CRI Hausa" />

Chen Zifang: Nakasasshen Matashi Basine Mai Kokarin Taimakon Al’umma

Chen Zifang wani mutum ne mai fama da larurar nakasa, wanda aka haifa ba hannaye. Duk da haka ya yi kokarin koyon fasahohi don samun damar kula da kansa, har ma ya yi amfani da fasahar da ya koya wajen taimakawa mutanen kauyensa fita daga kangin talauci.

An haife Chen Zifang a shekarar 1989, a gundumar Badong dake lardin Hubei na kasar Sin. An haife shi ba shi da hannaye, sa’an nan lokacin da yake da watanni 9 a duniya, mahaifinsa ya mutu sakamakon cutar shan inna, lamarin da ya sanya shi Chen Zifang, da mamarsa, da yayansa zama cikin talauci.
Saboda yadda yake fama da larurar nakasa, Chen ba ya iya tsayawa da kansa, har zuwa lokacin da ya kai shekaru 4 da haihuwa. Sa’an nan, lokacin da ya ke da shekaru 7 a duniya, ya ga yadda sauran yara suka fara shiga makaranta, shi ma yana sha’awar zuwa makaranta matuka. Sai dai rashin hannaye, ya sa jami’an makarantu suka rika nuna tsoron wahalar dawainiya da shi.
Don neman shiga makaranta, Chen ya yi kokarin koyon fasahar rubutu ta hanyar rike alkalami da yatsun kafarsa. Sa’an nan mamarsa ita ma ta dinga zuwa makaranta har sau 8, inda ta yi kokarin lallashin malamai don su yarda su karbi danta. Bayan da ya kai shekaru 8 malam Chen da mamarsa sun sake zuwa wata makaranta, inda Chen ya nuna wa malamai yadda ya iya rubuta kalmomi, da cin abinci, da sanya tufafi, da wanke fuska, duk da kafafuwansa, lamarin da ya burge malaman matuka, don haka a karshe sun yarda da karbe shi a matsayin daya daga daliban makarantarsu.
Malam Chen ya ce, “A lokacin, na dade ina fama da larurar nakasa, don haka ina kallon karatu a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci, wanda zai iya taimaka min da iyalina kawar da talauci.” Saboda haka Chen ya yi matukar kokari wajen karatu, duk da cewa yadda yake rubuta abubuwa da kafa na yi masa wahala sosai. Kamar yadda a kan ce kokarin haka ya kan cimma ruwa, yadda ya yi kokari fiye da sauran dalibai, ya sa makin da ya samu a jarrabawa ya zama na farko a cikin daliban makarantarsa har shekaru 3 a jere.


Gidan malam Chen yana cikin yankin duwatsu ne. A lokacin ya kan yi tafiya har tsawon kilomita 8 a ko wace rana don zuwa makaranta. Sakamakon yadda ba shi da hannu, wani lokaci ya kan fadi kasa, har ma ya ji rauni, amma bai taba saduda ba.
Sai dai zuwa lokacin da zai shiga wata makarantar midil, wannan makarantar tana da matukar nisa da gidansa, inda nisan ya kai kilomita 20. Don haka, ba zai iya ci gaba da karatu ba, saboda ya zai iya yin tafiyar tsawon kilomita 40 a kowace rana, cikin wani yanki mai duwatsu, tare da tabbatar da tsaron kansa ba. Musamman ma ta la’akari da yadda yake da shekaru 14 kacal a lokacin.


