Abba Ibrahim Wada">

Chelsea Za Ta Sayar Da ’Yan Wasa Ciki Har Da Jorginho

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta saka wasu daga cikin ‘yan wasan ta a kasuwa sakamakon kudin da kungiyar take bukata domin ci gaba da sayan ‘yan wasan da zasu karawa kungiyar karfi a kakar wasa mai zuwa.

Shugabannin kungiyar dai sun bawa mai koyar da ‘yan wasa Frank Lampard kudi domin ya sayi sababbin ‘yan wasa a kasuwa tuni dai kungiyar ta shirya rabuwa da akalla ‘yan wasa goma daga cikin tawagar ta Chelsea.
A kwanakin baya Chelsea ta sayi dan wasan gaba daga kungiyar kwallon k afa ta RB Leipzig, Timo Werner sannan da dan wasa Hakim Ziyech daga Ajad ta kasar Holland da dan wasa Kai Habertz daga Bayern Liberkusen da Ben Chilwell daga kungiyar Leceister City sannan kungiyar ta dauki dan wasa Thiago Silba daga PSG kyauta har ila yau Chelsea ta na dab da daukar mai tsaron raga daga kungiyar Rennes ta Faransa mai suna Mendy.
Sai dai duk da haka shugabannin kungiyar ta Chelsea sun tabbatar wa da mai koyarwa Frank Lampard cewa dole sai ya sayar da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar idan har yana fatan su ci gaba da bashi kudi yana sayan sababbin ‘yan wasa.
Wasu daga cikin ‘yan wasan da a ke ganin za su bar kungiyar akwai mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga wanda ya koma Benci tun kafin kammala wasannin firimiya sai kuma dan wasan tsakiya dan kasar Italiya, Jorginho.
Bugu da kari Lampard ya saka dan wasan baya Tomori tare da abokin wasansa Kurt Zuma a kasuwa da kuma dan wasa Andreas Christensen wadanda gaba daya ‘yan wasan baya ne su ukun kuma sun buga wasanni da dama a kakar data gabata.
Sannan Chelsea tana shirin sayar da dan wasan kasar Italiya, Emerson Palmeri da dan wasan Nigeriya Victor Moses wanda yake zaman aro a Inter Milan da tsohon dan wasan kungiyar Leceister City Danny Drinkwater da dan wasa Tiemou Bakayoko wanda yake shirin komawa AC Milan ya yinda tuni dan wasan gaba Mitchy Matchuayi ya kuma Crystal Palace a matsayin aro na shekara daya.
Lampard yana son daukar dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta West Ham United Declan Rice wanda dole sai kungiyar ta sayar da wasu daga cikin ‘yan wasanta sannan zata samu damar daukar dan wasan wanda a baya ya taba bugawa kungiyar wasa lokacin da yake matashi.
Tuni kungiyar ta rabu da dan wasa Willian wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sannan  shima dan wasa Pedro dan kasar Sipaniya wanda ya koma Chelsea daga Barcelona ya koma kungiyar AS Roma ta kasar Italiya shi ma bayan kwantiraginsa ya kare sai dai wasu rahotanni daga kasar ta Ingila sun bayyana cewa Chelsea ta kusa kammala yarjejeniya da Rennes akan mai tsaron raga Mendy, wanda tuni ya kulla yarjejeniya da Chelsea a kan albashi da kwantiragin shekara biyar.

Exit mobile version