Connect with us

LABARAI

Chiroman  Agbolagu Ya Jinjina Wa  Gwamna Sule Kan Ciyar Da Jihar Nasarawa Gaba

Published

on

Wani sanane mai rike da sarautar gargajiya Chiroman  Agbolagu Alhaji Abdullahi Musa dake a jihar Nasarawa ya nuna jin dadinsa kan nasarorin da Gwamnan jihar  Injiya Abdullahi Sule ya samar a jihar a cikin shekara daya na shugabancin sa.
Abdullahi Abdullahi Musa ya sanar da hakan ne  a cikin wata sanarwa da ya bai wa Leadership Ayau a Kaduna, inda ya ci gaba da cewa, Injiya Abdullahi Sule  ya yi matukar kokari wajen samar da ayyukan da suka inganta rayuwar alummar jihar a cikin shekara daya.
Basaraken wanda ya kasanace daya ne daga cikin masu fada aji a cikin yankin Rindere dake a garin Lafia a jihar ta Nasarawa, ya kuma ta ya Gwamnan jihar  Injiya Abdullahi Sule, yan majalisar dokokin jihar murnar cika shekara daya kan karagar mulki, inda kuma ya shawarce su kada su gajiya wajen samar da ayyukan da zasu ciyar day an jihar da kuma jihar gaba.

Alhaji Abdullahi ya danganta Gwamna Sule a matsayin mutum mai rikon gaskiya da rikon amana, inda ya ce,  alummar yankin Rindere dake da kauyuka 43 na matukara alfahari da irin ayyukan ci gaba da Gwamna Sul ya samar a jihar.

A cewar sa, alummar Rindere da suka taso daga  daular Kwararafa  tun a karni na 12, an san su da bin dka da oda kuma zasu ci gaba da bai wa Gwamnna  Sule goyon bayan day a dace don a samu sakamakon da ake bukata a na kara  ciyar da jihar gaba.

Alh Abdulllahi wanda akafi sani da Allahji Abdullahi Keffi ya sanar da cewa, Gwaman Sule ya kasanace mutum mai da’a, mai bin doka da oda  da kuma tabbatar da yana bin ka’ida wajen gudanar da aikin gwamnati.

Ya yabawa gwamnan kan gina gadoji 7 a yankin, inda ya kuma roki gwamnna day a gina masu hanyar data tashi daga Ashige-Gidan Buba-Wuga-Padama zuwa Padama ta Kudu zuwa Agbolagu ta Arewa don a samu a dinga gudanar da zirga-zirgar gudanar da kasuanci a cikin sauki.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar data karbi makarantar Sakandare da a yankin  Agbolagu  da alumma suka gina ta hanyar aikin sa kai a cikin shekaru 15 da suka gabata, musamman don kara gina azuzuwa da kuma kara samar da kayan aiki a makarantar.

A  karshe ya  yi kira ga daukacin alummar jihar Nasarawa kada su yi kasa a gwaiwa ajen ci gaba da bai wa  Gwamna Abdullahi Sule goyon bayan su don ya cimma burin ciyar da jihar gaba da kuma alummar jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: