Cibiyar horas da matan aure da zawarawa da ‘yan mata sana’o’in dogaro da kai da ke makarantar Baba Sidi a Bauchi ta nemi tallafin gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin hukumar lura da mata da matasa don a kawo musu dauki ta yadda za su ci gaba gudanar da ayyukan su na koyawa mata sana’a don su dogara da kan su, musamman a wannan lokaci da gwamnati ta himmatu wajen ganin mutane sun iya sana’a da za ta tallafa musu wajen samun abin kan su.
Huzaifa Hamza Rahama shugaban cibiyar koyar wa mata sana’a da ke harabar makarantar Baba Sisi Firamare da ke Kofar Ran ya bayyana wa wakilin mu da ya ziyarci cibiyar cewa suna yiwa wajen lakabin cibiyar koyar da mata sana’a ta M.A. Abubakar Waomen Empowerment, inda ya bayyana cewa sun kirkiri wannan cibiya ce don koyawa matana sana’o’i don su dogara da kan su. Suna koyar da yadda ake yin man shafawa da shamfo na wanke kai da kayan adon mata da kayan adon daki kamar kwaryar adon daki na kallo ya koma sama da ragaya da kayan adon bango na fulawoyi da huluna da zanen gado da aikin wuyan riga da jaka da sauran su. Ya ce sun himmatu kan wannan aikine don kowace mace ta dogara da kanta kuma ta koyawa yaranta don suma su samu abin dogaro da kan su, kuma kyauta ne basa biya ko sisi.
Yace shi mai sana’a ne kuma ya bude wajen don koyar da sana’a kuma idan an yi kayayyakin an kai kasuwa an sayar sai a sake zuwa kasuwa a sayo wasu kayan aiki ayi wasu kayan ribar kuma a biya matan da suke koyarwa kudin abin hawa. Ya ce har yau basa samun tallafin gwamnati kuma ba wanda ya taba ware wani abu ya basu don fadada wajen duk da cewa suna da dalibai 4634 da suke zuwa lokaci lokaci akwai masu zuwa da safe wasu da rana.
Aishatu Hassan wata daliba tace ta koyi yin jaka da kallo ya koma sama suna sana’ar suna samun riba don haka suke neman tallafin gwamnati don ta basu jari, saboda sun kai wata goma tun bude cibiyar suke wurin suna koya amma basu da jari duk da cewa sun koyi abubuwa da dama da suke yi.
Amina Abdullahi wata daliba itama tace ta iya yin man shafawa da shamfo da abun wuya da turare da kayan gyaran jiki da morning fresh na wanki. Ta ce shugaban cibiyar yana da kokari wajen yin hakuri ba tare da karbar kudi ba yake daukar dawainiyar koyar da daliban sana’a da dama.
Saudatu Mato Babakarami Malama a Makarantar tace tana koyar da sakar kayan sanyi na yara da na manya da kallo ya koma sama na adon bangon daki da kuma aikin wuyan riga na keken dinki da sauran kayan sana’a ba abin da basa koyawar wa daliban don su dogara da kansu game da kayan amfani na gida.
Ummi Ibrahim ta bayyana cewa tana koyar da sana’ar kwalliya kuma tana yi a gida na biki ko suna a rana tana yiwa mutane 20 musamman amarya da kawaye kuma tana koyarwa a kan naira dubu da dari biyar mako guda a gida ga duk wacce ke son koyo na musamman a inda take. Kuma ta bayyana cewa game da farashi suna da sauki saboda tana yin kwalliya akan naira dari biyar mutum guda zuwa har sama da haka yadda akwai kwalliya naira dubu biyar.
Hafsat Manga malamace a wurin ita kuma tana koyar da jaka da shirya duwatsu da wurin adana fulawar cikin gida. Don haka ta bayyana cewa suna cin moriya sosai wajen koyar da abin da suka iya da kuma koyon wanda basu iyaba a wajen malamai ‘yan uwan su. Don haka ta bayyana cewa ya kamata gwamnati ta shigo don ta agaza musu ta yadda za su samu ingantuwar sana’o’in da suka koya don su jima suna cin moriya.
Cibiyar ta koyon sana’a da ke Makarantar Baba Sidi wacce Malam Huzaifa Hamza Rahama ya assasa wurine da duk wanda ke da kishi idan ya ga abin da suke sarrafawa na kayan sana’a zai ji sha’awar ganin an tallafa musu. Saboda ya bayyana cewa idan sun sayar da kayan da suka yi ne suke samun kudin gudanar da cibiyar da kuma bayar da abin da ya samu wa malaman don biyan kudin abin hawa zuwa cibiyar don su ji dadin zuwa su ci gaba da koyarwa.
Amma ya bayyana cewa sun yi iyaka kokari zuwa cibiyoyin gwamnati da ke tallafawa don ganin sun samu agaji amma har yanzu babu komai da suka samu. Don haka ya ja hankalin hukumar lura da mata da matasa ta BASYWORD mallakar Jihar Bauchi da su kawo musu daukin gaggawa don samun yadda za su ci gaba da fadada wannan cibiyar don ta ci gaba da koyar da matan sana’a yadda ko sun