Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Cibiyar ‘Dr. Physiq Wellness Centre’ Ta Kaddamar Da Kasaitaccen Littafi

by Muhammad
December 1, 2020
in LABARAI
2 min read
littafi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa

 

samndaads

A ranar Asabar din da ta gabata ne cibiyar kula da kiwon lafiya gami da bayar da shawarwari kan abubuwan da su ka shafin kula da motsa jiki mai suna ‘Dr. Physiq Wellness Centre’ ta gudanar da bikin kaddamar da littafi, wanda Dakta Susana Adams ta rubuta, gami da bude katafaren asibitinta a rukunin gidanjen ’yan majalisa da ke Apo mai lamba 17 kan titin Chuba Okadgbo Street a Zone B da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya.

Taron kaddamar da littafin an gudanar da shi a babban dakin taro da ke cikin rukunin gidajen, inda taron ya samu halartar manyan baki daga ko ina a fadin kasar nan. Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Dakta Jonathan Gooluck, ya zama babban bako, sai Sanata Ali Ndume da ya daya daga cikin manyan baki. An gabatar da jawabai masu gamsarwa daga manyan likitoci da farfesoshi.

“Rubuta littafi kan abin da ya shafi harkar lafiya ba abu ne mai sauki ba, wannan ‘yan uwar tamu ta yi abin a yaba mata duba da yadda a halin yanzu irinsu su ke nema su yi karanci. Ina mamakin yadda mace kamarta ta yi wannan kokari, hakan na nuni da irin tarbiyya da ta samu daga iyaye na gari,” in ji shi.

A karshe ya yi fatan alheri gare ta da addu’ar Allah ya kara ma ta gwarin gwiwa kan dukkan abin da ta sanya a gaba. Shi ma a nasa bayanin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattijai, Sanata Ali Ndume, ya yaba ma ta kan irin kokarin da ta yi a matsayinta na mace, inda ya ce da a ce wadanda suka zo taron nan sun yadda wannan wurin ya ke kafin a gyara shi da sun yi mamaki.

“Lokacin da na zo na ga an gyara wurin sai na yi mamaki har ta kai ga na yi tambayar shin waye ya ke da kokarin gyara wannan wurin da ya lalace aka daina amfani da shi, a ka gaya min Dakta ce, kuma da ma makociyata ce, na yi ta mamakin ganin haka. Don haka wannan kalubale ne gare ku mata, kun ga dai abin da ‘yan uwarku ‘yan Nijeriya ta yi.  Kada don kun ji a tarihinta an ta zauna kasar Amurka da sauransu ai dama ce, kuma kowa za ta iya zo masa, kawai dai ana bukatar jajircewa,” in ji shi.

A karshe ya yi addu’ar fatan alheri gare ta da kuma kira ga sauran mata su tashi tsaye, domin ganin su ma sun yi wani abu da zai kawo cigaba a kasar.

Ita ma shuhagar cibiyar wadda kuma ita ta kafa wannan wuri Dakata Susana Adams, a nata jawabin cewa ta yi ba ta da bakin da za ta godewa Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Goodluck, saboda ba da lokacinsa da ya yi har na tsawon awanni ana zaune tare da shi a wurin, amma ta yi addu’ar fatan alheri gare shi da ma dukkan wadanda suka samu damar amsa gayyatarta.

Babban mai kaddamar da littafin, kuma Shugaban yankunan, Abuja da Arewa, na Bankin Heritage, George Oko-Oboh, shi ya fara sayen kofi biyar na littafin a kan kudi Naira Miliyan 10, sannan sauran jama’a su ka cigaba da zuwa a na saye har zuwa lokacin da a ka kammala a ka rufe taron.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sojoji Sun Kwato Mutane 39 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna

Next Post

Ministar Jinkai Ta Nuna Jimamin Kisan Gillar Zabarmari

RelatedPosts

Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

by Muhammad
10 hours ago
0

Tambuwal Ya Kafa Kwamitin Bincike   Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,...

A duniyar Nijeriya ta yanzu, da yawan mutane da ma masu lura da al’amuran yau da kullum su na kallon gudanar da zabukan kananan hukumomi

Abubuwan Al’ajabi A Zaben Kananan Hukumomin Kano

by Sulaiman Ibrahim
21 hours ago
0

Kuri’un Da Aka Kidaya Sun Haura Na Zaben Gwamna A...

Ranar Bude Makarantu

Korona: Har Yanzu Babu Ranar Bude Makarantu A Jihar Kaduna

by Sulaiman Ibrahim
21 hours ago
0

 Dukkanin makarantun Firamare da na sakandari da suke jihar Kaduna...

Next Post
Jinkai

Ministar Jinkai Ta Nuna Jimamin Kisan Gillar Zabarmari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version