Abubuwa sun bi sun damalmale, komai ya rincabe, kayan masarufi ya yi dan karen tsada, tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ya gagara, tattalin arzikin kasa ya durkushe, talakawa suna ta dandana kudarsu; ilimi ya gagari ‘ya’yan talakawa sakamakon rashin kulawar gwamnati, kai da dai abubuwa birjik ga su nan da gwamnati ta kasa tabuka komai a kai. Wanda hakan ya sa wuraren hirarrakin jama’a da majalisun zauniyar mutane da dandamalin sada zumunta dangin Facebook, Twitter da ma WhatsApp suka cike da sakonni iri-iri da suke nuna Allah wadai da tofin Allah tsine. Rubuce-rubuce, hotuna da ma faya-fayen bidiyo da na sauti sai karakaina suke yi dauke da kalaman tsinuwa, fushi da jafai wanda duka hakan na nuni kan cewa turar fa ta kai bango. Kuma kawancen da ke tsakanin talaka da Shugaba Buhari ya zo karshe. An ci Talatar, Larabar ta watse. Domin bayan maganganun bacin rai a wasu wuraren ma har an fara samun zanga-zanga wanda zuwa yanzu ba a san ya abin zai kare ba.
A duk cikin wadannan abubuwa da suke faruwa abin da na fi lura da shi shi ne nadama da takaicin yarda da amincewar da mutane talakawa, musamman na nan yankin Arewa, su ka yi wa shugaban gwamnati mai ci, wato Muhammadu Buhari. Na ga, na kuma ji, faya-fayen bidiyo da na sauti ma su yawa na irin maganganun da yake na alkawarurruka ga jamaa da wasu faye-fayen da suke nuna irin bidiri da mutane suka yi lokacin da aka aiyana cewa shi ne ya lashe zaben shugabancin kasar nan a shekara ta 2015.
Tun bayan shigowar sa fagen siyasa a shekara ta 2002, da kuma takarar shugabancin kasar nan da ya nema har sau uku ba tare da cimma gaci ba, Janar Muhammadu Buhari ya zama wani gwarzo a idanun talakawan Nijeriya musamman ma na yankin Arewa. A duk yan siyasar kasar nan ba wanda suke buri da fatan ya karbi ragamar shugabancin kasar tamkar sa. Su na yi ma sa kallon wanda zai ceto su daga kangin fatara, zalunci da talauci; suna ma sa kallon shi ne zai iya gyara alamuran kasar ta hanyar fatattakar cin hanci da rashawa. Sun rada ma sa taken “Mai Gaskiya” tun bayan da wani mawaki ya kira shi da hakan a cikin wakar da ya yi ma sa mai amshin Yau Nijeriya Riko Sai Mai Gaskiya…
A kan Buhari talakawan kasar nan sun ki ji sun ki gani. Sun zagi kowa sun tsinewa kowa. Sun ce kowa na banza ne shi kadai ne na kwarai. Kowa mugu ne shi kadai ne mai tausayi da imani. Kowa macuci ne shi kadai ne nagartacce. Kowa bai iya ba shi kadai ne ya iya. An halaka rayuka an kuma salwantar da dukiya duk saboda Buhari.
Sai dai kuma tun bayan lashe zaben da ya yi a watan Maris na shekara ta 2015, da kuma darewa kujerar shugabancin da ya yi tun daga ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2015 din, sai abubuwa da ba ai zato ko tsammaninsu ba suka fara bayyana. Ana murna an fatattaki jamiyyar PDP to amma sai aka ga ita ma jamiyyar APC din, wanda Buharin ne komai nata, ba ta sauya zani ba. Komai ya tsaya cik. An ci gaba da shaani kamar yadda ake yi da can. Maimakon a motsa gaba sai aka ga baya ma kawai ake yi domin wasu abubuwan asshsha da ba su faru a bayan ba ma, a karkashin wadanda ake dangantawa duk wani nauin zalunci da rashin gaskiya, sai ga shi sun bayyana sun kuma samu wurin zama a karkashin wadanda akai ta mafarkin shi ne zai kawo sauyi, shi ne zai kawo gyara.
Babu ko shakka wannan raba gari da kuma juyin waina da ya faru tsakanin talakawa da Shugaba Buhari abu ne da ya kyautu ma su nazari da ma su sharhi kan alamuran yau da kullum su yi fashin baki a kan sa. Zai yi kyau in aka yi duba tare da nazari kan wane irin mutum ne Shugaba Buhari? Mene ne dalilin da ya sa talakawa suka kwallafa ran su a kan sa? A wurina ta hanyar yin wadannan tambayoyi ne kadai za mu iya fahimtar hakikanin abin da ya kawo mu halin da muka tsinci kawunan mu a yanzu, ta yadda a yau talakawa ke kuka da Allah wadai da gwarzon na su da kuma kokawa da salon mulkinsa. Da ma ai an ce yau da gobe mai sa ango ya mari amarya.
