Umar A Hunkuyi" />

Chana Za Ta Samar Da Hasken Lantarki Mega Watts 7,000 A Neja Delta

Hukumar kyautata yankin Neja Delta NDDC, ta shaida cewa, a yanzun haka tana kan tattaunawa da wani kamfanin kasar Chana, domin ya samar wa da yankin na Neja Delta hasken lantarkin da yake bukata.

Babban daraktan hukumar ne, Nsima Ekere, ya bayyana hakan, ta bakin daraktan hulda da jama’a na hukumar, Ibitoye Abosede, ranar Litinin a Fatakwal.

Mista Ekere, wanda daraktan ayyukan hukumar, Samuel Adjogbe, ya wakilce shi ya fadi cewa, a tattaunawar da suka yi da wakilan kamfanin na kasar Chana mai suna, SINOTEC, cewa an tsara wannan aikin ne domin samar da ci gaban masana’antu a yankin.

Ya bayyana cewa, da zaran an kammala aikin za a rarraba hasken lantarkin ne a sassa 18 da ke yankin.

“Mun nemi wasu hanyoyin, amma sai muka tabbatar da ba zamu iya samun abin da muke bukata daga garesu ba, don ci gaban masana’antu a wannan yankin namu.

Hakan ya sa ya zama tilas, mu yi wani hobbasan wanda zai iya ba mu abin da muke nema, ta yadda za mu janyo hankulan masu zuba jari zuwa wannan yankin namu.

Mista Ekere, ya ce, hukumar na su ta mayar da hankalinta ne kacokan wajen samarwa da yankin wata hanyar ta tattalin arziki, ba tare da dogaro da Man Fetur ko iskan Gas ba.

A cewarsa, tuni suka kammala duba yanda za a gudanar da aikin a Jihohin na yankin  Neja Delta.

Shugaban hukumar ta NDDC, ya bukaci kamfanin na mutanan Chana, da ya zo da bayanin duk yadda aikin zai gudana, da suka hada da yawan kudin da za a bukata ya zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu.

Matthew Edebbie, daraktan, ‘Income Electrik,’ wanda shine mai duba aikin, ya ce, an shirya gudanar da wannan gagarumin aikin ne domin samar da hasken lantarki mai arha, yalwatacce, tabbatacce wanda ko kiftawa ba ya yi balle wai daukewa a yankin na Neja Delta.”

Da yake mayar da martani, babban manajan kamfanin na SINOTEC, Bu Songo, ya tabbatar da bukatan samar da wani yunkuri na hadin kai domin ciyar da yanking aba ta fuskacin hasken lantarki.

Ya kara da cewa, akwai bukatar tallafin masu zuba jari daga waje don samun nasarar aiwatar da wannan aikin, a cewarsa, kamfanin na su na SINOTEC, ya kware wajen samar da hasken lantarki da kuma rarraba ta, ya kuma san hanyoyin da za a samo masu daukan nauyin irin wannan aikin.

Amma ya koka kan halin da safarar Jirage yake a wannan kasar, inda ya nemi gwamnati da ta yi wani abu a kan hakan.

“A wannan sashen na duniya, yana da wahala ka yi gasa da manyan kasashe na wasu sassan. Idan ba ka da kudi da kuma agajin babban bankin kasa wanda zai iya agaza maka da dalolin da za ka gudanar da ayyukan ka da su, ba yanda za ka iya rayuwa.

“Sam a wannan kasar ko ma mu ce a wannan nahiyar, ba inda za ka sami tabbataccen wajen da za a duba maka lafiyar Jiragenka, ta yanda za ka iya kulawa da lafiyar na su.

“Ba masu sayar da kayan gyaran da za su iya taimaka maka a kowane lokaci in bukata ta tashi, amma a Turai kuwa, duk lokacin da ka bukata ga su nan birjik,” a cewarsa.

 

Exit mobile version