Kasa zuwa karatu a makaranta ya sa malam Chen Zifang bakin ciki sosai, har ma ya rika jin kamar ya kashe kansa. Sai dai bisa kulawa da kaunar da mamarsa ta ba shi, sannu a hankali ya farfado, inda ya fara koyon ayyukan gida, irinsu tsabtace muhalli, da dafa abinci, da dai sauransu. Bayan ya mallaki wadannan fasahohi, wato yin ayyukan gida da kafa. Sa’an nan ya fara neman hanyar daidaita yanayin da yake ciki na fama da talauci. A lokacin, wato shekarar 2008, ragon gabas da ya kiwata ta haifi ‘ya’ya guda 13, don haka Chen ya fara tunanin kiwon aladai. Mamarsa ta ga ba isashen mutane a gida wadanda za su kula da kananan aladai, ban da wannan kuma ba su da kudin sayen abincin aladai, don haka ta yi kokarin lallashin malam Chen kar ya fara wannan aiki na kiwo ragunan gabas. Amma Chen baya tsoron wahala, ya riga ya dauki niyyar kula da wadannan ragunan gabas da kansa. Don haka ya fara kokarin yankar wasu ciyayi da aladai suke son ci, wadanda zai iya dinga yin amfani da su a matsayin abincin aladai. Sai dai aikin yanko ciyayi shi ma wani aiki ne mai matukar wahala gare shi. Domin sauran mutane za su iya kama ciyayi da wani hannu, sa’an nan su yi amfani da daya hannun wajen yankar ciyayin. Amma shi sai ya zauna a kasa, ya yi amfani da yatsun kafa na hagu waje kama ciyayi, sa’an nan kafarsa ta dama ta rike wata wuka, tana yankar ciyayin. Ya kan ji rauni a kafafuwansa, har yanzu ana iya ganin tabbo da yawa a kansu. Sai dai bayan shekara daya yana kokarin kiwo aladai, bai samu riba ba, har ma ya yi asarar Yuan dubu 4 sakamakon yadda ya kasa sayar da aladan da wani farashi mai kyau. Lamarin da ya sake jefa shi cikin wani yanayi na bakin ciki matuka.
Ganin wannan yanayin da Chen yake ciki, wasu mutanen kauyensa sun zo sun lallashe shi, inda suka ba shi shawarar yin watsi da duk wani aikin da yake yi, sa’an nan ya zauna a gaban kofar gwamnatin wurinsu don rokon a ba shi taimako. Sun ce kai nakasasshe ne matashi, su jami’an gwamnati ba za su nade hannu suna kallon yadda kake fama da yunwa ba. Amma Chen Zifang bai yarda da wannan shawara ba. Ya ce, “ Gwamnatin kasarmu na samar da manufofi masu kyau, dole ne za su kula da ni, amma idan na yi zaman kashe wando don jiran samun taimako kawai, hakan ba zai taimaka mana kawar da talauci daga tushe ba. Ban da wannan kuma, ina jin kunyar rokon samun wani abu daga sauran mutane.” Shi ya sa bai tafi rokon taimako ba, maimakon haka ya ci gaba da kokarin neman hanyar daidaita yanayin da yake ciki.
A lokacin, yayansa ya sayo masa wata tunkiya, don haka ya fara kiwon raguna. Bayan wasu shekaru 2, ya samu raguna 35. Sa’an nan ta hanyar sayar da raguna, yana iya samun fiye da Yuan dubu 10 a kowace shekara. Daga bisani, ya sayi wata wayar salula, inda ya fara gwada yin amfani da yatsun kafa wajen sarrafa wayar ta sa, abin da ya hada shi da shafin yanar gizo ta Internet. Daga baya ya fara tunanin dalilin da ya sa bai iya sayar da ragunansa da wani farashi mai kyau ba, idan an kwatanta da ragunan da sauran mutane ke sayarwa. Sa’an nan ya fara fahimtar cewa, yadda yake zama a cikin yankin duwatsu, inda ba a samun bayanai cikin sauki, da kuma rashin hanyoyin jigilar kaya masu kyau, shi ne dalilin da ya hana tattalin arzikin wurinsu samun ci gaba. Don haka, ya fara tunanin wata dabarar da zai iya yin amfani da ita don daidaita wannan yanayin da yake ciki.
