Connect with us

MU KOYI ADDINI

Ci Gaban Tambayoyi Da Amsoshi A Kan Jinin Haida Da Na Biki  

Published

on

Tambaya Ta 31:- Menene ra’ayin ka dangane da shan kwayoyi na hana jinin haida wanda yake zuwa a mata duk wata menene ra’ayinka dangane da kwayoyinn da ake sha don hana wannan wai don matan su samu su yi Azumi tare da mutane,  don kar su sha Azumi?

Amsa:- Ni dai ina gargadi ina tsoratarwa daga shan wannan kwaya, akawi cutarwa a cikinta cutarwa mai girma. Kuma na tabbatar da hakan ta gurin likitoci. Kuma abin da za’ a gayawa mata shine:­ Wannan jini Allah ne ya rubutawa ‘yan Adam don haka su yarda da abin da Allah ya rubuta kuma suyi Azumi a lokacin da babu abin da zai hana su yin Azumin. Idan kuma ya zo lokacin da suke da abin da zai hana su yin Azumin to su sha Azumin suna masu yarda da abin da Allah mai Girma da Daukaka ya kaddara.

 

Tambaya Ta 32:- Menene hukuncin dandana abinci lokacin Azumin Ramadana alhalin matar kuma tana Azumi?

Amsa:- Hukuncinsa babu laifi da shi idan dai akwai wata bukata da ta janyo zuwa ga yin hakan, sai dai matar kuma ta tofar da  abinda ta dandan da sauri kuma kar ta bari ya shiga cikin makwogwaron ta.

 

Tambaya Ta  33:- Idan mace haidarta ta yanke kafin fitowar Alfijir amma bata yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir yaya Azuminta?

Amsa: In mace jinin ta ya yanke kafin fitowar Alfijir ko da daminti daya ne matukar ta tabbar da jinin ya yanke da auduga ko da farin kyale to azuminta bai baciba. Don tayi azumine lokacin da jininta ya dauke. Ko da yake ba tayi wanka ba sai da Alfijir ya keto, to ba komai akanta, hakanan kuma da zata wayi gari da janaba amma ba tayi wanka ba sai bayan fitowar Alfijir to Azumin yayi. Da wannan ne na keso na ja hankalin mata don wasun su sukanyi bude baki bayan rana ta fadi amma basu yi Sallah ba sai jini yazo musu suna gani kamar basu da wannan Azumin. Wannan magana tasu ba ta da asali tun da tariga ta sharuwa kuma rana ta fadi, ko da minti da yane sai jini yazo mata to babu abin da ya shafi Azumin ta.

 

Tambaya Ta 34:- Idan mace mai jini biki jininta ya yanke kafin akwana arba’in (40) shin ya halatta ta yi Azumi ta yi Sallah?

Amsa:- ‘E’, ya halatta duk Iokacin da jini ya dauke wa mace bayan haihuwanta tilas tayi wanka in a watan Azumi ne ta cigaba da Azumin ta don ta tsarkaka. Don haka babu abinda zai hana Sallah da Azumi da kuma saduwa da mijinta

 

Tambaya Ta 35:-  ldan mace al’adanta kwana bakwai ko takwas sannan jinin ya karu da kwana daya ko kwanuka biyu, to menene hukuncin ta?

Amsa:- ldan mace al’adanta kwana shida ne, ko bakwai ko takwas daga shida sai yaki tsayawa ya kai kwana bakwai, ko takwas ko tara, ko kwana goma, kai ko kwana goma sha-daya. To za ta bar Sallah da Azumi, har sai jinin ya dauke. Don Annabi (S.A.W) bai iyakance iyakansa ba ya dangantan ne da gwargwadon al’adan da mace take yi. Don haka nema Allah (S.W.T.) yake cewa: “Suna  tambayarka neye hukuncin haila, sai Allah Ya ce kace  kazanta ce kula da wannan ayah. Duk lokacin da mace take tare da wannan jini dolene ta bar Sallah har sai tayi wanka. In ya ragu a gwargwadon da takeyi shi kenan. In kuma ya kara karuwa, matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba. Amma ba’a lokaci daya ake karin ba kamar yadda ya gabata.

 

Tambaya Ta 36: Wai tilas ne mace mai jinin biki ta zauna ba Sallah, bata Azumi har kwana arba’in? Ko kuma in ya yanke kafin kwana arba’in tana iya yin Sallah da Azumi?

Amsa: – Mace mai jinin biki ba wai sai ta kai kwana arba’in ba. ldan jinin ya yanke, ko bayan kwana goma ne ko kwana biyar sai tayi wanka, tayi Azumi, tayi SaIlah, har ma mijinta ya saduwa da ita. Koda a ranar da ta haihu ya dauke sai tayi wanka tayi Sallah.

 

Tambaya Ta 37:- Idan mace taga dan digon jini kadan sai taci gaba da Azuminta har zuwa karshen Watan Azumi, shin azuminta nabnan?

