suke haurowa domin yanke muku hukuncin da ku da kanku ya kamata ku yankewa kanku ba.

Haka kuma ya kamata Gwamnatin APC karkashin Shugaba Buhari ta canza al’amuran zaɓen Kasar nan wajen amfani da jami’an tsaro wajen cin zarafin yan jam’iyyar adawa. Sannan ayi ADALCI wajen sanar da sakamako batare da amfani da hukumar zaɓe wajen bawa jam’iyyar mulki kujera ba.

Exit mobile version