Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

CGTN Ya Bullo Da Wani Sabon Shiri Dangane Da Yadda Ake Kokarin Dakile Ta’addanci A Jihar Xinjiang

Published

on

Kafar talabijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN dake karkashin babban gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG, ya bullo da wani sabon shirin TV mai suna “Tianshan: Still Standing – Memories of Fighting Terrorism in Xinjiang 2020”, wato tunawa da yadda ake kokarin yakar ta’addanci a Xinjiang. Kwanan nan, Amurka ta sa hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2020. Kuma a daidai wannan lokacin, kasar Sin ta bullo da wannan shirin TV dake kunshe da kwararan shaidu masu tarin yawa, domin nunawa duniya miyagun laifuffukan da ‘yan ta’adda suka aikata a Xinjiang, da wajibci gami da manyan nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta samu a fannonin da suka shafi yaki da ta’addanci da kawar da masu tsattsauran ra’ayi, al’amarin da ya tona asirin ‘yan siyasar Amurka wadanda ke yunkurin yin karya kan abun dake wakana a Xinjiang.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, daga shekara ta 1990 zuwa karshen shekara ta 2016, an samu barkewar al’amuran ta’addanci fiye da sau dubu 1 a jihar Xinjiang, abun da ya haddasa mummunar hasarar rayuka da dukiyoyi. Amma duk da haka, akwai wasu ‘yan siyasa gami da kafafen yada labaran kasar Amurka, wadanda suka jirkita gaskiya da boye ainihin abubuwan da suka faru, abun da ya sa kasa da kasa ba su san gaskiyar abubuwan dake faruwa ba. Abun takaici shi ne, wadannan ‘yan siyasar ba su koyi darasi daga hare-haren ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumba ba, har ma suke goyon-baya da tallafawa ‘yan ta’addan da suka sha aikata kisan kiyashi a jihar. Zartas da shirin doka da ya jibanci Xinjiang, da bata sunan kasar Sin, da kuma kalubalantar manufofin gwamnatin kasar kan Xinjiang da Amurka ta yi, ya shaida cewa, Amurka tana marawa ‘yan ta’addan baya, wannan ya nuna cewa, jirgi daya ne ya kwaso su!
Kafar talabijin ta CGTN ta taba bullo da wasu shirye-shirye biyu a karshen bara, wadanda suka shafi yadda ake dakile ayyukan ta’addanci a jihar Xinjiang, inda masu amfani da yanar gizo ta intanet suka maida martani cewa, shin irin wadannan munanan ayyukan ta’addanci su ma hakkokin dan Adam ne da Amurka take karewa? Gaskiyar abun da ya wakana a Xinjiang ita ce, ‘yan ta’adda sun kashe fararen hula da dama! Amma wasu kafafen yada labaran kasashen yamma sun yi shiru, har ma akwai wasu shafukan sada zumunta wadanda suka cire wadannan shirye-shiryen biyu bisa hujjoji daban-daban. Yanzu CGTN ya bullo da sabon shiri, ko me za su yi a wannan karon? Ko za su ci gaba da yin shiru ne? Duniya ta zura musu ido! (Mai Fassara: Murtala Zhang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: