Charles Horton Da Nazariyyar ‘Looking-glass Self’

Kamar yadda muke kan bayani a cikin sabuwar makarantar ‘Symbolic Interactionism’, har muka kawo nazariyyar Ervin Goffman inda ya yi mana bayanin rayuwar mutane kala biyu, ya kuma kwatanta ta da yanayin yadda ɗan fim ke fitowa da wata siffa ta daban a fim, alhali a haƙiƙaninsa ga siffarsa.

Yau za mu yi dubi ne ga gudummawar wasu cikin malaman wannan makaranta ta Symbolic Interaction, musamman aikin masani Charles Horton Cooley da George Herbert Mead.

Horton Cooley shi ne ya ƙirƙiri nazariyyar ‘Looking-glass Self’ inda ya ce kowannenmu al’umma ce ke gina tunaninshi a matsayin mutum. Yadda ka ke kallon kanka a matsayin mutumin kirki ko mutumin banza, yana da alaƙa da mu’amalarka da mutane da kake rayuwa da su.

Wannan nazariyyar tana nuni da cewa, muna rayuwa ne kamar yadda mutum zai tsaya a gaban gilashin da ke nuna taswirarsa. Idan ka tsaya gaban madubi, hoton fuskarka za ka gani, idan kana da tsage, tabo, haske, duhu duk za ka gani. Wannan a babin taswira kenan, ko kuma na ce kammanin mutum. Shi ‘looking-glass’ ya kalli abin ne ta fuskacin yadda mutum ke kallon kansa a rayuwa; ƙimarsa, mutuncinsa, da sauransu duk yana auna su ne da irin mu’amalar da mutane ke yi da shi.

Mutum kullum yana cikin tantamar yadda mutane ke kallonsa. Idan ka fara tunanin cewa wasu da ka ke mu’amala da su suna yi maka kallon daƙiƙi, za ka fara sa wa kanka shakkun cewa, anya kai ba daƙiƙi ba ne kuwa?

Cooley ya ci gaba da cewa, mutum yana saurin fassara yanayin mutane. Idan ka shiga wuri sai ka ga fuskokin mutane sun yamutse, wasu ma cikinsu suna ɗan toshe hanci. Za ka fara zargin ko turaren da ka fesa a gida ne yake wari, alhali a ƙa’ida ƙamshi ya kamata turaren yake yi. Wannan zai iya tilasta mutum ya koma gida don canza kaya ko kuma ya haƙura ya zauna a takure cikin ƙunci.

Mutum ne da kansa yake gina kansa, kamar yadda na faɗi a sama cewa ta yadda mutane suka mu’amalance shi. Wannan mu’amala ta mutanen da muke rayuwa da su, za ta yi tasiri ba kawai kan suturarmu ba, har da yadda muke kallon kanmu. Idan mutanen da ke zagaye da kai kullum suna ma’amala da kai a matsayin wani mabuƙaci, nauyi, gajiyayye ko mara ilimi wannan zai sa mutum ya riƙa kallon kanshi a haka, kuma zai kashe masa gwiwa ga ƙoƙarin inganta rayuwarsa.

Akwai wani abu mai muhimmanci da ya kamata mu sani, ko da a ce mutum ne ya yi kuskuren fahimtar yadda mutane ke kallonsa (bisa zato), toh a haka zai gina kanshi da rayuwarshi. Sannan iyaye suna da rawar takawa wurin gina rayuwar ‘ya’yansu yadda za su riƙa ganin darajar kansu.

Ana iya yin gyara ga yanayin yadda mutum ke kallon kansa, amma sai idan a shirya a ƙashin kansa cewa zai gyara ɗin

Shi kuwa George Herbert Mead a nashi nazariyyar wacce ya kira da ‘Role Taking’ ya nuna muhimmancin wasa ne musamman tun daga yarinta. Domin a faɗinsa, yayin da muke wasa ne muke gina ɗabi’armu ko kuma haƙiƙanin kanmu. Daga wasa ne muke koyon sanya kawunanmu a halin da wasu suka tsinci kansu. Daga nan kuma mu fahimci yadda suke ji idan aka yi musu wani abu.

A cewarsa, ko a yayin wasa, za ka yaro yana kwaikwayon ɗabi’u da halayen mutanen da suka fi kusanci da shi ne (mutane masu tasiri a rayuwarmu), kamar iyaye da ‘yan uwa makusanta. A yayin wasannin yarinta, za ka ga muna kwaikwayon sanya babbar riga yadda mahaifinmu ke sawa. Ƙannenmu ko yayyinmu mata kuma su riƙa kwaikwayon girkin ƙasa da sauransu.

A haka za mu yi ta kwaikwayon rayuwar mutanen da muke tare da su da kuma waɗanda ke burge mu (masu tasiri), amma a yayin da muka girma a maimakon mu riƙa kwatanta rayuwarsau a cikin wasa, sai mu riƙa ƙoƙarin gina kanmu da abubuwan da muke koyo daga rayuwarsu.

Mead ya kawo matakai uku da ake bi wurin koyon ayyukan wasu. Sune kamar haka:

  1. Kwaikwayo: a yayin da muke ƙananan yara ‘yan shekara uku, muke fara kwaikwayon mutane. A wannan shekarun ba mu da hankalin da za mu iya bambance kawunanmu da wasu, saboda kawai muna iya kwaiwayon motsi ne (alami) da kuma tsintar kalamai. A wannan matakin ba muna sa kanmu a rayuwar wasu bane, muna shirya kanmu ne don hakan.
  2. Wasa: zango na biyu na fara wa daga shekara 3 zuwa 6, a nan ne muke yin wasa don kwaikwayon rayuwar makusantanmu ko wasu da ke burge mu. Za ka ga muna wasa a matsayin baba, sojoji, ‘yan dambe, Spiderman ko wani ɗan fim ɗin yara. Su ma a nan ne za ka ga mata na kwaikwayon uwa, malamar jinya, sarauniya da sauransu. A wannan matakin muna kwaikwayon har da yanayin sutura.
  3. Wasanni Cikin Abokai: wannan matakin yana nufin mun ɗan tasa, don har mun shiga makaranta. A wannan matakin George Herbert Mead ya kafa misali da wasan zungure ‘Baseball’. A wannan wasan mutum ba kawai ta kansa yake ba, a’a yana mayar da hankali ga rawar da sauran abokan wasansa ke takawa, saboda sanin matakin da zai ɗauka na gaba.

Zan ci gaba…

 

 

 

Exit mobile version