Chora: An Sake Mayar Da Wani Coci Mai Tarihi Zuwa Masallaci A Turkiyya

Chora

Shugaba Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Juma’a ya saka hannu kan wata doka Ta mayar da wani tsohon coci na Karni na 6 da aka mayar gidan tarihi zuwa masallaci a Istanbul.

Ginin na da nisan kilomita shida ne daga fitaccen ginin Hagia Sophia da a watan July aka mayar da shi masallaci har Musulmi sun fara Sallah.

Dokar da shugaban kasar ya saka wa hannu kamar yadda aka wallafa ta umurci a mayar da gidan tarihin Chora zuwa Masallaci. A cewar dokar mai kama da wadda aka yi a game da Hagia Sophia, za a mika ginin ga hukumar kula da addini na kasar Turkiyya.

Ginin wanda aka sani da sunan ‘Church of Holy Saviour’ ya yi fice saboda zane da wasu kayayyakin tarihi da ke cikin sa. Daular Usmaniyya ce ta mayar da shi zuwa masallaci a karni da 16 sannan mahukunta kasar Turkiyya suka mayar da shi gidan tarihi a shekarar 1945.

A watan Nuwamban 2019, babban kotun kasar Turkiyya ta soke dokar da aka yi a 1945 inda hakan ya bayar da damar a mayar da shi Masallaci. Chora da Hagia Sophia dukkan su da farko coci ne na Kirista sannan gidajen tarihi, inda daga baya kuma aka mayar da su Masallatai

A watan Yuli, Amurka, EU, Rasha da UNESCO da wasu shugabannin coci-coci da dama sun nuna damuwar su kan sauya Hagia Sophia zuwa Masallaci duba da cewa abin tarihi ne da al’ada ga Musulmi da Kirista baki daya.

Shugaba Erdogan ya yi watsi da sukar da suka yi inda ya ce ba zai amince da katsalandan daga kasashen waje ba tunda Turkiyya kasa ce mai ‘yancin kanta. Amma a halin yanzu ba a sanar da ranar da za a fara Sallar a Chora ba.

Exit mobile version