To shi dai Muhammadu Buhari ya rike mukamin gwamnan soja na jihar Arewa Maso-Gabas a karkashin mulkin soja na Murtala/Obasanjo daga shekara ta 1975 zuwa 1979 kodayake a wannan tsakanin ya bar matsayin gwamna ya koma ministan albarkatun man fetur. Ita waccan jiha ta Arewa Maso-Gabas a wancan lokaci ta kunshi wuraren da a yanzu su ne jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe.
Bayan sojoji sun koma bariki sun mika mulki a hannun farar hula a shekarar 1979, Muhammadu Buhari ya dawo ya hambare wannan zababbiyar gwamnati a karshen shekarar 1983. Ya yi mulkin nuna karfi da kama-karya. An daure kusan duk wadanda suka rike mukami a tsakanin shekarun 1979-1983. An kassara tattalin arzikin jamaa ta hanyar sauya kudi cikin kankanin lokaci ba tare da ba wa jamaa wadataccen lokacin da za su iya kai kudadensu banki a sauya mu su da sabon kudin ba. An kama dukiyoyin mutane.
A wannan lokaci aka fara abin da ake kira Ruwa-Ruwa, wato Special Task Force ma su bin mutane da gudu suna kama su da kayan siyarwan su. An fasa wurin ajiyar kayayyakin yan kasuwa an yi baje-kolin hajojin. Jamian gwamnati sun zama shafaffu da mai domin gwamnatin ta samar da dokar Public Officers (Protection Againts False Accusations) Decree No 4 wanda ya sanyawa yan jarida sasari ta yadda in misali in an yi wani abu ranar Talata ka ce ranar Laraba a ka yi to za a iya gurfanar da kai gaban kotu a daure! An kuma yi yunwa da ake kiranta Yar Buhari ko kuma Buhariyya.
Duk wadannan abubuwa sun faru ne cikin watanni ashirin kacal. A sannan ne yan uwansa sojoji suka ga kazantar ta yi yawa, kwamacalar ta wuce iyaka, suka hambarar da shi daga kan karagar mulkin. Sai dai a tsawon wannan watanni ashirin da ya yi babu wani abu na ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta aiwatar. Alal hakika ma ya warware ko kuma soke ayyuka da yawa da gwamnatin Shugaba Shehu Shagari ta bayar. Daya daga cikin wadannan ayyuka sun hada da sabuwar jamiar Bayero ta Kano wacce sai bayan da Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya hau mulki ne aka dawo da kwangilar.
Tun bayan fitowarsa a shekarar 1989 daga killacewar kusan shekaru hudu da sabuwar gwamnati ta yi masa, ba a kuma jin duriyarsa ba sai da gwmanatin Janar Sani Abacha ta jajibo shi ta nada shi shugaban hukumar kula da asusun rarar man fetur wato PTF, wacce ta zama komai da ruwanka a shaanin ayyukan gwamnati ta yadda ita take aikin kowace maaikata kama daga abin da ya danganci maaikatar lafiya, maaikatar noma, maaikatar ayyuka, maaikatar ilimi da sauransu. Bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999 sai ya yi komawarsa gida ya zauna kafin daga bisani ya tsunduma, ko kuma mu ce aka tsindimo da shi cikin siyasa a shekarar 2002. Duk abin da ya biyo wannan sananne ne a wurin mu. Ba a da bukatar yin maimai a nan.
Daga bayanan da suka gabata mun ga wane ne Muhammadu Buhari a takaice. Wanda hakan shi ne amsar dayan tambayoyi biyu da muka ce ya wajaba a nemo amsarsu. Yanzu kuma sai mu koma kan daya tambayar kan mene ne ya sanya talakawan Nijeriya, musamman na yankin Arewa, suka ki ji su ka ki gani kan wannan bawan Allah?
Safiyar mutum ita ke nuni zuwa ga yammacinsa. Ko kuma ma iya cewa kuruciyar mutum manuni ce ga yadda tsufansa zai kasance. Abin nan dai da Bahaushe ke cewa Jumaar da za tai kyau tun daga Laraba ake gane ta.
