Connect with us

KASUWANCI

CBN Ta Samar Da Sabon Tsarin Bunkasa Masa’anatu Da Aikin Gona

Published

on

Babban bankin kasa (CBN) zai kaddamar da wani sabon tsari wanda ake kira special cash reserbes rekuirement (CRR), wanda kuma zai taimakawa, ajiye kudade a Bankuna, saboda su samu damar bada bashin da zai dauki dogon lokaci , kafina kai ga biya. Ga bangarorin masu masana’antu da kuma banagren aikin gona domin a bunkasa tattalin arziki.
Gwamnan Babban banki na kasa Godwin Emefiele shi ya bayyana hakan ga manema labaru, jimkadan bayan da aka kamamala taron kwamitin tsare tsaren kudade, wanda aka yi a Abuja ranar Talata.
A karkashin sabon tsarin kamar dai yadda ya bayyana za a iy bada bashi akan matsayin kashi 9, da kuma shekaru tara wadanda za ayi kafin a fara biyan shi bashin, da kuma shekaru biyu na daga kafa kafin a biya shi bashin, saboda samu bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
‘’Yayin da yake da akwi wahala wajen al’amarin samar da ayyukan yi, saboda ana samun matsalar abubuwan more rayuwa,, shi kwamitin ya ga cewar abin so ne shi Bankin ya ci gaba da abada dama ta, ajiye kudade a Bankuna, saboda ta wannan hanyar sai a kara samar da hanyar da kudade zasu rika shigowa, saboda hakan zai taimaka wajen samar da karuwar hanayar taimako na bashi, saboda asamu bunkasa tattalin arziki, saboda farfado da shi tattalin arzikin kasa’’ kamar dai yadda ya bayyana’’.
Su DMB su zasu samar da taimako wajen matsalar harkokin kasuwanci suke samu, musamman ma manyan kamfanoni, saboda idan aka yi haka, zai ja hankalin, masu son zuba hannunn jari, a karkashin shi wannan tsarin babban bankin zai bayar da wani karin taimako.
Ya bayyana cikakkun al’amuran da za a sa ido akansu, wanda shi Babban bankin yasa ayi a sashen ziyararr bankuna saboda a san irin halin da suke ciki, sashen tsare tsaren manufofin kudade, da kuma bincike, na shi Babban bankin saboda, duk wadansu matsalolin da suka iya kao tarnaki ga, harkar kasuwanci an yi maganin su, ba ma kamar manyan kamfanoni da ake sa ran zasu samar da ayyukan yi masu yawa.
Yayain da kuma ake ta tsammanin rashin tabbasa kasa, saboda yadda ake ciki danagane da matsalar hauhawar farashin kayayyaki, da kuma yadda darajar Naira take , shi yasa kwamitin ya yanke shawarar, abar yadda tsare tsaren kudade suke, da kuma wasu hanyoyin da ake bi saboda a samu kare hanyoyin da suke bunkasa al’amarin tattalin arzki.
Baya ga ci gaba da amafani da shi wato MPR wanda wata hanya ce wadda aka kokarin, hana yadda ake ba Bankunan kasuwanci bashi, akan kashi 14, da kuma cash reserbe ratio, wato yadda ake kula mizani yadda ake ajiye kudade, wanda shi ne mafi kankantar, kason da za a iya karba, a Bankin kasuwanci, zuwa wani lokaci abin ya tsaya ne akan kashi 22.5.
Sai kuma maganar likuidity ratio wato ainihin gundarin ruan bashn , an bar shi kashi 30, sai kuma +200 da kuma -500 akan yadda abin yake dangane da MPR.
Wannan kuma dai shi ne taro na goma sha daya, wanda aka bar al’amrin MPR ba tare da wani canji ba tiun shekarar 2016.
Ita kuma Hukumar kulawa da harkar kididdiga ta kasa (NBS ) ranar Litinin ce bayyana labari da dumin dumi danagen, da mizanin da ake duba tabarbarewar tattalin arziki, wanda tace abin ya tsaya akan kashi 11.23 tun cikin watan Yuni na wannan shekara, wanda an samu ci gaba, saboda abin ya sauko kasa da kashi 11.61, a watannin da suka wuce. Raguwar ko kuma faduwar ta kasance karo na goma sha bakwai wanda aka samu koma baya na wahalar da ake sha saboda matsalar da aka shiga, tun watan Janairu na 2017.
Ranar Talata ce shi gamnanj Babban banki na kasa ya bayyana cewar, shi al’amarin kawo ma tattalin arziki na kasa dauki, abin ya samar da ci gaba, ajen yadda darajar Naira take da dalar Amurka, data kasance Naira 360 watanni masu yawa.
Amma kuma duk da hakan akwai wurin da kasa take ajiyar kudinta na kasashen waje, saboda abin an samu ja da baya, daga dalar Amurka bilyan 47. 79 a watan Mayu zuwa dala bilyan 47. 2, tun dai daga 23b ga watan Yuni na wannan shekarar.
Y akuma bayyana dalilan da suka sa aka samu matsalar danagane da kudade waje da ake ajiya, duk kua d ayake an samu karuwar tashin farashin man fetur, a kasuwar mai ta duniya, da kuma wata matsalar da aka samu saboda ci gaba da kasuwanci da kasar Amurka.
Kamar dai yadda gamnan Babban bankin kasa a dalilin daukar wani mataki na, kara bunkasar shi tattalin arzikin su, sai maganar interest rate wato kudin ruwa na ksar Amurka, da kuma sauran wasu kasashen da suka ci gaba, abin sai ya kara sama.
‘’Kudaden da aka sa su wasu kasuwanni da zummar a ganin sun taimaka wajen samar da sauki, amma maimakon haka sai abubuwa suka kara yin sama, wahala ta karu, ta bangaren tattalin arzikinsu. Don haka an shiga babbar matsala saboda kuwa, maimakon kudade su shigo , sai ma fita suke kara yi, wannan kuma abin ya shafi Nijeriya.
Sai dai kuma shi gwamnan na Babban banki ya kara jaddada cewar Nijeriya ta ci gaba fiye dac sauranasu kasashe, idan ana maganar harkar kasuanci, saboda tafi kasashe kamarc su Afirka ta Kudu, Guine, Turkey,Indonesia, wadanda suka fuskanci kramara matsala, danganne yadda kudaden kasarsu suka ja da baya wato darajarsu.
Al’amarin daya shafi darajar kudin kasa dana Amurka, akawai ci gaba , saboda kuwa, munsamu damar kare ita darajar Nairar, Wannan ma shi yasa har yanzu abinn ya tsaya akan Naira 360, akan dala daya ta Amurka har watanni masu yawa.’’
MPC ta nuna rashin jin dadinta saboda rashin nuna kmar yi da gaske na asu lokuta ba Nijeriya take yi, wajen samar da wani tsarin tatttalin arziki wanda zai kai ta tudun mun tsira.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: