Connect with us

LABARAI

Cibiyar Binciken Aikin Gona Ta Gargadi Manoma Kan Sauyin Yanayi A Daminar Bana

Published

on

Cibiyar Binciken Aikin Gona da hadin gwiwar Tsangayar koyar da aikin gona da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, sun bayyana barazanar ake fuskanta dangane da sauyin yanayi a daminar bana, wanda hakan na iya zama babbar barazana ga harkar noma a fadin kasar nana.
Bayanin hakan ya fito ne, a cikin takardar da Cibiyar Binciken Aikin Gona ta raba wa manema labarai a Zariya, wadda ke dauke da sa Farfesa Mohammed Faguci Ishaku. Rahotanni sun nuna cewa, mutum sama da dari suka samu shiga wannan taron ta hanyar intanet.
Haka kuma, sanarwa ta ci gaba da cewa, za a samu tsaikon tsayuwar damina da karewarta a kasar nan musamman a jihar, Bauchi da Kano da Katsina da Adamawa da Gombe da Taraba da Kaduna da Benuwe da Nasarawa da Neja da kuma yankin Birnin tarayya. Bayan haka, hasashen da ake da shi, shi ne za a samu ruwa mai yawa amma kuma zai dauke da wuri.
Bisa wannan hasashe, an shawarci manoma su jinkirta shuka, saboda haka sai su yi amfani da iri mai matsakaicin zango ko kuma a jinkirya shuka irin da ke zuwa da wuri. Saboda haka, aka bukaci manoma da su yi amfani da takin zamani kamar yadda ya kamata.
Advertisement

labarai