Daga Rabiu Ali Indabawa,
CBN a cikin wata takarda mai dauke da BSD / DIR / GEN / LAB / 14/001 da aka fitar a ranar Juma’a, ya umarci duk cibiyoyin hada-hadar kudi “da su tantance mutane da / ko cibiyoyin da ke mu’amala da tsarin Crypto, ko kuma gudanar da musayar kudi a cikin tsarin su kuma tabbatar da cewa an rufe irin wadannan asusun nan take. ”.
Yayi gargadi kan duk wani kamfanin hada-hadar kudi da ya karya wannan umarnin na (CBN) “zai ja fuskanci takunkumi mai tsauri”. A cewar CBN, ” An haramta ma’amala a cikin tsarin ko saukaka biyan kudi don musayar cryptocurrency”. Sanarwar mai dauke da sahannun Bello Hassan, Daraktan Kula da Banki da Musa I Jimoh Darakta, Sashen kula da tsarin biyan kudiin da suka ce umarnin ya fara aiki ne nan take.
Sun kuma ce bankin kolin a baya ya yi gargadi ga Bankin Kudina(DMBs), Cibiyoyin Kudina Bankin (NBFIs), Sauran Cibiyoyin Kudi (OFls) da mambobin ma sha ya game da hadarin da ketattare da ma’amaloli a cikin kudin Crypto, kamar yadda yayi nuni ”. Ko ma dai yaya, bankin koli tare da masu tasiri a shafukan sada zumunta kamar Japheth Omojuwa, ya yanke hukuncin bisa ga shawara yana mai cewa “wannan tsari idan ya tafi a haka, zai kasha kamfanonin Nijeriya a Zahiri kuma ta cutar da masu saka hannun jari na kasashen waje”.
Omojuwa ya bayar da hujjar cewa “masu saka jari galibi daga Amurka suna da, duk da irin kasadar da ke tattare da saka hannun jari a kasarmu, sun saka hannun jari a kamfanonin fintech na Nijeriya da wannan wasikar ta yi niyya karara”.
“Wannan ba lamari ne na rasa wasu kudi ba, wannan lamari ne na yadda kamfanoni za su rufe shago. Kamfanoni masu aiki akan saka hannun jari daga kasashen waje. Wannan kafin ka magance tasiri a kan ‘yan Nijeriya na yau da kullum suna halatta kasuwanci da neman biyan bukatun rayuwa a cikin yanayi mai wahala da tattalin arziki “.
Da wannan shawarar ta CBN, Omojuwa ya koka da cewa “CBN na son kashe ‘yan kasuwanci”.
Da yake maida martini ga umarnin na CBN, Farfesa Uche Uwaleke, na Jami’ar Jihar Nasarawa yace shawarar ba za ta rasa nasa ba da gaskiyar cewa “CBN da Hukumar Tsaro da Kasuwanci (SEC) basu riga sun shirya tare da dokokin da ke jagorantar ayyukan cibiyoyin kasuwancin kadarar Nijeriya ba. ”Ya bukaci jama’a da su ga wannan umarnin da CBN ta bayar ga bankuna “dangane da hadarin da cinikin kudin da bashi da tsari zai iya haifarwa tsarin kudi.”