Canja Kungiya Ba Za Ta Shafi Kokarina Ba A Wasannin Turai – Ronaldo

Ronaldo Kungiya

Dan wasan tawagar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa zancen canja kungiya da ake has ashen cewa zaiyi bayan kammala gasar cin kofin nahiyar turai ba zata shafi kokarinsa ba a gasar gaba daya.

Ronaldo ya bayyana haka ne a hirarsa da manema labarai kafin wasan da kasarsa ta Portugal ta fafata da kasar Hungary a jiya, inda yace yanzu yayi girman da irin wannan maganar ba zata dauke masa hankali ba.

Tuni  aka fara cece-kucen kungiyar da dan wasa Cristiano Ronaldo zai koma sakamakon wasu maganganu da yayi a kwanakin baya inda yake cewa ya gama cika burinsa a kungiyar ta Jubentus.

Kalaman da Ronaldo yayi na cewa ya cika burinsa a kungiyar shi ne ya sake rura maganar cewa karshen zamansa yazo a kungiyar wadda ya bayyana cewa ta yi masa komai bayan ta taimaka masa ya lashe gasar Siriya A a kasar.

Tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United ake saran Ronaldo zai yiwa kome a kakar wasa mai zuwa ya yinda ake hasashen za’a iya yin musaya da dan wasa Paul Pogba wanda shima saura kwantiragin shekara daya zamansa ya kare a Manchester United.

A watan Mayun da ya gabata a wata hira da ya yi da manema labarai, Cristiano Ronaldo, ya ce burinsa ya cika tun daga lokacin da ya koma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a shekarar 2018 domin buga wasannin gasar Siriya A kamar yadda ya tsara a rayuwarsa.

Dan wasan wanda shi ne kyaftin din tawagar Portugal ya ce ya ji dadi da matsayin da kungiyar ta karkare kakar wasan bana duk da cewa basu lashe gasar Serie A ba, bayan guda tara a jere da suka lashe a baya, kuma yana fatan kungiyar zata gyara kuskuren da tayi a kakar wasa mai zuwa.

Kawo yanzu dai sauran kwantiragin shekara daya ya rage wa Ronaldo, mai shekara 36 a Jubentus, sai dai ana ta rade-radin cewar zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana domin komawa kasar Ingila da buga wasa.

Shima dan wasa Paul Pogba saura shekara daya kwantiraginsa na kungiyar ya kare wanda hakan yasa ake ganin zai iya komawa tsohuwar kungiyarsa ta Jubentus sannan Ronaldo ma ya koma Manchester United.

Ronaldo, mai shekara 36 a duniya ya buga wasa a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid  ya ce yana cike da farin ciki da ya lashe manyan gasa a kungiyoyi  uku da suka hada da Manchester United da Real Madrid da kuma Jubentus daga kasashe uku daya buga wasa.

Dan wasan shi ne  zai ja ragamar tawagar kwallon kafar Portugal gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana da aka fara ranar 11 ga wata kuma a kammala a watan Yulin shekara ta 2021 kuma kasar Portugal din ita ce mai kare kambu bayan ta lashe gasar karshe da aka buga shekaru biyar da suka gabata a kasar Faransa.

Rahotanni daga Portugal sun ruwaito cewa kungiyoyin Manchester United da Paris Saint German ne kadai a halin yanzu suke ci gaba da bibiyar dan wasan wanda ake saran zai bar kungiyar Jubentus bayan kammala wasan kofin turai.

An bayyana cewa Ronaldo ya yanke shawarar barin kungiyar ta Jubentus sakamakon kungiyar ta kasa lashe kofin zakarun turai sannan kuma rashin lashe gasar La liga ya taimaka sosai.

Exit mobile version