Cibiyar Fort Detrick Ta Yi Kazamar Alaka Da Rundunar Sojojin Japan Ta 731

Daga CRI Hausa

A baya bayan nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, an yiwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin tambaya, game da jita jitar da gwamnatin Amurka ke yadawa don gane da asalin cutar COVID-19.

Game da hakan, kakakin ya ce bayanai daga wasu kafofi sun tabbatar da cewa, cibiyar binciken kwayoyin halittu ta Fort Detrick dake Amurka, na da alakar kud da kud da rundunar sojojin kasar Japan ta 731, wadda ita ce ta yiwa kasar Sin mamaya.

Kaza lika, kwararrun kasar Sin game da ayyukan wannan runduna ta 731, sun bayyana cewa, Amurka da Japan sun fara gudanar da wasu ayyukan sirri tun daga watan Satumbar shekarar 1945, lokacin da Amurka ta aikewa cibiyar Fort Detrick, umarnin yin bincike kan kayayyakin yaki masu nasaba da cututtuka na Japan, ya zuwa kammala binciken da ya gudana a birnin Tokyo cikin watan Nuwambar shekarar 1948.
Bisa sharadin wanke rundunar ta 731 daga laifukan yaki, Amurka ta samu damar amfani da bayanan wannan runduna ta 731, a fannin yin gwaji kan bil adama, da amfani da kwayoyin cututtuka, da amfani da su a yaki, da gwajin iska mai guba.

Rundunar ta 731, bangare ne na ayyukan sirri na soji dake nazari kan amfani da kwayoyin cututtuka a yaki, da gwaji kan bil adama, da sauran bincike da sojojin Japan wadanda suka mamaye kasar Sin suke yi, a lokacin yakin duniya na II. An ce akwai wasu rahotanni na irin wadannan gwaje gwaje da aka yi kan mutane, a rumbun adana bayanai na sashen dakin karatun majalissar dokokin kasar, fannin ayyukan kimiyya da fasaha.

Amurka ta aike da kwararru daga cibiyar Fort Detrick, domin yin bincike kan kayayyakin yakin kasar Japan masu nasaba da kwayoyin cututtuka, inda ta biya yen 250,000 domin karbar bayanai game da irin wadannan kwayoyin cuta daga cibiyar ta 731.

Kaza lika Amurka ta karbi bayanai da ta yi amfani da su wajen hada sinadaran cututtuka na amfani a yaki, yayin da cibiyar Fort Detrick ta samu nasarar fadada ayyukan ta bayan yakin duniya, kuma a yanzu ita ce dakin gwaje gwaje na sojojin Amurka mai lakabin P4. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version