Daga El-Mansu Abubakar, Gombe
Hakimin masarautar Pantami a jihar Gombe, Alhaji Yakubu Abdullahi, ya nada Hajiya Fati Usman Kulani sarautar Jakadiyar Pantami ya na mai cewa cancantarta c eta janyo hakan.
Alhaji Yakubu Abdullahi ya bayyana dalilansa na nada Hajiya Fati Usman Kulani ne a lokacin wani bikin midawa matasa 79 takardar shaidar aiki da Hajiya Fati Usman Kulani ta samar mu su, wacce ita ce ko-odinatar shiyyar Arewa Maso Gabas ta hadaddiyar kungiyar kasashen gwamnatocin Afirka ta United African States.
Ya ce, yadda ta ke tsayawa da kafarta wajen samarwa da matasa ayyukan yi ya sa masarautar Pantami ta ba ta wannan sarauta ta Jakadiya, domin ta na yin jakadanci yadda ya kamata.
Ita dai Hajiya Fati Usman Kulani mace ce mai kamar maza, domin gogaggiyar ’yar jarida ce wacce ta yi aiki a gidan Rediyon jihar Bauchi (BRC) kafin da a ka sami jihar ta dawo Rediyon Gombe (GMC), kuma ta bada gudumawa sosai a shirye-shiryen ta da ta ke gabatarwa kafin ta yi ritaya ta shiga harkar siyasa, wanda yanzu kuma Allah Ya sa ta zama ko-odinata ta kungiyar kasashen Afirka.
A gefe guda da wakilinmu ya ke zantawa da Jakadiyar ta Pantami, don jin yadda ta karbi wannan sarauta da a ka ba ta; sai ta ce, ta ji dadi matuka na yadda ba tare da taje ta roka ba uban kasa Hakimin Pantami ya ga cancanta da dacewarta ya ba ta wannan sarautar.
Jakadiyar kasancewar ta ko-odinatar wannan kungiya ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da amfani da ofishinta don samarwa ’ya’yan talakawa aikin yi.
Ta ce, ba iya wadannan matasa 79 kadai ta samarwa da aiki ba akwai wasu 53 da su ne su ka fara cin gajiyar shirin sannan kuma har yanzu ba za ta zauna ba har sai ta tabbatar da ‘Ya’yan Marasa galihu sun ci gajiyar wannan shiri kafin lokaci ya kure.
Sannan sai tayi amfani da wannan damar inda ta godewa Hakimin na Pantami Alhaji Yakubu Abdullahi, na yadda ya nada ta Jakadiyar Pantami tare da kokarin Jarman Pantami Alhaji Sa’idu Sulaiman Mai kusa na yadda yake taimaka mata da shawarwari irin na Uba.
Daga nan sai tace a shirye take da ta ci gaba da karbar shawarwari na yadda za ta sake taimakawa Matasa dan ganin rayuwar su ta inganta.