Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
Babban bankin Nijeriya (CBN) ya gabatar da tsarin sabbin caji ga kwastomomi masu amfani da lambar USSD a wayoyinsu wajen aiwatar da hada-hadar kudi na banki.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, kuma dauke da sa hannun mukaddashin daraktan bankin na bangaren sadarwar, Osita Nwanisobi, da daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Nijeriya, Ikechukwu Adinde.
A cewar sanarwar, kwastomomi za su rinka biyan Naira 6.98 a kan kowace ciniki a duk lokacin da suka yi amfani da lambar USSD.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna farin cikin sanar da cewa bayan cikakken tattaunawa kan muhimman batutuwan, an amince da tsarin kuduri wanda zai yarda da dukkan bangarori.”
“Daga 16 ga Maris, 2021, lambar USSD na hada-hadar kudi da aka gudanar a DMBs (Deposit Money Banks) da dukkan cibiyoyin da ke da lasisi na CBN za a caje su kan kudi N6.98 a kowace ciniki. Wannan ya maye gurbin tsarin biyan kudi na kowane zama na yanzu, yana tabbatar da tsada mai yawa mai sauki ga kwastomomi don bunkasa hada hada-hadar kudi. Wannan tsarin kuma na nuna gaskiya, kuma zai tabbatar da adadin ya zama iri daya, ba tare da la’akari da yawan zaman da aka yi ba,” inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Don inganta nuna gaskiya a cikin Gwamnatinta, za a tattara sabbin cajin na USSD a madadin MNOs (Masu ba da hanyar sadarwar waya), kai tsaye daga asusun banki na abokan ciniki. Bankuna ba za su sanya karin caji a kan kwastomomi a gare mu na hanyar USSD ba.”
A makon da ya gabata ne Gwamnatin Nijeriya ta bukaci kamfanonin sadarwa da su dakatar da shirinsu na dakatar da ayyukan USSD a kan bashin Naira biliyan 42 da bankuna ke bin su.