Wani sashi na yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, da masu gudun hijira ke zama
Ƙasar Chadi ta fara janye daruruwan dakarun ta da ke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Diffa, dakarun da zasu kula da tsare kan iyakokin ƙasar da Libya da Nijar.
Gwamnatin Chadi ta umurci sojojinta da suka baro yankin Diffa kula da kan iyakokin ƙasar da Libya da Nijar a matakin shirin nan na rundunar G5.
Ministan tsaron Chadi Bichara Issa a wata zantawa da manema labarai ya bayyana cewa Chadi ba ta janye dakarun ta ba daga Nijar, matakin shine na karfafa tsaro a kan iyakokin ta da sauren ƙasashe, a karshe ministan ya bayyana cewa hadin guiwar rundunar ƙasashen za ta maye gurbin rundunar Chadi da ta fice daga yankin Diffa a Nijar.