Connect with us

WASANNI

Chelsea Ta  Cimma Yarjejeniya Da Sabon Mai Koyarwa

Published

on

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila ta cimma yarjejeniya da Maurizio Sarri, tsohon mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya.

Kungiyar Chelsea dai ana rade radin zata rabu da mai koyar da kungiyar ta, Antonio Conte, wanda shima dan kasar Italiya ne sakamakon rashin buga abin ardiki da kungiyar tayi wanda yasa ta kammala gasar firimiya a matsayi na biyar kuma bazata buga gasar zakarun turai ba a shekara mai zuwa.

Kawo yanzu dai Chelsea tana tattaunawa da Conte akan kudinsa da zata biya shi idan ta koreshi wanda yakai kusan fam miliyan 17 sai dai kuma har yanzu basu fara tattauna maganar albashi da Sarri ba wanda suke shirin dauka.

Idan har Chelsea tanason daukar Sarri a wannan watan sai ta biya kungiyar Napoli fam miliyan 7 idan kuma batason biya dole sai dai ta jira sai wata mai kamawa lokacin da kwantaragin Sarri zai kare a kungiyar Napoli.

Sarri, wanda ya shafe shekaru uku a Napoli ana tunanin itama kungiyar kwallon kafa ta Zenith ta kasar Russia tana zawarcinsa domin yakoma kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: