Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

CBN Ya Fitar Da Tsarin Gudanar Da Hada-hadar Kudade Ta Yanar Gizo

by Yusuf Shuaibu
January 18, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Manoman Auduga
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sabon tsari wajen gudanar da hada-hadar kudade ta yanar gizo da kuma wasu wadanda suke da alaka da kimiyyar kudade. Babban Bankin ya bullo da wadannan tsarin ne domin magance matsalolin da ake samu wajen biyan kudi a cikin kasar nan.

“Tsarin zai taimaka wajen dai-daita harkokin kudade a Nijeriya da kara amfani da yanar gizo wajen hada-haadar kudade, inda a yanzu CBN ya samar da wani lambobin sirri wanda za a dunga amfani da shi wajen gudana da hada-hadar kudade a yanar gizo, domin gabatar da dangantaka a tsakanin abokanan huddar bankuna da ke cikin kasar nan.

“Tsarin ya kayyade yawan kudaden da za a gudanar da hada-hadar a yanar gizo, sannan ya samar da tsarin tabbatar da kulawa da hada-hadar kudade ta yanar gizo domin dakile ayyukan masu damfara a ta yanar gizo da kuma safarar kudade ba bisa ka’ida ba.

“Za a dunga samun rahoton hada-hadar kudade ta yanar gizo a sashin kula da tsarin biyan kudade da ke cikin babban bankin Nijeriya. Za a dunga kulawa da lamarin ne domin magance matsalolin damfarar kudade ta yanar gizo a cikin kasar nan.”

“Kalmomin sirrin na  biyan kudaden za su kasance ne bisa wasu kebabbun tsarin biyan kudade. Haka kuma bankin ya aiwatar da samar da wasu kalmomin sirri dai-daita tsaro cikin hada-hadar biyan kudade ta yanar gizo. Wannan zai gudana ne a tsakanin CBN da kuma kamfanoni,” in ji shi.

An dai shirya lambobin sirrin a na’urori ga masu amfani da hada-hada ta yanar gizo. Wannan lamari na samar da lambobin sirrin zai samar da ci gaba wajen biyan kudade a yanar gizo. A bangare daya kuma, zai rage tsohon hanyar da kamfanoni suke gwada kayayyakin da suka samar da ayyuka da kuma yadda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu. Za a saka ido wajen kulawa da hanyoyin samarwa a tsakanin kamfanoni.

CBN ya bayyana cewa, yana kira ga ‘yan Nijeriya da su yi kokarin bin wannan tsari saau da kafa domin ci gaba da gudanar da gasa a tsakanin ‘yan kasuwa da yin amfani da na’urori na zamani wajen gudanar da hada-hadar kudade, domin hakan zai taimaka wajen bunkasa basirar abokanan kasuwanci a tsarin da suka dace. Ya ci gaba da bayyana cewa, makasudin samar da wannan sabon tsarin dai shi ne, kara gudanar da harkokin kasuwanci ta hanayar kimiyya da fasaha da kara inganta ayyukan hada-hadar kudade da saukaka harkokin kudade a Nijeriya da kuma rage matsalar satar kudade ta yanar gizo. Ya ce, bin wannan tsarin sau da kafa zai taimaka wajen inganta cibiyoyin kudade a Nijeriya da cike tazarar da ke tsakanin wadanda suka dade cikin lamarin da kuma masu tasowa a yanzu tare da samun alfanu mai yawan gaske. Ya ce, zai taimaka wajen samun ayyuka masu inganci ga abokan cinikayya wanda hakan zai rage hatsarin da suka dade suna fuskanta a baya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tabbas Za A Cefanar Da Kadarorin Gwamnati Domin Samun Kudin Kasafin 2021 – Gwamnatin Tarayya

Next Post

Kamfanin Total Na Tsammanin Samun Harajin Biliyan N115.97

RelatedPosts

Anchor

Manoma Miliyan 3.8 Suka Amfana Daga Shirin ‘Anchor Borrrowers’ – CBN

by Yusuf Shuaibu
14 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana...

Emefiele

Bunkasa Tattalin Arziki: Nijeriya Na Bukatar Kara Kaimi Wajen Adana Abinci – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
5 days ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN),...

Bankuna

Rahoton Bangaren Bankuna Yana Nuna Samun Cigaba Mai Matukar Ma’ana – CBN

by Yusuf Shuaibu
5 days ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Rahoton karshe na Babban bankin...

Next Post
Kamfanin Total

Kamfanin Total Na Tsammanin Samun Harajin Biliyan N115.97

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version