Champions League: A Istanbul Za A Buga Wasan Karshe  Na Shekarar 2022

Champions League

Hukumar kula da gasar cin kwallon kafa ta nahiyar turai ta bayyana filin wasan da zai karbi bakuncin wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai wato Champions League a shekara ta 2023.

Babban kwamitin hukumar kwallon kafar Turai ne ya amince da filin Ataturk Olympic a Instambul ya karbi bakuncin wasan karshe na gasar Zakarun Turai a 2023 bayan nazari a kan filin wasan tun a shekarar data gabata.

Wannan filin da ke Turkiya ne ya kamata ya karbi fafatawar karshe tsakanin kungiyoyin Chelsea da Manchester City, amma aka dage karawar zuwa birnin Porto na kasar Portugal a wasan na karshe 2021.

Hakan ya biyo bayan dokar kasa da kasa domin hana yada cutar korona, kuma Burtaniya ta ayyana Turkiya cikin wadanda annobar ke barazana a lokacin hakan yasa hukumar kwallon kafa ta turai ta canja zuwa filin wasa na Estadio de Dragoa na kungiyar FC Porto.

Haka kuma kwamitin ya tsayar cewar cikin watan Agusta za a yi bikin gudanar da jadawalin Champions League da gasar Europa league da kuma sabuwar gasar Conference League na gasar da za a fara nan gaba.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ce ta lashe kofin Champions League na kakar da aka kammala, bayan da ta doke abokiyar hamayyarta daga kasar Ingila, Manchester City a Porto, Portugal.

Sannan kuma an bayyana sauran wuraren da za a yi karawar karshe a Champions League shekaru uku nan gaba bayan da tun farko wasan karshe da ya kamata a yi a Munich a shekarar 2023, yanzu za a yi ne a shekarar 2025.

Har ila yau, filin wasa na Wembley dake London zai gudanar da fafatawar karshe a Champions League a shekarar 2024, kamar yadda aka tsara a baya in ji hukumar ta nahiyar turai.

Daga karshe birnin Dublin ne zai karbi wasan karshe a Europa League a shekarar 2024, shi kuwa Bilbao zai karbi bakuncin gumurzun karshe a karawar mata a shekarar 2024 da na Europa League a shekarar 2025.

Exit mobile version