Chadi Ta Karbi Gudunmawar Riga-kafin COVID-19 Daga Kasar Sin

Daga CRI Hausa

Gwamnatin Chadi ta karbi gudunmawar riga-kafin cutar COVID-19 daga kamfanin Sinopharm na kasar Sin.

Li Jinjin, jakadan kasar Sin a Chadi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi amana riga-kafin zai yi matukar amfanawa al’ummar duniya. Duk da bukatar da ake da shi na riga-kafin a cikin gida, amma kasar Sin tana burin cika alkawarinta na tallafawa sama da kasashe masu tasowa 80 wadanda suke tsanain bukatar riga-kafin. Ya bayyana hakan ne a filin jirgin saman kasa da kasa na N’DJAMENA a lokacin da riga-kafin ya isa kasar.

Ya kara da cewa, wasu sun ce, “wai kasar Sin tana amfani da riga-kafi a matsayin hanyar diflomasiyya. Amsa ta mai sauki ce: Kasar Sin ba ta son yin baba-kere a fannin diflomasiyya, muna gayyatar saura su ma su yi irin yadda muke yi. Sin da Chadi suna yin kokari tare wajen fama da cutar annobar.”
Ministan kiwon lafiyar kasar Chadi, Abdoulaye Saber Fadoul, wanda ya samu halartar filin jirgin saman lokacin karbar riga-kafin, ya yabawa kasar Sin bisa goyon bayan da take nunawa kasarsa, ta hanyar wannan gudunmawar riga-kafin, da kuma sauran kayayyakin kiwon lafiyar da ta samarwa kasar Chadi tun a farkon barkewar annobar. (Ahmad)

Exit mobile version