Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

CBN Ya Bukaci Bankuna Su Rungumi Shirin Bada Rancen Noma

by
1 year ago
in NOMA
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kira ga Cibiyoyin samar da kudade dake a jihar Edo da su rungumi shirin bayar da rance kudin aikin noma na (ACGSF), musamman domin rage matsalar karancin abinci a daukacin fadin kasar nan.

Mista Jumbo Dabis, Kontirolan shiyya na Babban Bankin Nijeriya CBN a jihar ta Edo dake a garin Benin ne ya yi wannan kiran a yayin gabatar da lambar yabo ta manomi ta shekarar 2020 ga bankin samar da kudin noma na LAPO Microfinance da kuma ga bankin Prosperity Microfinance.

Kontirolan shiyya na Babban Bankin Nijeriya Mista Jumbo Dabis ya ci gaba da cewa, shirin zai taimaka matuka wajen kara samar wa da gwamnatin tarayya da kuadaden shiga masu dimbin yawa.

Labarai Masu Nasaba

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

Noman Rogo: Yadda Nijeriya Ke Asarar Naira Tiriliyan 27 A Kasuwar Duniya

Bugu da kari, wadanda suka karbi lambar ta yabon su ne, shugabnin bankunan Mista Osagie Imohimi da Obamwonyi Franklyn.

A cewar Kontirolan shiyya na Babban Bankin Nijeriya Mista Mista Jumbo Dabis, shirin an kafa shi ne a shekarar 1977, inda shiyar shirin ta farko ta kai naira miliyan 100 ta kuma karu zuwa naira biliyan 30, hart a kara karuwa zuwa naira biliyan 50.

Kontirolan shiyya na Babban Bankin Nijeriya Mista ya sanar da cewa gwmnatin tarayya da kuma Babban Bankin Nijeriya CBN, na da kashi 60.4 a cikin dari na shiyar kudin.

Kontirolan shiyya na Babban Bankin Nijeriya Mista Jumbo Dabis ya yaba wa wadanda suka samu lambar karmarwar bisa kokarin da suke kan yin a kara bunkasa fannin aikin noma a kasar nan, inda ya kara da cewa, bankin ba zai yi kasa a gwiwa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar ba.

Shi ma a na sa jawabin a gurin taron shugbana bankin LAPO Microfinance Bank Oluremi Akande ya bayyana cewa, daga watan Janairun shekarar shekarar 2020 zuwa watan Disambar shekarar 2012, bankin ya rabar da sama da naira biliyan 27 ga manoma sama da 34,000 a jihohi 34 dake a fadin kasar nan harda babban birin tarayar Abuja.

Shugbana bankin LAPO Microfinance Bank Oluremi Akande ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyu cur, bankin na LAPO MfB ya zamo Zakara a jihar Edo da kuma a cikin kasar nan.

A cewar shugbana bankin LAPO Microfinance Oluremi Akande ya bayyana cewa, Cibiyar bayar da rance kudaden, na kan wani shirin rabar da sama da naira biliyan 10 a cikin wannan shekarar ta 2021 domin talla fa manoma sama da 100,000.

Da yake yin tsokaci kan shirin na bankin, shugbana bankin LAPO Microfinance Bank Oluremi Akande ya bayyana ya bayar da tabbacin cewa, bakin zai ci gaba da inganta rayuwar alumma, tattali arzikn kasar nan, tallafa wa manoman kasar da kuma masu yin matsakaitan sana’oi.

Shi ma a na sa bangaren, shugaban sashen bayar da bashin kudaden na bankin na Prosperity Microfinance Mista Harrison Ewemade ya jinjia wa babban bankin Nijeriya CBN kan shirin, inda ya kara da cewa, bankin na su ya rabar da sama da naira miliyan 50 ga sama da manoma guda 200 daga shekarar 2018 zuwa 2020.

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

CBN Ya Saki Naira Biliyan 33.4 Ga Kamfanin DisCos Don Aikin Lantarki

Next Post

Shafin Farko: Leadership A Yau Talata 30 Ga Maris 2021

Labarai Masu Nasaba

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

by Abubakar Abba
1 week ago
0

...

Rogo

Noman Rogo: Yadda Nijeriya Ke Asarar Naira Tiriliyan 27 A Kasuwar Duniya

by Abubakar Abba
2 weeks ago
0

...

Gurjiya

Sirrin Noman Gurjiya Wajen Bunkasa Tattalin Arziki

by Abubakar Abba
3 weeks ago
0

...

Bunsuru

Kiwon Bunsuru A Saukake

by Abubakar Abba
1 month ago
0

...

Next Post
Shafin Farko: Leadership A Yau Talata 30 Ga Maris 2021

Shafin Farko: Leadership A Yau Talata 30 Ga Maris 2021

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: