Tsohon mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Iker Casillas ya koma kungiyar da aiki inda aka bayyana cewa zai soma aiki da gidauniyar dake dauke da sunan kungiyar ta Real Madrid.
Tsohon mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid din, Iker Casilas ya taba lashe kofuna 19 da wannan kungiya a matsayin dan wasa ciki har da gasar cin kofin zakarun turai da La liga da sauran kofunan da ya taimakawa kungiyar ta lashe.
Wannan gidauniya na tallata matasa tare da basu horo da ya dace a fanin kwallon kafa kuma Iker Casilas da ya haska da kungiyar kasar Spain sau 167 tare da lashe kofin Duniya da kungiyar Spain a shekara ta 2010 da kofin Turai a shekara ta 2008 da 2012 .
Tsohon dan wasan mai tsaron bayan ya dawo kungiyar ne bayan share shekaru biyar da ficewa daga Real Madrid zuwa kungiyar kwallon kafa ta FC Porto, kungiyar da a rayuwarsa ya taba wakilta banda Real Madrid.
Shima a nasa bangaren, shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya tabbatar da cewa za suyi aiki tare da Casillas kuma zai taimakawa matasan ‘yan wasan kungiyar wajen sun kware wajen buga wasa sannan kuma sun zama manyan ‘yan wasa a kokarin da kungiyar takeyi na tabbatar da ganin ta ci gaba da fitar da matasan ‘yan wasa masu jini a jika.
“Casillas babban dan wasa ne wanda ya kware wajen kare ragarsa kuma yana da gogewa da kwarewa wadda zata taimaka mana tare da matasan ‘yan wasan da zaiyi aiki dasu wajen bunkasa wannan kungiya tamu,” in ji Perez.
Ya ci gaba da cewa “Babban abinda yake gabana a yanzu shine kafin nabar shugabancin wannan kungiya ya kasance na tabbatar da ganin an gina babbar kungiya ta matasan ‘yan wasan da zasu dinga shiga babbar kungiyar mu hakan zai taimaka mana wajen rage kashe kudi a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa kuma zamu samu matasan ‘yan wasa masu kishi da kaunar wannan kungiya.”