Cibiyar Aminu Kano Ce Ke Ba Wa Marayu Da Nakasassu Ilimi Kyauta –Dr. Ayuba

Makarantar Aminu Kano Education Center babbar makaranta ce wacce gogaggun malaman jami’a wadanda su ka hada da farfesoshi da kuma daktoci da makamantansu ’yan asalin jihar Kano ko kuma masu kishin Kano su ka hadu su ka kirkire ta kuma su ka kafa domin rage gibin tazarar ilim a tsakanin ’ya’yan mawadata da kuma ’ya’yan talakawa, domin bada ingantaccen ilimi kyauta ga marayu da kuma masu bukata ta musamman, wato nakassasu a Kano.
Bayanin hakan ya fito daga bakin mataimakin Daraktan Makarantar wanda ke a matsayin suhgaban Makarantar ta Aminu Kano Educational Billage, Dakta Ayuba Muhammad Ahmad, ya bayyana cewa wannan Makaranta wacce take cikin shekaru uku da kafuwa a Kano bayan ta samu amincewar Hukumar NTI ta kasa an kafata ne domin yada ilimi a tsakanin Matasa musamman marasa galihu wanda basa iya biyan kudin Makaranta a Makarantun Gwamnati balle kuma na masu zaman kansu masu tsada ya ce ganin yadda ake kuka da rashin ingantattun malaman Makaranta tun daga Firamare har zuwa Sakandare yasa sukayi wannan tunani na kafa wannan Makaranta domin samar da ingantattun malamai a matakan bada shaidar karatu ta NCE wanda wannan Makaranta ta dukufa wajan koyarwa a sako da lunguna na Jahar Kano kamar yadda wannan Hukuma ta NTI ta amince ya ce yanzu haka akwai cibiyoyi sama da ashirin banda a matakan kananan Hukumomin Kano.
Haka zalika ya kara da cewa saboda kwarewar Malaman wannan Makaranta da kuma sadaukar da kai da sukeyi yanzu haka Daliban wannan makaranta da aka tura su Makarantu domin koyan yadda ake koyarwa a aikace wato TP cikin kasha 60 zuwa 70 na daliban wannan Makaranta Makarantu masu zaman kansu sun dauke su aiki saboda ingancin karatun da akaga suna da shi kasancewar ita wannan Makaranta anayi ne Asabar da Lahadi duk da akwai masuyi da yamma a kullum kamar dai yadda Dr. Ayuban ya bayyana.
Haka kuma ya ce a bangaren Horar da Dalibai wadanda suke karatun share fagen karatun NCE Aminu Kano Education ta yaye Dalibai a kalla 1000 wasu sun cigaba a wannan Makaranta ta Aminu Kano Education wasu kuma sun tafi wasu Makarantun kuma sune kadai Makarantar Al’umma da suke karbar kudin makaranta kasa da farashin Makarantun Gwamnati inda suka zaftare kashi 35 cikin 100 na farashin kudin makaratun gwamnatin Kano.

A karshe Dr. Ayuba Muhammad Ahmad ya shawarci Gwamnatin Kano da ta Tarayya Sarkin Kano da sauran mawadata da kungiyoyi akan su lura da irin wannan gudun mawa ta masu kishin Kano kuma su kawo tallafi tun daga kan kungiyoyi na Gida da na waje domin bunkasa ilimi a Kano da Kasa baki daya musamman in akayi la’akari da yadda Yayan Talakawa suke kasa karatu saboda tsada kuma shiyasa su suka raba biyan kudin karatu kasha uku zuwa hudu a shekara ba kamar na Gwamnati ba da ake biya lokaci guda kuma dai Marayu da Nakassassu kyauta suke karatu kuma mu muke biya musu kudade da ake biya na wasu mahimman abubuwa a matakin sama

Exit mobile version