A shekarar 2015, gwamnatin gundumar Badong ta fara wani aiki na taimakawa manoman wurin wajen raya harkar kasuwanci ta hanyar yin amfani da shafin yanar gizo na Internet. Wannan manufa ta sa Chen Zifang shi fara son bude wani shago a shafin Internet. Wansa ya ce wannan aiki yana da wuya, saboda Chen wani mutum ne dake fama da larurar nakasa, kana bai samu damar yin karatu a makaranta sosai ba. Amma Chen ya ce, “ Ba komai. Ko da yake ba ni da hannu, amma yanzu ina iya yanko ciyayi da kafa, da sauran ayyukan gida. Duk wata fasaha zan iya koyonta.”
A lokacin, gwamnatin kasar Sin ta riga ta fara daukar matakai na taimakawa matalauta don fid da su daga kangin talauci, lamarin da ya sa Chen ke samun tallafi a duk wata. Sa’an nan ta hanyar kiwon raguna, shi ma yana samun wasu karin kudin shiga. Don haka shi da iyalinsa sun samu damar gina wani sabon gini mai benaye 2, sun sayo wani keken inji mai wili 3, domin yayan Chen Zifang ya yi amfani da shi wajen taimakawa sauran mutane daukar kaya. Ta wannan hanya sannu a hankali, Chen ya fara samun wasu kudade. Wannan ya taimakawa karfafa niyyarsa ta bude wani shago kan shafin yanar gizo ta Inernet.
Zuwa shekarar 2016, Chen ya shiga wani kwas na horar da fasahar kasuwanci ta yanar gizo, inda ya koyi fasahar sarrafa na’ura mai kwakwalwa ta kamfuta. Daga baya, hukumar gundumarsa ta ba shi wani shago a cikin kasuwa ba tare da karbar kudi ba, inda ya ajiye na’urar kwamfuta, ya fara samar da hidimar sayar da kayayyaki kan shafin yanar gizo.
Bayan da manoman wurin suka ga yadda shagonsa yake, sun yi mamaki sosai, domin ba su amince cewa za a iya sayar da kaya, kawai ta wata na’urar kwamfuta ba. Amma malam Chen cike yake da imani, don ya san yadda yanar gizo ta Internet take hada mutane daga duk wata kusurwa, kuma ya san ta wannan kafa za a iya fitar da kayayyakin manoman kauyensa daga yankin duwatsu da suke ciki zuwa sauran wurare.
Sai dai a shekara ta farko, maimakon samun riba, Chen ya ci bashin da ya kai Yuan dubu 30. Duk da haka, yana kokarin nuna gaskiya yayin da yake hulda da sauran mutane. Daga baya, karin manoma suka fara hadin gwiwa da shi. Inda yake sayar da wasu kayayyakin musamman da manoman wurinsu ke samarwa, irinsu dankali, da Walnut, da Chestnut, da dai sauransu, kan shafin Internet. Yadda yake kokarin tabbatar da ingancin kayayyaki, ya sa abubuwan da yake sayarwa samun karbuwa. Har ma a duk wata ya kan iya sayar da dankalin da yawansa ya kai kilogram dubu 100.
Ta haka, bayan ya kwashe shekara 1 yana gudanar da aikin, yawan darajar kayayyakin da ya sayar a duk shekara ya kai Yuan miliyan 1.2. Sa’an nan ya samu damar biyan dukkan bashin da ya ci, tare da samun ribar da ta kai Yuan dubu 60. Daga baya ya kafa wata kungiyar hadin gwiwar manoma, inda dukkan manoman wurinsu suke ba shi amfanin gonar da suka samar, don ya taimakawa wajen sayar da su kan shafin yanar gizo.
