Bayanai daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa ƙasar Chadi ta fara janye daruruwan dakarunta da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a yankin Diffa na ƙasar Nijar.
Masu sa-ido na kallon matakin a matsayin wanda ke da nasaba da sanya sunan ƙasar Chadi a cikin ƙasashen da aka hana ba su katin shaidar zuwa Amurka, lura da cewa tun daga lokacin da Amurka ta sanar da haka ne Chadi ta bayyana cewa matakin zai iya shafar ayyukan samar da tsaro da ta ke yi.
Janye dakarun zai yi matuƙar illa ga zaman lafiyar yankin, kamar dai yadda Ɗan Majalisarsu Lamido Moumouni Harouna ya ce sun fara kokawa.