Tare da Sani Anwar 08036365416 (leadershipayau.com)
Kasar China ta ce zata goyi bayan majalisar dinkin duniya a kokarin da take yi na daukan karin matakai akan kasar Koriya ta arewa domin gwajin makamin nukiliya na baya-bayan nan da ta yi.
A ranar Alhamis ministan harkokin wajen China, Wang Yi yayi wannan furuci wajen wani taron ‘yan jarida a birnin Beijing. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya maida martani ya dauki dukkan matakan da suka kamata na tinkarar wannan rikici.
To amma Mr Wang ya kuma jaddada cewa tilas takunkumi da matsin lamba su tafi kafada da kafada da yin shawarwari da Koriya ta arewan.
A yayin da China ke cewa tana goyon bayan matakan da Majalisar Dinkin Duniya zata dauka akan Koriya ta arewa, ita kuma kasar Rasha tana ta kokarin ganin an amince da Koriya ta arewa a zaman kasa mai karfin makaman nukiliya. Kuma Rashan bata goyi ko kuma bata goyon bayan matsayin Amurka da kawayenta akan kasar Koriya ta arewa.
A yayin da yake ganawa da shugaban Koriya ta kudu Moon Jae’in a Bladibostok yau Alhamis, shugaban Rasha Bladimir Putin ya kara yin kiran da’ayi shawarwari da Korea ta arewa domin magance rikicin nukiliyan.