Rabiu Ali Indabawa" />

Chandrayaan-2: Indiya Ta Yi Nasarar Zuwa Duniyar Wata?

Kawo yanzu ba a ga kumbon Indiya da ya kamata ya sauka a duniyar wata ba, tun bayan da masana kimiyya suka daina ganinsa ‘yan dakikoki gab da lokacin da ya kamata ya sauka.

Sai dai masanan sun shaida wa wakilin BBC na sashen Hindi, Imran Kureshi, dalilan da yasa suke ganin ba za a ce tafiyar ba ta yi nasara ba.

Miliyoyin Indiyawa ne suka kalli tafiyar kumbon, Bikram zuwa duniyar wata da jijjibin safiyar ranar bakwai ga watan Satumba – an yi ta nuna yadda tafiyarsa ta kasance ta gidajen Talbijin da kuma ta dandalin sada zumunta.

Sai dai kumbon na gab da sauka ne kuma a ka samu matsala. Nisan bai wuce kilomita 2.1 ba da inda ya kamata ya sauka, sai masana kimiyyar suka daina ganinsa da kuma jin duriyarsa. Hakan ya kawar da burin kasar na zama ta hudu a duniya da kumbonta ya sauka a duniyar watan.

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA ta ce kumbon ya yi mummunan sauka ne.

Wasu sabbin hotuna da Nasa ta fitar sun nuna inda ya kamata kumbon ya sauka, amma an dauke su ne da almuru saboda haka ba a ga kumbon ba.

Tafiyar da aka yi wa lakani da Chandrayaan-2 ta kasance mafi sarkakiyar da hukumar binciken sararin samaniya ta Indiya, Isro ta yi yunkurin yi.

Shugaban hukumar, K Siban – wanda tun da fari ya bayyana mintuna 15 na karshen tafiyar a matsayin ‘mintoci masu cike da tashin hankali’ – ya ce kashi 98 cikin dari na tafiyar ta yi nasara, kamar yadda bayanan wani kwamitin gwamnati ya nuna.

Mista Siban’s ya fuskanci suka daga masana kimiyya kan abin da ya fada, inda suke ganin ya yi wuri hukumar ta Isro ta bayyana tafiyar a matsayin mai cike da nasara, musamman tun da ba a cimma muhimmin dalilin yin tafiyar, wato sauke na’urar da zata tattara bayanai bai yi nasara ba.

Kumbon wanda aka yi wa lakabi da sunan Bikram Sarabhai, mutumin da ya kirkiri Isro, na da nauyin kilogiram 27 kuma yana dauke da na’urorin da za su tattara bayanai kan irin kasar da ke duniyar watan.

Idan da ace kumbon ya taba kasa a daidai inda aka so ya sauka a tsakanin wasu manyan ramuka biyu, da robar da ya dauka za ta mirgina ne kan kasar duniyar watan kuma ta dauki hotuna da bayanai ta aiko duniya domin a yi nazari a kansu.

Robar za ta yi tafiyar mita 500 ne daga faduwarta daga kumbon kuma za ta yi aiki na tsawon makonni biyu ne.

Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Image caption

Chandrayaan-2 is a three-in-one mission comprising an orbiter, a lander and a sid-wheeled rober

Sai dai wasu daga cikin masana kimiyyar da suka taba aiki da hukumar da ma wadanda suke aiki da ita a yanzu sun goyi bayan Dr. Siban, suna masu cewa ba a yi adalci ba idan aka ce tafiyar bata yi nasara ba.

Wani masani da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa BBC Hindi cewa ana auna nasarar ce da abubuwan da aka cimma.

Ya kara da cewa “mun kaddamar da kumbon a kan lokacin da ya dace, an sarrafa kumbon kamar yadda muka yi tsammani, wanda hakan wata babbar nasara ce ta wani bangaren, bugu da kari matakai uku da ya kamata kumbon ya bi duk an samu nasara, sai dai mataki na karshe ne kawai ba a kai gacci ba.”

Masanin ya yi nuni da cewa a yanzu za su dogara ne da bayanan da wani bangaren kumbon da ke kewaya duniyar watan ya samu. “An inganta tsawon shekarun da wannan bangaren kumbon zai yi daga shekara daya zuwa bakwai don bai kona mai ba. Mun ci sa’a kam. Kuma idan kana samun bayanai daga gareshi har tsawon shekara bakwai hakan na nufin fasahar ta yi nasara ke nan. “

Tsohon shugaban hukumar Isro, Dr Madhaban Nair ya ce “wani karamin bangare na tafiyar ne” bai yi nasara ba, kuma duk da cewa kumbon bai sauka a tsanake ba, an daina ganinsa ne yana gab da sauka a sararin duniyar watan.”

Hakkin mallakar hotoISRO

Image caption

An nuna yadda aka harba kumbon kai tsaye a gidan talbijin kuma miliyoyin mutane ne suka kalla

Ya kuma bayyana cewa dole mu duba bangarorin tafiyar – kaddamarwar da kewaye duniyar wata da kumbon ya yi da kuma raba bangarensa mai zagaye da wanda yakamata ya sauka a kan duniyar watan duk sun yi nasara.

A cewarsa. “Watakila ma mun samu hotuna na watan masu kyau da wasu al’ummar duniya suka dauka, “

Saukar kumbo a wata duniyar nasara ce da kawo yanzu kasashe uku ne kawai suka cimma – da kuma hakan ya zamo wani baban cigaba ta fuskar fasaha ga hukumar Isro da burin Indiya a sararin samaniya, a cewar wani mai rubuce-rubucen kimiyya, Pallaba Bagla.

Inda ya kara da cewa da nasarar ta kuma bude wata hanyar tafiye-tafiyen zuwa wasu duniyoyi kamar Mars a nan gaba, ga kasar ta indiya tare da ba ta damar tura ‘yan sama jannati.

Sai dai da alamu tuni Isro ta fara wannan shirin.

Dr. Siban ya shaida wa wata jaridar kasar cewa “ A watan Disambar 2021, za mu tura Ba Indiye na farko sararin samaniya da kumbonmu, Isro ta fara aiki a kan hakan.”

Exit mobile version