Dan wasan Real Madrid, Dani Carbahal ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Santiago Bernabeu.
Dan wasan ya saka hannu kan kwantiragin shekara biyar a gaban shugaban Real Madrid, Florentino Perez.
Carbahal mai tsaron baya ya fara wasa a karamar kungiyar Madrid a 2010 daga nan ya koma Bayern Leberkursen a 2012 sannan ya koma Real a 2013, ya kuma buga mata wasa 103 ya ci kwallo biyu.
Ga jerin kofunan da ya lashe a Real Madrid
Copa del Rey: 2013-14
Supercopa de España: 2017
UEFA Champions League: 2013-14, 2015-16, 2016-17
UEFA Super Cup: 2014, 2016, 2017
IFA Club World Cup: 2014, 2016