A wannan lokaci ne kuma Chen ya fara gano cewa, idan ana son sayar da dimbin kayayyaki a shafin Internet, ana bukatar samun wasu takardun da ake bayarwa don tabbatar da ingancin kayayyakin. Don samun wadannan takardu, ana bukatar kashe kudi da yawa, amma a lokacin Chen ba shi da wannan kudi. Wannan matsala ta rashin takardun da ake bukata, ta sa Chen ya kasa cimma alkawarin da ya yi wa manoman, na taimaka musu sayar da dukkan kayayyakinsu.
Chen ya yi tunani sosai kan wata dabarar da zai iya yi don daidaita wannan matsala. Sa’an nan ya gano wasu bidiyon da aka watsa kan shafin Internet, inda ake nuna wa jama’a yadda ake samar da wasu kayayyaki, don neman tallarsu. Ya ga shi ma zai iya daukar wannan sabuwar dabara, don haka shi ma ya fara daukar bidiyo, inda ya nuna wa masu kallo yadda yake zaman rayuwa, da yadda yake aiki a cikin gonaki. Ya ce, “ Bidiyo na farko da na dauka, shi ne game da yadda nake hako dankali daga kasa da kafafu na, sa’an nan na dauke shi zuwa gida, na tsabtace shi, tare da dafa abinci da shi.”
Hotunan bidiyon da Chen ya dauka suna da burgewa, kuma masu kallo suna mamaki kan yadda wani nakasasshen matashi marasa hannaye zai iya kula da kansa, da yin ayyuka daban daban kamar yadda sauran mutane masu lafiya suke yi. Saboda haka, bayan da Chen ya kwashe watanni 2 yana kokarin tsara bidiyo da watsa su ta shafin Internet, yawan mutane masu sha’awar bidiyonsa ya riga ya kai fiye da dubu 200.
Bayan da Chen ya kara yin suna a shafin yanar gizo, wata rana, wani manomi ya buga masa waya, inda ya roki Chen don ya taimaka masa wajen sayar da lemu. Chen ya yarda, ya hau icen lemu, inda aka dauki wani bidiyon, game da yadda yake tsinkar lemu a kan ice, abun da ya janyo hankalin dimbin mutane, kuma da yawa daga cikinsu sun sayi lemun, ta yadda aka sayi dukkan lemun da wannan manomi ya samar cikin sauri. Yayin da yake tsinkar lemu a kan wani ice, Chen ya gaya ma masu kallo cewa, “ Kar ku sayi kayayyakin da na nuna muku bisa tausayi. Abin da nake so shi ne, ku sayi wadannan abubuwa, saboda suna da inganci, da yadda kuka yarda cewa ni mutum ne mai gaskiya.”
Duk wani alkawarin da Chen ya yi wa jama’a, yana yin kokarin tabbatar da cewa ya cika shi. Misali, a wannan shekarar da muke ciki, annobar COVID-19 ta haddasa babbar asara a birnin Wuhan dake tsakiyar kasar Sin. A lokacin, Chen ya yi alkawarin cewa, shi da abokanansa za su ba da wasu lemu kyauta ga mutanen Wuhan. Da farko dai, wasu mutane sun nuna shakku kan ko zai cika alkawarin da ya yi. Don kawar da shakkun da suka nuna, Chen ya dauki bidiyon don nuna yadda shi da manoman wurinsa suke zuba lemu a cikin wata babbar mota, sa’an nan shi da kansa ya shiga cikin motar, inda ya sa ido kan yadda aka yi jigilar lemun zuwa birnin Wuhan, don gabatarwa mutanen birnin a matsayin kyauta.
Da ya ambaci yadda yake kokarin taimakawa sauran mutane, Chen ya ce, “Mutane da yawa sun taba ba ni taimako, don haka duk wani abun da na yi musu, na yi shi ne da niyyar nuna musu kauna da godiya. Na san, idan na ci gaba da daukar wannan ra’ayi na godiya ga sauran mutane, to, duk wani aikin da na yi, zan iya yin shi da kyau.” (Bello Wang)

Exit mobile version