Chelsea Ta Sallami Kociyanta, Frank Lampard

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sallami mai horar da ‘yan wasanta Frank Lampard daga mukaminsa bayan da kungiyar ta tsaya a matsayi na tara a teburin gasar Premier League ta Ingila.
Matakin sallamar Lampard na zuwa ne, bayan da club din ya cimma matsayar a sallame shi saboda shan kaye da kungiyar ta yi har sau biyar cikin wasanni takwas da ta buga.

Lampard ya kasance koci na goma da kungiyar ta Chelsea ta sallama a zamanin Roman Abramovich da ke mallakar kungiyar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Abramovich, ya kwatanta Lampard a matsayin mutum “mai sanin ya kamata” yayin da yake sanar da korar Lampard, yana mai cewa, “a halin da ake ciki, mun yi ammanar cewa abu mafi a’ala shi ne, mu sauya manajojin wannan club din.”

Duk da cewa Chelsea ta lallasa Luton Town a ranar Lahadi don kai wa ga zagaye na biyar a gasar FA Cup, hakan bai sa an ragawa Lampard ba.

Yanzu haka an zabi Thomas Tuchei, don maye gurbin Lampard inda ake sa ran nan ba da jimawa ba za a sanar da nadinsa.

Tuchie ya taba horar da PSG da Borrussia Dortmund.

Exit mobile version