Connect with us

RAHOTANNI

Ci Gaban Harkokin Kasar Sin Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

Published

on

Alkaluman ma’aikatar kasuwancin kasar Sin na nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar bana, gaba daya adadin kudin da aka samu a fannin shige da fice na harkokin hidima ya kai kudin Sin yuan biliyan 2975.4, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, inda ci gabansa ya kai matsayin koli a tarihi, haka kuma adadin ya kai kaso 15 bisa dari na kwatankwacin adadin kudin da kasar Sin ta samu a fannin cinikayyar waje wadda ya kunshi cinikin kaya da harkokin hidima.

Yayin da ake tinkarar matsalar ra’ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya a duniya, yawan kudin da kasar Sin ta samu a fannin harkokin hidima ya karu da kusan kashi 10 cikin dari, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin na kara samun ci gaba a wannan fanni yadda ya kamata. Abin da ya fi muhimmanci shi ne tsarin cinikayyar harkokin hidima yana ta kyautatuwa, aikin shige da fice a fannin sabbin harkokin hidima ya yi fintikau.

A farkon watanni bakwai na farkon shekarar bana, jimillar kudin da aka samu a fannin harkokin shige da fice na sabbin harkokin hidima ta kai Yuan biliya 988.84, wadda ta karu da kashi 20.3%. A ciki, an fi fitar da yawan harkokin hidima a fannonin na’urar kwamfuta da sadarwa da inshora da al’adu da harkokin nishadi zuwa ketare, sa’an nan an fi shigo da yawan harkokin hidima a fannonin kudin amfani da ’yancin mallakar fasaha da sha’anin kudi da na’urar kwamfuta da sadarwa cikin kasar Sin. Yanzu cinikayyar harkokin hidima ta kasar Sin tana canjawa daga yawon shakatawa da karbar kwangila da tura ma’aikata zuwa waje zuwa fannonnin ba da shawara da sha’anin kudi da al’adu da ciniki a kan intanat. Hakan ya shaida cewa, cinikayyar harkokin hidima ta kasar Sin tana ta samun karfin yin takara.

A fannin wuraren da suka fi samun karuwa a wannan fannin, yankunan musamman 17 na gudanar da cinikayyar harkokin hidima suna karuwa, inda jimillar kudin cinikayyar harkokin hidima da aka samu a yankunan ya kai 76.4% bisa na fadin kasar. Ban da wannan, harkokin cinikayya a gabashi da yammacin kasar Sin sun fi saurin karuwa bisa na tsakiya da arewa maso gabashin kasar. Alkaluma sun nuna cewa, fannin harkokin hidima a kasar Sin ya ci gajiya sosai daga manufar kasar Sin ta bude kofa ga waje.

A halin yanzu, harkokin cinikin kaya ba sa gudana yadda kamata, a don haka ci gaban harkokin hidima yana da babbar ma’ana ga kasar Sin, har ma ga daukacin kasashen duniya baki daya.

Da farko dai, kasar Sin ta dade ba ta samu ci gaba yadda ya kamata a fannin harkokin hidima ba, amma a farkon bana, kasuwar harkokin hidimar kasar ta samu ci gaba cikin sauri, lamarin da zai taimakawa kasar wajen raya wannan fanni.

Na biyu, wani abin farin ciki shi ne kasar Sin ta bullo da tsari mai inganci wajen saukaka cinikayya a kasuwar harkokin hidima, kuma ta samu wasu fasahohin da abin ya shafa, lamarin da zai taimaka harkokin cinikayyar waje.

A farkon shekarar 2016, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da “shirin raya harkokin hidima ta hanyar yin kirkire kirkire”, inda aka kebe yankuna 15 wadanda suka kunshi birnin Tianjin da birnin Shanghai, domin su zama yankunan musamman na gudanar da cinikayyar harkokin hidima, ya zuwa watan Yunin shekarar bana, majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da “shirin zurfafa aikin cinikayyar harkokin hidima ta hanyar yin kirkire kirkire” da ma’aikatar kasuwancin kasar ta gabatar, sannan ta kara kebe yankuna biyu domin gudanar da wannan aikin, kana ta bukaci a kara bude kofa ga ketare a fannonin sadarwa da yawon shakatawa da samar da hidimar amsa tambayoyin da suka shafi aikin gine-gine da hada-hadar kudi, duk wadannan matakai za su kara habaka bude kofa ga ketare kan aikin hidimar kasar ta Sin.

Na uku, ingancin harkokin hidima da ribar da aka samu a wadannan fannoni sun kara kyautatuwa, hakan ya taimaka wajen inganta tsarin tattalin arziki da ci gaban tattalin arziki mai inganci, ko shakka babu lamarin zai taimaka ci gaban tattalin arzikin daukacin kasashen duniya. (Kande Gao, Jamila Zhou, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: