Za mu cigaba da goyon bayan manoman dake noman shinkafa a kasar ta hanyar ba su bashi a karkaahin shirin aikin noma na Anchor Borrowers.
Furucin ya fito ne daga bakin Gwamnan Babban Banki Nijerya CBN Godwin Emefiele a hirarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taro da masu ruwa da tsaki a fannin noma a babban birinin tarayyar Abuja.
Mista Emefiele ya ce, “Za mu cigaba da goya ba su goyon baya ta hanyar ba su bashi a karkaahin shirin aikin noma na ‘Anchor Borrowers’, domin su ma su na bayar da babbar gudunmawa wajen samar da abinci da kuma kara habaka tattalin arzikin kasar nan.”
Gwamnan ya cigaba da cewa, gwamnati za ta goyi bayan masu noman shinkafa don kau da haramtacciyar hanyar shiga da kaya cikin kasar da kuma bunkasa sashin samar da isasshen abinci.
Gwamnan CBN na ya yi kira ga al’umma da su goyi bayan rufe iyakar da gwamnatin ta yi, inda ya ke cewa gwamnatin ta dauki matakin ne don amfanin su Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Ya bukaci manoman shinkafa a fadin kasar da kada su kara farashin shinkafa saboda garkame iyakar iyakokin Nijeriya da gwamnati ta sanaya aka yi. Ya bukaci yayan kungiyar manoman shinkafa na kasa RIMAN da sauran masu ruwa da tsaki a sana’ar da kada su boye shinkafa.
Gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakar kasar ta a watan Agusta, inda take bayanin cewa a hakan ne za ta binciki shigo da kayayyaki ta haramtacciyar hanya.
Yayin da ya ke bayyana ra’ayinsa kan lamarin, Emefiele yace gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ne don bunkata tattalin arziki da kuma tabbatar da cewa kasar ta cimma isasshen abinci musamman a fannin noman shinkafa.