Amsa:- ‘E’, Azumin ta yayi, don wannan jini dan digonnan ba komai ba ne. Wannan jini yana daga jijiya ne. Don Hadisin da aka karbo daga Aliyu dan Abi Talib (RA) yace irin wannan digon habo ne kawai dake fitowa daga hanci ba haida bane, haka  aka karbo daga Aliyu (RA).

 

Tambaya Ta 38:- Idan mace mai haida, ko biki jininta ya dauke kafin fitowar Al-fijir, amma bata yi wanka ba sai bayan fitowar Al-fijir, shin Azuminta yayi?

Amsa:- ‘E’, Azumnta na nan, idan dai har tayi tsarki kafin fitowar Al-fijir haka yake ga mace mai haida da mai biki, don wadannan suna daga cikin wanda Azumi ya wajaba a kansu. Don kamar wanda ya wayi gari ne da janaba, amma bai yi wanka. Don Allah (SWT) Yana cewa a cikin Al-Kur’ani  Mai  Girma, yanzu mun halarta muku ku sadu da matayenku a cikin daren Ramadana don neman abin da Allah (SWT) ya rubuta muku na arziki. Kuma kuci, ku sha har sai bakin zare (wato fitowar Al-fijir). To tun da Allah (SWT) yayi izini ana iya saduwa da iyali har zuwa fitowar Al-fijir kaga kenan wanka sai bayan Al-fijir ya keto. Sabo da Hadisin Aisha (RA), Annabi yana wayan gari da janaba wanda ya sadu da iyalensa. Wannan ya nuna Annabi (SAW) ba ya wanka sai bayan fitowar AI-fijir.

 

Tambaya  Ta 39:- ldan mace taji alamun jini amma bai fito ba, ko dan dumi amma bai fito ba da ta duba, shin Azumin ta yayi? Ko zata rama?

Amsa:- Idan mace taji alamun jini ko dumi, amma bai fito ba, da ta duba bata ga jini ba amma ga shi tana Azumi, amma bai fito ba sai bayan faduwar rana to, Azuminta bai baci ba. Tun da jini bai fito ba sai bayan rana ta fadi.

 

Tambaya Ta 40:- Idan mace taga jini amma bata san a ina ta same shi ba, to menene hukuncin Azuminta?

Amsa:- Azuminta na wannan rana bai baci ba. Idan ta duba da wani kyalle ko auduga kuma dai ba haida take yi ba har sai ta sami hujja kwakkwara don asali ta dauka ba haida bane.

 

Tambaya Ta 41:- Wani lokaci mace tana ganin digon jini kadan, a waje waje a jikin tufarta da rana; wani lokaci tana ganin haka lokacin al’adarta, wani lokaci ba lokacin al’adartaba, to menene hukuncinta a wannan lokaci biyu, ko halaye biyu?

Amsa:- Irin wannan tambaya mun amsa ta a baya to amma in taga wannan digon jini a ranakun al’adarta, to wannan ba tababa haidane, ba tada Azumin wannan rana.

 

Tambaya Ta 42:- Mace mai haida ko jinin biki zata iya ci da sha da ranan Azumi?

Amsa:- ‘E’, zata iya ci da sha meye zai hana, amma taci a boye in akwai yara a gidan, don karya rikita yara kanana.

 

Tambaya Ta 43:- In jini ya yanke a lokacin Sallar La’asar shin Azahar da La’asar ne zata yi ko La’asar ne kawai?

Amsa:- Maluma sun yi sabani, wasunsu sun ce Azahar da La’asar ne zata yi, wasu suka ce babu wani dalilin wajibcin Azahar a kanta. Don lokacin jini bai yanke ba, don Annabi (SAW) ) ya ce wanda ya riski raka’ah daya a Sallah La’asar, kafin rana ta fadi, to hakika ya riski Sallar La’asar. A wannan Hadisin a lura yace ta riski La’asar, bai ce ta riski Azahar da La’asar ba, sai ya ambaci La’asar kawai.

 

Tambaya Ta  44:- Idan mace a lokacin da take al’ada, sai taga jini Iokacin al’adarta, sai ya yanke a kwana daya meye hukuncinta?

Amsa:- Idan mace taga jini a kwana daya, rana na biyu bata gani ba to wannan bushewar gaban tane amma tana nan, sai ta zauna kar tayi SalIah, kar tayi Azumi. Wasu malamai sukace, in jinin zai zo kwana daya sannan kwana na biyu sai ya dauke, to ranar da ya dauke tayi tsarki sai tayi wanka taci gaba da SalIah da Azumi, in kuma ya dawo to sai ta ajiye Azumi da Sallah. Har ya kai gwargwadon kwanakin da take ganin jini matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba, in ya wuce kwana goma sha biyar, to ciwo ne sai ta nemi magani ta cigaba da Sallah da Azumi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: