Abubakar Abba" />

CBN Zai Tallafa Wa Manoman Auduga Da Naira Miliyan 1.6

Manoman Auduga

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, zai tallafawa manoma miliyan 1.6 a cikin daminar shekarar 2020 a fadin kasar don taimakawa wajen bunkasa noman kayan gona.

Bankin ya kuma ce zai tallafawa manoma a karkashin shirin shiga tsakani na kayan masarufi.

Daraktan sashen kudi da ci na CBN Mista Yila Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da ake raba kayan noman rani ga manoman auduga don noman shekarar 2020 a Kwali, Abuja.

Yusuf wanda ya samu wakilcin Mista Ayoola Kuadri ya ce, matakin shine don samar da wani tasiri da zai tabbatar da wadatar abinci a kasar.

Yusuf ya ce bankin na CBN ya dauki nauyin manoma 256,000 a harkar noman auduga domin noman shekarar 2020 ta hanyar shirin aikin noma na Anchor Borrowers.

A na sa ran manoman za su biya bashin da bankin na CBN ya bayar a karkashin shirin bankin na Anchor Borrowers.

Ya bayyana cewa bankin, ya rage kudin ruwa da aka biya akan rancen daga kashi tara zuwa kashi biyar saboda kamuwa da cutar korona.

Ya ce, CBN na aiki tukuru don farfado da masana’antun da domin samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya bayyana cewa, ta re da jajircewar bankin a shekarar 2018 kan noman auduga, masana’antun masaku a shekarar 2019 saboda da ake amfani da su a lokacin ana samunsu a cikin kasar har ma sun bar wasu a rumbunan ajiya.

A wata sabuwa kuwa, Ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta tarayya ta nuna bukatar kashe sama da naira biliyan 9 don bunkasa fannin noma akan kuma amfanin gona iri-iri.

Sai dai, kalubalen kamar yadda wasu ma su fashin baki a fannin su ke gani, duk da kasafin da aka warewa fannin, kwalliya bata biyan kudin Sabulu.

Amma a na samun nasara ne kawai daga tallafin da ake samu daga gun kungiyoyin aikin noma na kasa da kasa.

Bugu da kari, akan samar da hanyoyi a karkara da samar da ingantaccen ruwan sha, ma’aikatar tana son kashe naira biliyan 7.64.

Sun kuma lura cewa, mafi yawancin hanyoyin dake a karkara, ayyukansu sun fada ne a cikin ayyukan mazabun da yan siyasar da aka zaba suka fito hatta manyan fitilun kan hanya.

Dangane da abinci da dabarun adana abinci wanda aka dinga sukar gwamnati kan barin samar da kyakyawan tsarin adana abincin da zai rage radadin karancin abincin da ake dashi a kasar nan, an kebe naira biliyan 2.01 din samar da rumbunan zamani na adana hatsi, sai dai, rumbunan an bayar da aikin yin su ta hanyar jingina a karkashin yarjejeniyar tsarin PPP.

Har ila yau, a fannin kiwo kuwa, gwamnatin zata kashe naira biliyan 1.6 don kebe wuraren yin kiwo na zamani.

Misali, a kwannan baya an ruwaito Kungiyar wadata abinci ta Duduniya FAO, ta nuna taikaicin ta kan yaduwar cutar dabbobi, inda ta lashi takon yin hadaka da Hukumar daile yaduwar Cututtuka ta kasa don magance yaduwar wasu kwayoyin cuta ma su hana magunguna yin tasiri a jikin dabbobi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wakilin ta a Nijeriya, Sufyan Koroma, inda ya kara da cewa, kwayoyin cututtuka ba a dabbobi ne kadai suka zama makarai na maganin warkar da cututtuka ba ce har ma a cikin kayan gona.

Exit mobile version