Idan muka bibiyi rayuwar Buhari ta shugabanci tun daga lokacin da ya rike mukamin gwamna, minista da me gaba daya shugaban kasa na mulkin soji, abin da zai bayyana gare mu shi ne ba wani mutum ne mai kwarewar shugabanci da iya tafiyar da harkokin jamaa ba. Mu tambayi mutanen Arewa Maso-Gabas wane abu ne za su nuna da Buhari ya samar lokacin da yake can?
Mu kwatanta shi ta wannan fuskar da gwamnan tsohuwar jihar Kano Audu Bako, wanda har zuwa yau ba ma maganar irin aiyukan da ya yi ake yi ba, har yau gwamnatocin da suka biyo bayansa a jihar Kano da ma kanwarta Jigawa dori suke yi kan tsare-tsaren da ya fitar domin ciyar da alumma gaba. Haka ma idan aka kalli ayyukan da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi, wato Marigayi Alhaji Balarabe Musa a cikin watanni goma sha takwas zuwa ashirin.
Haka za mu gani in mun koma kan hukumar albarkatun man fetur ta kasa wato NNPC wadda a lokacin da shi shugaba Buharin yake ministan mai ne ma aka kafa ta. In za mu duba wannan hukumar da yadda ake fama da dawainiyar man fetur a kasar nan sai mu ce ta zama shirim-ba-ci ba. Har yau ba ma iya samar wa da kan mu man fetur din da za mu yi amfani da shi sai dai mu fitar da danye mu siyo tatacce. Babu mamaki irin ga-ludayan da hukumar ke yi har zuwa yau din nan ya samo asali ne daga wanda ya yanke mata cibiya, mutumin da ke rike da matsayin minista lokacin da aka kirkire ta.
Saboda haka a kokarin mu na gano dalilin da ya sa talakawa suka makale wa Buhari, zuwa yanzu mun fahimci cewa zaman sa gwamna da zaman sa minista ba su ne suka janyo masa wannan makauniyar soyayyar daga talakawa ba. Don haka abu na gaba shi ne mu duba mene ne ya yi lokacin da ya shugabanci kasar nan tsawon watanni ashirin a karkashin tsarin mulkin soja. A wuri na a wannan gabar ne za mu samu amsar da muke nema.
Babu ko shakka kowa ya san akwai takun-saka da kuma gani-gani tsakanin ma su wadata da kuma marasa shi. Kusan a kowane yare, a cikin kowace alumma da ma addinai, za ka ga akwai nauin zaman doya da manja tsakanin wadannan bangarorin alumma guda biyu. In muka dauki Bahaushe za mu samu karin maganar ku ci anan mu ma ci a can da makamantan wadannan.
To, kamar yadda na bayyana a baya, lokacin mulkin da ya yi na soja Shugaba Buhari ya tsawwala wa kowa da kowa amma ma su abin kan su su ne suka fi dandana kudarsu. To dama shi talaka da ba komai gare shi ba ai dole azabar da ya sha lokacin ta gaza ta ma su wadata. Don ta kare a yi gobara, tun da ai shi ba shi da komai.
To, ni a iya fahimtata wannan gallazawa da Shugaba Buhari ya yi wa ma su wadata ita ce ta saya masa farin jini a wurin talakawa da samun muhalli a zukatansu. Za ka yarda da ni in ka yi duba da fatan irin abubuwan da talakawan suke so ya yi da zarar ya karbi ragamar shugabanci. Kirarin da suke yi masa shi ne fiya-fiya maganin kwari. Wani daga wadanda suka yi masa waka ya fassara wannan maganar inda ya ke cewa:
Ya Allah ka ba Janaral Buhari,
Manya su ci kwal ubansu!
Saboda haka, ganin da yanzu aka yi wa Buhari da ralakawa a rana sai mu ce kaikayi ne ya koma kan mashekiya, reshe kuma ya juye da mujiya. Talakawa sun gina rami don ma su wadata su afka. Amma daga karshe kuma ramin ya rufta ciki da su talakawan. To ruwa cikin cokali dai ya ishi mai hankali yin wanka. Dole ne jamaa su sauya tunaninsu ta hanyar gamsar da kan su game da abin da suke bukata a shugabanci, kuma wane irin mutum ne zai iya samar da irin wannan shugabancin. Ni dai a halin yanzu ban san me zan ce mana ba mu talakawa. Jaje zan yi mana ko dariya? Amma dai na taba ganin wani ya rubuta cewa: wannan canjin ya zama canjin rigar mahaukata: an cire mai dauda an sanya yagaggiya!