Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home FITATTUN MATA

Charlette N’Guessan: Matashiyar Da Ta Lashe Babbar Kyautar Injiniyanci Ta Afirka

by Muhammad
January 22, 2021
in FITATTUN MATA
3 min read
Injiniyanci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ko-kun-san….

Charlette N’Guessan wata matashiya ce da ke zaune a  Birnin Accara ta kasar Ghana wacce ta zama abun alfahari ga Afrika a fannin Injiniyanci?

Matashiyar tauraronta ya cilla kuma na cigaba da cillawa ne bayan da ta samu nasarar kirkirar wani manhajar fasahar da ke taimakawa wajen tantancewa da gano bidiyo ko hoton da aka dauka. An yi amannar na’urar zai taimaka wajen gano masu kutse da kuma masu aikata ba daidai ba tare da rage kaifin matsaloli a nahiyar Afrika.

Wace Ce Charlette N’Guessan?

Bayan kasancewarta ‘yar Afirka ta farko da ta samu wannan kyautar, ta kuma daukaka darajar kasar Ghana na kasancewa ta farko da ta samu kaiwa ga wannan babban matakin.

N’Guessan ta lashe kyautar ne saboda fasahar da ta kirkira ta BACE API ita da ‘yan tawagarta, fasahar da ke ganowa da tantance mutane a yayin da ake bukatar hakan.

Wannan fasahar an sanya hikima wajen ganin an gano tare da tantancewa ta hanyar fikira da hikima cikin sauki, wanda jama’a da kamfanoni da dama suka gamsu an zuba kwarewa da kokari sosai wajen kirkirar wannan manhajar.

Fasahar na iya tabbatar da hoton mutum na asali ko bidiyo da aka dauka a wayoyin salula tare da tantance wanda ake son tantancewa ko ganowa cikin hanzari. Wannan manhajar kai tsaye zai taimaka wa kamfanoni da hukumomi sosai wajen saukake ayyukan da ke gabansu.

Na’urar da ta samar, bai bukatar wasu muhimman kayayyaki wajen tafiyar da kansa. Wani abun sha’awa da burgewa da wannan na’urar mai amfani da wayoyin salula ko kwamfutocir da aka samar ba kamar na’urar Global AI Systems ba ne, shi BACE API an samar ne tare da ingantasa wanda zai yi aiki sosai musamman don ‘yan Afrika.

N’Guessan a matsayin wacce ta lashe gasar Injiniyanci na Afrika ta samu kyautar fan dubu 25,000.

N’Guessan da abokan aikinta ne suka kirkira wannan manhajar a shekarar 2018 bayan sun gudanar da wani dogon bincike wanda ya nuna cewa bankuna a Ghana su na da muhimman matsaloli ta hanyar yanar gizonsu, wanda suke fuskantar masu kutse da ‘yan damfara. Don haka ne suka dukufa binciken hanyoyin da za su taimaka wajen samar da manhajar da zai taimaka wajen shawo kan lamarin.

An kirkiri fasahar ne domin taimakawa ma’aikatu da kamfanonin da ke dogaro da na’urar tantance mutane. Kuma yanzu haka kamfanoni biyu na kasar Ghana na amfani da manhajar domin tantance kwastamominsu da taskace lamura.

Gasar baje kolin fasaha ta Africa Prize for Engineering ya kasance wani babban gaza da masu hasaha suke baje kolinsu domin ganin an samar da wani cigaba da fuskacin kere-kere. Royal Academy of Engineeing da ke kasar UK ce ta kaddamar a shekarar 2014 wanda kuma ake yinsa duk shekara.

Lokacin da matashiyar ta samu wannan nasarar, ta samu lambar yabo da jinjina daga bangarori daban-daban ko Ministan Afrika a UK, James Duddridge sai ya nuna jinjiya da ta jarumar matashiyar murnar daukaka Afrika da ta yi bisa nuna hazakar samar da manhajar da zai taimaka wa kasa da kasa wajen rage kaifin matsaloli musamman na ‘yan damfara da masu kutse.

Ya nuna bukatar a samar da wasu matan da matasa da za su rungumi harkokin fasaha wajen ganin sun tabuka ababen a zo a gani wajen kyautata rayuwar jama’a musamman ta fannonin kimiyya da fasaha.

 

Ga masu sha’awar shiga wannan filin su aiko da takardar tarihinsu ta wannan kafa: kidrisdoya200@gmail.com ko kiran waya kai tsaye 07069724750

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ba A Zama A Kashe Komai A Ce Aure Ake Jira –Hauwa Muhammad

Next Post

Lafiya Jari: Alakar Cin Kwai Da Ciwon Zuciya

RelatedPosts

Ellen Johnson Sirleaf: Mace Ta Farko Da Ta Fara Zama Shugaban Kasa A Afrika

Ellen Johnson Sirleaf: Mace Ta Farko Da Ta Fara Zama Shugaban Kasa A Afrika

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya Ko-kun-san…. Ellen Johnson Sirleaf ce mace...

Hajiya Dijatu Yerima Balla: Fitacciya A Fannin Ilimi Da Shakatawar Yara

Hajiya Dijatu Yerima Balla: Fitacciya A Fannin Ilimi Da Shakatawar Yara

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Ko-Kun-San… Dijatu Yerima Balla tsohuwar malamar makaranta ce, kuma mamallakiyar...

Amina

Amina Nikatau: Sarauniyar Da Ta Mulki Masarautar Zazzau Bisa Jarumta

by Muhammad
4 weeks ago
0

Ko-kun-san…. Sarauniya Amina Nikatau ce ta ki aure domin kar...

Next Post
Kwai

Lafiya Jari: Alakar Cin Kwai Da Ciwon Zuciya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version