CBN Ya Gargadi Cibiyoyin Kudade Kan Kasuwancin Kudade Ta Intanet

Kudade

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gargadi bankunonin na ‘yan kasuwa da sauran cibiyoyin kudade a kan gudanar da kasuwancin kudade ta intanet wanda aka haramta a kwanan nan. CBN ya bayyana hakan ne ta shafinsa ta hannun daraktan da ke kulawa da bankuna, Mista Bello Hassan da daraktan tsarin biyan kudade, Mista Musa Jimoh.

Wannan gargadi ya shafi bankunan da ke fitar da kudade da cibiyoyin kudade wadanda ba bankuna ba da sauran cibiyoyi da ke da kalaka da harkokin kudade duk wannan gargadi ya shafe su.

“Tun da farko dai, Babban Bankin Nijeriya ya dakatar da hada-hadar kasuwancin kudade a intanet ko biyan kudade a wannan hanya.

“A cewarsa, ya bayar da umurnin hana wannan kasuwancin hada-hadar kudade domin toshe hanyoyin da kudaden kasar nan ne sulalewa, inda ya bayar da umurnin nan take a kulle duk wani asusu irin wannan.

“Wannan mataki ya fara aiki ne tun lokacin da aka bayayyana shi, wanda za a saka ido tare da daukan mataki ga wadanda suka yi kunnen kashe da wannan umurni,” inji CBN.

 

Exit mobile version